Saurayin tsayawa kawai yayi yana kllnta ba
tare da yace komai ba, ya dan dauki tsawon
sakwanni kadan kafin ya gyara tsayuwarsa
fuskarsa bata wani nuna alamun damuwa
ba ko kadan.
Ya sake binta da kallo tare da cewa " haba
BAIWAR ALLAH!! Me yayi zafi haka??
Sanin cewa nayi miki laifi fa shi yasa ma na
dakata don baki hakuri, amma kin kama
zagina idan kuma nima nahau sama me kike
zaton zai faru??
Fada zamuyi kenan??"
ya saisaita muryarsa ckn rarrashi da cewa:
"Don Allah kiyi hakuri, hanyar ce da ramuka
da yawa su nayi kokarin kaucewa ko kadan
ban lura da wannan ba.
Kiyi hakuri"
ya sake mai-maitawa a karo na biyu.
Lkc guda jikinta yayi sanyi domin ta tbbtr da
cewa ba yadda tayi zato yake ba, tbbs bai
cancanci bakaken maganganun data fada
masa ba.
dakyar ta iya dago kai ta dubeshi tadan
jinjina kai alamar amsa abnd ya nema,
kamar me jin kunyar magana kuma tace "
nayi gaggawar yanke hukunci ckn fushi ba
tare da nayi maka uzuri ba raina ne ya baci
amma kayi hakuri..."
Daga ganinki bakiyi kama da mara hakuri
ba, sai dai kowacce zuciya kanji zafi duk
sanda aka munana mata nagode da fahimta
ta da kikai.
Ya taka zai wuce idonsa yakai ga jikinta a
karo na biyu, ba karamin bata ta yayi ba
hakan yasa ya dakata tare da juyowa gareta
yace " idan ba damuwa ki shiga mota na
karasa dake gida mana. "
Tayi saurin grgz kai da cewa " A'A ngd kaje
kawai zan karasa."
Yadanyi murmushi tare da cewa " bai dace
ki tafi a haka ba koda namiji ne bare ke
mace, zai fi kyau na direki har kofar gdnku
yadda ba wanda zai ganki a haka."
Ta sake grgz kai da cewa "ka riga ka bani
hakuri kuma na hakura, na shiga motarka
kuma ba abune me karbuwa ba kayi hakuri
kawai."
Takai karshen maganar sanda ta juya taci
gaba da tfy bisa mikakkiyar hanyar. Binta da
kll kawai yayi da sauri yace "hakan na nufin
baki hakura ba kenan??"
Tayi saurin dakatawa da tafiyar tare da
juyowa tace " ba haka bane!..."
Idan har kin hakura da gaske to ki bani
dama na kyautata miki sau daya tak!! " ya
fada byn daya katseta.
Kmr zata ce wani abu amma ta fasa wanda
ya bashi damar takowa da fadin " idan
kuma kina zaton ni wani mugun ne to ki
cire hkn daga ranki don na tbbtr idanuna
kawai sun isa sheda akan cewa ni bame
yanka kan mutane bane."
dariya tadan kwace mata sanda ta taka suka
jera tace " su din ai ba kama garesu ba.
" eh hakane amma ki yarda dani ba wani
mugun nufi a tare dani.
Ta gyada kai da cewa " da ganinka kam,
amma kasan a matsayina na mace dole nayi
taka tsan-tsan ko?? Sbd mutum abin tsorone
musamman maza. Ta fada dai-dai sanda
suka karaso jikin motar tasa.
Yayi dariya tare da cewa " wasu ba amma
duk lalacewa akwai nagari."
ya bude kofar motar ya shiga tare da bude
mata kofar gaban daga ciki, ba tare da
gardama ba ta kuwa shiga tare da mayar da
kofar ta rufe.
Wani iri taji domin yaune ranar farko data
aminta da shiga motar wanda bata sani ba,
shigar tatane kuma ya kara tbbtr mata
motar ta kasaita ce domin daga ciki ya linka
wajenta kyau ma2ka ga sanyin A-C ta ko ina.
