Doguwar hanya ce me ma2kar fadi
wacce ta kasance mikakkiya sambal! Ta
yadda zaka iya hango abinda yake nesa,
shimfidaddiyar kwaltar dake daukar ido da
babu ramuka ko kwazazzabai akanta ya
karawa hanyar fasali da kyan yanayi.
Idan ka kalli hagu da daman titin kuwa
kyawawan kantuna ne kala-kala duk inda ka
gifta, tsakiyar kwaltar kuwa motocine
manya da kanana, tsala-tsala wadanda daka
gansu kasan mallakar masu hannu da shuni
ne da kuma na masu rangwamen hali
harma da taxi-taxi na haya dake ta tallar
wurin da suka dosa.
Hakadai suketa giftawa wata nabin wata.
Daga gefen titin kadan kuwa mutane dake
tafiya a kasa ne keta kaiwa da kawowa
kowa na nufar inda ya dosa, a cikin
wadanda ke tafiyar kasan itama take sai
sauri take tamkar zata tashi sararin
samaniya.
Hannunta na rike da bakar leda babba irinta
store wadda da alama kaya ne a cknta,
hankalinta gaba daya yayi gida kasancewar
yamma ta doso don akalla karfe 6:00pm na
yamma ta kawo jiki.
Sai dai duk da saurin da takeyi baisa ta koda
nuna alamun ta tsaya don tarar mota ba, illa
saurin da take zubawa da kafarta duk da
cewa masu taxi nata kawo mata talla ganin
cewa bata dace koyin kama da tafiyar kasa
ba.
KALLO DAYA zakayi mata kasan bata ckn
walwala ko farin ciki hasalima ckn damuwa
take tamkar zata fashe da kuka, sai dai duk
halin da take ciki bai bayyana muni a gareta
ba wata kila hakan na nuna tsantsar
kyawun da Allah yayi mata ne.
Domin kuwa farilla ne ga duk wanda ya
kalleta ya sake kallonta, ta kasance ba fara
ba amma ba zaka kirata baka can ba wanda
hakan ya dace da yanayinta.
Kusan komai madaidaicine a tare da ita,
jikinta rufe yake da ingattacciyar sutura ta
kamala data dace da addini da kuma
yanayinta.
*A hankali ta saki doguwar hanyar da take
bi izuwa wata y'ar siririya kwalta da tayi
kwana hannunta na hagu, babu mutane
sosai a hanyar hakan yasa ta kara saurin
tafiyar domin yanzu ta tabbatar ba me
ganinta.
Sai da tayi tafiya kamar ta mintina goma
tana tabin kwane-kwanen hanyar da take bi,
jin karar worn da tayi a bayanta yasata
ratsewa ta koma gefe motar ta wuce ta
gabanta.
Kasancewar lkcn damuna ne ruwa na
kwanciya a yan ramukan dake samuwa a
mafi yawan hanyoyi musamman na layuka
irin wadannan hakan yasa Bisa AKASI tayar
motar ta shiga ramin da ruwa ke kwance a
cknsa wanda yayi fallatsi kai tsaye ga inda
kamilalliyar budurwar ta ratse don baiwa
motar damar wucewa, ilahirin jikinta kuwa
ya baci da ruwan wanda ya kasance ba
ruwa kamar saura ba hade yake da kasa.
Tayi saurin rintse ido ckn tsananin takaici ta
bude idanun nata tabi jikinta da kallo yadda
yayi ma2kar baci, WATA SABUWA kenan ita
da take tfyr kafa ga kaya a hannunta, gashi
ta gaji ga bata da abin hawa mota kuma
gashi jikinta ya baci ta yadda zataji kunyar
tfy a haka ma2ka wasu ma ai sai suyi mata
kallon zararriya.
Damuwarta ta linka tada sosai irin wacce ita
kanta ta tabbatar ta bata taba yin irinta ba,
da sauri ta daga kanta tabi motar data gifta
din da kallo wacce tuni ta tsaya cak!! Tare da
dawowa da baya a hankali ta sake tsayawa
kofar motar ta bude a hankali wani
matashin saurayi kyakykyawa ya fito daga
tsaleliyar motar.
Kallo daya zakayi masa daga shi har motar
tasa kasan DAN KWALISA ne, yayi saurin
kauda glass din dake idonsa da cewa "inna-
lillahi wa inna ilaihir-raji'un", sanda yafi
jikinta da kallo.
A dai-dai lkcn ckn fusata byn ta gama binsa
da kll da muryarta data banbanta ma2ka
data kowa domin daban-daban take fita,
sanyayya da sai ka saurara sosai zaka
fahimci me take fada, tace " haba mlm!!
Amma ka cuceni wlh ka gama dani.
Kai mahaukacine??
Baka gani ko makahone kai??
Ji fa yadda ka bata ni??
Duk fadin hanyar nan sai ka biyo tanan inda
nake sbd dama akwai mugunta a ranka
naka batamin ko??
To kayi kaji dadi amma ka sani Akwai
ALLAH!!
Dan iska!! Macuci!! Azzalumi!! kawai...
Allah ya qara dawo dani...
Dan samun rubu tun mu akoda yaushe
shigo nan
Title :
Yar Amana part 1
Description : Doguwar hanya ce me ma2kar fadi wacce ta kasance mikakkiya sambal! Ta yadda zaka iya hango abinda yake nesa, shimfidaddiyar kwaltar dake...
Rating :
5