Ahankali taci gaba da ratsa kasaitaccen
gdn nasu, kai tsaye ckn gdn ta durfafa
hannunta rike da ledar siyayyar data yo.
Daga ina???
Kalaman da suka dira a kunnenta kenan kmr
daga sama, tayi saurin dakatawa domin
tadau muryar ko waye, kai tsaye takai kllnta
ga inda taji anyi maganar tayi arba da
Abbanta.
Tadanyi saurin sakin fuskarta tare da cewa "
uhm!! Abba daga siyayya nake, momi ce ta
aikeni."
Aiken ne sai yanzu?? Karfe kusan 7:00 na
dare??
Ta danyi saurin cewa "Abba kudi ne suka
yanke min don kusan a kasa ma na dawo."
waye wancan daya saukeki a mota??
Yayi nuni izuwa waje da dan yatsansa.
Tadan zaro ido kadan tare da tambayar
kanta " dama ya ganshi?? " ta dago kai
muryarta tadan kara canjawa domin tana
gudun kar yaki fahimtarta duk da tasan
saukin kansa, nan ta kwashe duk abinda ya
faru ta fada masa.
Ya kara jefo mata tambayar " a gdnnan ba
motoci?? "
kanta na kasa tace "direba ne bayanan
kuma ya tafi da mukullan motar."
Y'AR AMANA ba zarginki nake ba amma kibi
a hnkl ki kuma kula a duk inda kike, kinji
ko??"
A hnkl ta gyada kai alamar amsa abnd ya
fada mata ta kuma taka ta wuce izuwa ckn
gdn yabita da kll kawai tare da grgz kai
tamkar me tausaya mata.
Sannu Alhaji!! Wani dan lukutin mutumi fari
ya fada ya wuce.
Yauwa!! zonan. Ya fada.
Da sauri mutumin ya dawo tare da risinawa
ckn grmmw, gani alhaji. Alhaji jamil ya gyara
babbar rigarsa tare da cewa "ina kaje dazu
kabar aikinka alhalin kasan a matsayinka na
direba kowanne lkc za'a iya nemanka??"
direban ya kara risinawa da fadin " ranka ya
dade hajiya ce ta aikeni. "
menene dalilin tfy da mukullan motocin gdn
to??
Ya kara tambaya ba tare daya kalleshi ba. Ita
tace na tafi dasu.
Shiru kawai Alhaji jamil yayi kmr me tunanin
wani abu, tbbs zata iya!! ya fada a ransa. Ya
juyo gareshi yace " bazan hanaka kaje
aikenta ba amma karka kara tfy da mukullan
motocin gdn nan, sbd motocin ba naka
bane kuma ba nata bane, nawa ne " yayi
nuni da kansa.
Jeka!! Ya fada sanda shima ya juya tare da
takawa ya nufi ckn gdn.
Tun kafin ya karasa yake jiyo sautin hajiyar
tana bambamin bala'i ta inda ta shiga
batanan take fita ba.
A hnkl ya karasa hamshakin falon alfarmar
yana me binta da kll, kawai tasa Y'AR AMANA
a gaba ta inda ta shiga ba tanan take fita ba.
Domin a cewarta wai taje ta zauna don taja
mata zagi, harda sharrin wai siyayyar ma ba
dai-dai tayo ba.
Ganinsa ne yasa tayi saurin dakatawa taci
gaba da hura hanci.
Ya kikai shiru?? kici gaba mana, Ya fada
yana me kllnta.
Ko kuma keda kanki kinsan ba adalci kike
aiwatarwa ba ko??
Ba tare da bata damar amsawa ba ya dora
da cewa "kin aiketa byn kin sani sarai direba
bayanan kuma ke kika aikeshi kuma sbd
mugunta sai kika bata kudi kai da kai da
siyayyarki, sbd sanin yakamata irin nata bata
rage miki komai a siyayyarki ba ta
gwammace ta dawo a kasa, amma duk da
hakan da fada zaki saka mata.
Kin kyauta.
Yakai karshen mgnr tare da duban inda y'ar
amana ke zaune yace " tashi ki wuce kinji!!
Allah yayi miki albarka." A hnkl ta mike tare
da dan risinawa a gabanta tace " kiyi hakuri
momi."
ta taka tare da wucewa izuwa dakin dake
fuskartarsu." ya juyo da dubansa ga hajiyar
da har yanzu fuskarta ke a daure tamau
yace "yakamata ki rinka kamanta adalci a
duk abinda zakiyi sbd kina nuna fifiko fiye
da kima..."
Alhaji kenan bani da ikon aiken yarinyar nan
ko nayi mata fada idan tayi min ba dai-dai
ba?? Ta fada tare da kauda kai.
Kina dashi!! Ya fada tare da dorawa da fadin
"amma ai ba ita kadai ce a gdnnan bako??
Ina farida??