A hnkl ya fara 2ka motar ckn nutsuwa tana
meyi masa nuni da hanyar gdnnasu, sai da
suka dauki tsawon lkc suna tfy zuwa can
yana me duban hnyr yace " gdnku nada nisa
ashe amma me yasa tunda wuri baki nemi
taxi kin hau ba??
Tadanyi yake ckn muryarta mara amo tace "
eh! Daga siyayya nake a AGH STORE,
mahaifiyatace ta aikeni to kaga kudin data
bani da naje sai naga abbwn data lissafa
min da kudin hannuna sunzo kai da kai.
Idan har inaso nayi kudin mota to sai dai na
rage wani abu daga siyayyar ni kuma bana
so nayi mata haka, shine kawai na
gwammace nayi mata siyayyarta gaba daya
na koma a kafa."
Da sauri ya dubeta nadan lkc sannan yace "
Allahu akbar!! Kin fifita bukatar mahaifiyarki
akan taki!! Kin yarda kisha wahala ki shiga
tsanani don farantawa mahaifiyarki!!
Irinku a duniya kadan ne, Allah ya bani irin
halinki koda ba duka ba. Ta danyi dariya
tace " wace ni?? Ai halinka yafi nawa nesa
ba kusa ba."
me yasa kika ce haka?? Ya tambaya. Ta gyara
zama tace " akwai hadisin dake cewa:
[mafi alkhairi a ckn mutane shine wanda
aka batawa yana da damar daukar mataki
amma ya hakura]
amma ni da kayi min laifi sai na kasa hakura
nadau matakin da shine iyakar abnd zan
iyayi, kaga kai kuma duk da na bata maka da
munanan kalamai sai baka dau mataki ba ka
hakura harma ka taimakeni.
Kaga kenan kana daga ckn mafi alkairi a ckn
al'umma."
ya danyi murmushi kadan da cewa " kuma
dai ashe ke yasayyada ce??"
sukayi dariya dukkansu.
Tafiya kadan suka kara suka iso wata
kasaitacciyar unguwa kll daya zakayi mata
kasan ungwr masu akwai ce.
Mun iso!! Ta fada.
Yabita da kll tare da taka birki motar ta tsaya
cak!! Ya dubeta "to Amma dai yakamata
nasan sunanki domin nasan ba lallai mu
sake haduwa ba."
Ta danyi murmushi da cewa " sunana
nusaiba jamil amma anfi kirana da sunan
Y'AR AMANA."
ya danyi shiru zuwa can ya maimaita sunan
"Y'AR AMANA!!
Kmr akwai inda nake jin sunan nan."
ta yiwu amma sai dai wata daban bani ba.
Ta kama kofar tare da budewa ta juyo tace "
bazan taba manta abnd kamin ba, laifi daya
tak! Amma kabi hnyy da yawa na faranta
min ngd sosai mlm....." USMAN!!
Ya karasa mata.
Usman itama ta fada tare da dorawa da
fadin "ngd sosai".
ta bude kfr ta fice yabita da kll yana
murmushi sai dai fskrs ta sauya da yaga
katafaren gdn data shiga, ya hango motocin
alfarma a hrbr gdn, ckn grmmw kuma me
gadi ya bata hny ta wuc abnd ke nuni da
cewa yar gdnce.
To amma idan hkne me yasa ba za'a
dauketa a mota a kaita ba??
Irin tmbyyn da fara yiwa kansa kenan, Y'AR
AMANA ya sake fada kfn ya taka mtrsa ya
tafi...
Uhmm wato ya shiga kenan...allah sadai
baxakakasa fitaba...
Kunsan shi love shegen abune,,
Aßdool-azeez ßeen Aßoußakarke muku
barka da asubah..
Dan samun rubu tun mu akoda yaushe
shigo nan
Title :
Yar Amana Part 2
Description : Saurayin tsayawa kawai yayi yana kllnta ba tare da yace komai ba, ya dan dauki tsawon sakwanni kadan kafin ya gyara tsayuwarsa fuskarsa...
Rating :
5