Ana zargin wani mai aiki a gidan matar marigayi tsohon shugaban kasa HajiyaTurai Yar’adua, da sace mata kayayyaki da darajar su ta kai naira miliyan 91, inji rahoton jaridar Daily Trust.
Shi dai wannan dan aikin da ake zargi, shi ne Yusuf Sarkin Gida. Kwamishinan yansanda na jihar Katsina Usman Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin, inda a ranar talata 20 ga watan satumba ya bayyana ma yan jaridu cewa “yansada sun kama Alhaji Yusuf Sarkin Gida bayan Hajiya Turai Yar’adua ta kawo kararsa sati biyu da suka wuce, Alhaji Yusuf ya kwashe sama da shekaru 40 yana kula da dukkanin kadarorin Hajiya Turai Yar’adua” inji shi.
akwai akwati guda 37 na Hajiya Turai a hannunsa, amma guda 27 kawai aka samu. Sa’annan kayayyakin dake cikin guda 27 ma dun sun bata, kuma shi wanda ake zargin ya kasa yin gamsassun bayani dangane da bacewar akwatin da kayayyakin.. muna binciken shi, amma abin mamaki yau shekaru 40 kenan yana musu hidima.”
Ita dai HajiyaTurai Yar’adua itace matar tsohon shugaban kasa kuma tsohon gwamnan jihar Katsina, Umaru Musa Yar’adu, tayi zamani daga shekara ta 2007 zuwa 2010, labarai sun nuna cewa tana daya daga cikin makusanta mashawarta ga shugaba Yar’adua a zamaninsa.
Naij Hausa
Title :
Wani Dan Aikin Turai Yar’adua Ya Sace Mata Naira Miliyan 91
Description : Ana zargin wani mai aiki a gidan matar marigayi tsohon shugaban kasa HajiyaTurai Yar’adua, da sace mata kayayyaki da darajar su ta kai naira...
Rating :
5