To daga yau inda idan kin tashi aikenki ki
aikesu su duka, idan sukayo ba dai-dai ba
idan duka ma ta kama ki dakesu su duka
amma baki aiketa ita kadai ba, kinji na fada
miki."
ya juya tare da barin falon izuwa dakinsa.
Tabishi da kll kawai, koba komai tasan
hakan zai rage mata damar tozarta yar
amana.
** barin falon da tayi kai tsaye ta fada
dakinsu wanda su biyu kacal a cknsa,
sallama tayi wanda ya samu amsawar isa da
gadara daga farar kyakykyawar budurwar
dake zaune a tsakiyar tafkeken gadon barci
me matukar kyau da ban sha'awa tana
karanta novel, y'ar amana ta karaso bakin
gadon tare da zama bayan tace "kai! Rufaida
na debo gjy da yawa wlh."
ai nayi mamaki naga tun dazu shiru.
Ta fada har yanzu bata dago kai ta dubeta
ba.
Kedai bari kawai, kinyi salla kuwa??
Yar amana ta sake tambaya.
Nikam nayi kece dai makararriya.
Yar amana ta mike tare da cewa bari ki gani
nima dai na tashi na daura himma kada lkc
ya kara ja, kai tsaye ta nufi dauro alwala,
rufaida tabi ta kallo ta baya kasa-kasa taja
tsaki tare da cewa "banza wai ita Y'AR
AMANA."
Cak! Ta tsaya tare da waigowa da cewa " me
kika ce?? " rufaida ba wani canjawa da tayi
tace "me nace kuwa?? Ni Ba abnd na fada."
yar amana taci gaba da kllnta kawai nadan
lkc har idonta ya ciko da kwalla ta juya
kawai izuwa inda ta dosa.
*tunda ta zauna zaman sallar bata tashi ba
sai data dau wajen awanni biyu, ta hada
harda sallar isha'i tayi nafilolin data saba
sannan ta tashi ta koma kan gadon, har
yanzu farida nanan rike da novel ta dukufa.
Gobe lakcar mu ta safe ce yakamata ki
kwanta da wuri.
Yar amana ta fada sanda ta zauna a bakin
gadon.
Rufaida tace "na sani." bakiyi sallar isha'i
bama fa!! Ta sake fada tana duban rufaidar.
Zanyi!! Ta sake bada amsar a gajarce.
Yar amana ta mayar da zaman da tayi izuwa
kwanciya tace "sai yaushe??"
rufaida ta kauda kai tare da cewa "kai!!" ta
dawo da dubanta gareta tace "ina
ruwanki??
Babu!!
Yar amana ta fada tare da gyara kwanciya ta
juyar da kanta daga fuskantar rufaida.
Ta dade a haka ba tare da barci ya kwasheta
ba, kwakwalwarta nata tariyo mata
abubuwa daban-daban da suka faru yau har
dai barci yayi awon gaba da ita.
** washe gari kmr kullum misalin karfe
takwas na safe zaune suke su uku bisa
kujeru sun zagaye makeken tebirin dake
dauke da abinci kala-kala wanda yayi dai-dai
da irinna break fast, kujera daya ce tak! Ba
kowa akanta wato wacce Abbansu ke zama
sai dai yau su uku suke yin break din ba tare
dashi ba.
Shiru ne kawai ke gudana a wurin ba
wanda ke cewa kowa komai, zuwa can yar
amana ta dago kai kmr ta tuno wani abu
tace " wai momi yau abba lfy naga bai fito
ba har yanzu?? "
momin kmr ba zata ce komai ba zuwa can
tace " lfyrsa qlau kawai baiyi niyyar fitowa
bane. "
ta fada tare da kauda kai. Bari nagama naje
na dubashi. Yar amana ta fada. Farida ta
dago kai tare da cewa " ok! Baki yarda da
abnd aka fada ba kenan ko?? "
nidai bance haka ba, shikenan ko yana da lfy
bazan je na gaidashi ba?? Mahaifinane fa??
Y'ar amana ta fada.
Farida ta kalleta ta dauke kai tare da cewa "
mahaifinmu dai... Bake kadai ba malama. "
yar amana tabita da kll kawai ta kauda kai
tare da cgb da yin abnd ke gabanta. Jim
kadan suka kammala su biyu suka mike
suka doshi dakinsu tare da fara shirye-
shiryen tfy makaranta don daukar laccarsu
ta yau.
Tare suka fito izuwa falon kowaccensu ckn
shiga irin tata kuma irin wacce ta sabayi,
hajiyar ce kawai zaune a falon, yar amana ta
dubi farida tace " ina zuwa bari na shiga na
gaida Abba sai mu tafi. "
farida ta dubeta tare da duban agogon
wayar dake hannunta tace " kinga nusaiba
dalla kizo mu tafi mun kusan makara kin
sani fa!! "
ba tare data saurareta ba ta fada dakin
abbannasu.
