Dubun wani ma'aikacin EFCC mai mukamin mataimakin sufritanda mai binciken laifuka, mai suna Uzodinma Kingsley Agbazue ta cika, bayan da ya damfari wani dan majalisa da hukumar ke gudanar da wani a kansa.
Shi dai Agbazue ya bukaci dan majalisar ne da ya ba shi wadansu makudan kudade har naira miliyan 15, domin a nema masa sassauci game da binciken da ake yi masa.
Ya kuma yi karyar cewa, jami'in da yake gudanar da binciken ne ya nemi da ya shiga tsakani, don su taimakawa dan majalisar.
Ganin babu wani sassauci da yake fuskanta, dan majalisar da ba a bayyana ko waye ba, ya fallasa halin da ake ciki, bayan da jami'in da ake zargi Agbazue ya yi kokarin mayar masa da naira miliyan 5 tare da cewa an raba sauran ga manyan da ke sama.
Dan majalisar ya kuma yi zargin cewa ba sau daya ba ya sha bai wa jami'in kyautar kudade fiye da miliyan daya, a matsayin gudunmawa ga jinyar da matarsa take yi.
Hukumar ta EFCC dai ta tsare wannan jami'i nata da yake kokarin bata mata suna, tare da shirin daukar matakin ladabtar wa a kansa.
Zuma Time hausa
Title :
Wani Ma'aikacin EFCC Ya Karbi Cin Hancin Miliyan 15
Description : Dubun wani ma'aikacin EFCC mai mukamin mataimakin sufritanda mai binciken laifuka, mai suna Uzodinma Kingsley Agbazue ta cika, bayan da...
Rating :
5