Labari daga Shafin BBC Hausa Ya Nuna cewa
''Rundunar sojin Nijar ta ce dakarunta da hadin gwiwar na Chadi sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram talatin da takwas, a samamen da suka kai a yankin Diffa dake kudu maso gabashin kasar.
A cikin wata sanarwa, kakakin ma'aikatar tsaro ta Nijar, Kanar Moustapha Ledru ya ce sojoji biyu sun samu raununaka a samamen, wanda aka kai bayan harin da mayakan kungiyar suka kai a kauyen Toumour, dake kusa da tabkin Chadi.Kanar Ledru ya ce sojojin hadin gwiwar sun kuma kwace makamai masu yawa, da harsasai daga wajen mayakan.Ma'aikatar tsaron ta Nijar ta ce sojojin na ci gaba da fatattakar mayakan kungiyar ta Boko Haram daga yankin.
Sojojin sun kai samamen na hadin gwiwa ne a tsakanin ranar Litinin zuwa Laraba a kauyukan Gueskerou da Toumour, dake kudu maso gabashin Nijar.Wasu mazauna yankunan da kuma wata kungiya mai zaman kanta sun ce a ranar Laraba, mayakan kungiyar ta Boko Haram sun kai hari garin na Diffa, inda suka saci abinci da magunguna, amma ba su kashe kowa ba.A watan Fabrairun 2015 ne Boko Haram din ta fara kai hare-hare a yankin Diffa.A watan Yulin wannan shekarar, aka kafa rundunar tsaro ta hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Nijar da Chadi da Kamaru don kawar da mayakan kungiyar ta Boko Haram daga kasashenRikicin Boko Haram na tsawon shekaru bakwai, ya yi sanadiyar mutuwar fiye da mutane dubu ashirin a Najeriya da Kamaru da Chadi da Nijar, sannan fiye da miliyan biyu da dubu dari shida suka rasa gidajensu''
Title :
Sojojin Nijar Da na Chadi Sunyi Nasara Akan Boko Haram
Description : Labari daga Shafin BBC Hausa Ya Nuna cewa ''Rundunar sojin Nijar ta ce dakarunta da hadin gwiwar na Chadi sun kashe mayakan ku...
Rating :
5