Farida ta harareta tare da doka tsaki ta
koma kan kujerar ta zauna tace " ni ban
taba ganin banza irin wannan ba wai ita yar
amana mtsss...."
meye na tsakin to??
Hajiya dake zaune ta fada.
Kawai haushinta nake ji wlh momi sbd
munafuncinta. Farida ta fada.
Ba yar uwarki bace kike ce mata
munafuka??
Haka dai ake cewa wai yar uwata ce amma
allah momi ina kokwanton cewa anya kuwa
ke kika haifi nusaiba??
Jifa fatarmu ni dake farare sol damu amma
ita bakikkirin da ita."
amma ubanku ai baki ne ko?? Momi ta fada.
Tambayar da faridar ta kasa amsawa kenan
ta shiga 2nani momin ta mike tabar falon.
** Y'ar amana kai tsaye ta wuce ga inda
abbanta ke zaune bisa darduma byn tayi
sallama ta zauna a gefensa nesa kadan, ya
dago kai a hnkl tare da cewa "Y'AR AMANA".
Na'am Abba ina kwana?? Lfy qlau, ya amsa.
Shiru ya gudana nadan lkc tsakaninsu zuwa
can ya katse shirun da cewa "yar amana da
wani abu ne?? "
abba akwai.
Ta amsa wanda yasashi gyara zama da cewa
" fadi mana yar amana. "
Abba tambayar nan ce dai dana saba yi
maka a kowanne lkc wacce baka gamsar
dani amsarta, don allah ka fada min wacece
ni?? Meye alakata da wannan gdn??
Domin zuciyata da kasa yarda da cewa ni yar
gdnnan ce, tbbs akwai wani boyayyen
al'amari game da ni."
yayi saurin grgz kai tare da cewa " waye ya
gaya miki?? Na dade da fada miki cewa "ki
cire wannan 2nanin a ranki, ke y'ata ce
kuma y'ar gdnnan gaba da baya ba wani lbr
idan ba wannan ba." amma me yasa momi
da farida keyi min haka?? Me yasa basa
kaunata??
Kenan momi ba ita ce mahaifiyata ba?? In
haka ne wacece??
abba ka taimakeni ka fada min don allah
koda lbrn bazai min dadi ba nidai na fita
daga rudani."
yadan bita da kll tare da kakalo murmushi
yace " yar amana kenan, ba haka bane tana
kaunarki sbd bata da kmrki kema kuma
haka baki da wata mahaifiya idan ba ita ba,
sai dai wata kila idan ni ina nuna miki kauna
100% ita sai ta nuna miki 90% don kar a
shagwabaki da yawa."
Yakai karshen maganar dashi kansa yasan
ba haka take ba. Ta dago kai tare da cewa "
to abba me yasa kake cemin yar amana idan
har kaine ka haifeni?? " ya danyi shiru
domin jin tambayar yayi kmr daga sama
zuwa can yayi murmushi tare da cewa " yar
amana dukkan da ko y'a amanar allah ce
don na fada miki haka bana jin akwai wani
abu." da amsoshin dashi kansa me bada su
ya tbbtr ba gamsassu bane ta mike tare da
cewa "abba zamu tafi makaranta sai mun
dawo."
to a dawo lfy allah ya tsare, komai dai lfy ba
wata matsala ko?? Ta grgz kai kawai alamar
babu ta wuto izuwa waje, farida bata falon
abnd ke nuni da 2ni ta kosa tayi waje,
jakarta kawai ta zara tayo waje kai tsaye
izuwa harabar gdn ta fito 2ni kuwa direban
ya seta motar ta fuskanci waje ita kawai
suke jira.
Da sauri ta bude motar ta shiga ta mayar ta
rufe tare dace musu "am sorry fa na tsaida
ku ko?? Mu tafi."
ta fada tare da duban direban.
A hnkl ya taka motar suka fice farida nata
harararta da gefen ido.
Tayi kicin-kicin ta hade rai tamkar bata taba
yin dariya ba, direban da yar amana ne
kawai keyin hira jefi-jefi. Ba kuma yanzu
kawai ba kusan kowanne lkc yar amana ce
kawai ke iya sakin fuska da kuma yin hira da
ma'aikatan gdn sabanin farida da kowanne
lkc fuskarta ke a daure bawai ga yan aikin
gdn nasu ba ga kowa ma, hakan yaja mata
bakin jini a wajen al'umma.
Yar amana ce yar gaban goshi a wajen
kowa sbd kyawawan halayenta da iya zama
da kowa, tana da farin jini a wajen jama'a
musamman a makarantarsu sunanta ya
zagaye ko ina, duk inda kayi yar amana ake
fada wanda hakan ke kona ran farida a ko
yaushe.
Anya ko bawani abu aqasa???
Title :
Yar Amana Part 3
Description : Ahankali taci gaba da ratsa kasaitaccen gdn nasu, kai tsaye ckn gdn ta durfafa hannunta rike da ledar siyayyar data yo. Daga ina??? ...
Rating :
5