'Yan Nijeriya, kamar yadda kuke kan shagulgulan sallar Layya, a gefe daya ina kara baku hakuri akan koma bayan tattalin arzikin kasar.
Darussan Sallah, shine jin tsoron Allah da hakuri.
Koma bayan tattalin arzikin kasar a halin yanzu, ya samo asali ne sakamakon koma bayan tattalin arzikin a duniya gaba daya domin ba mu tanada kudade a lokacin da ya wuce ba.
Muna shan wuya a yanzu saboda kura-kuran da aka tafka a lokacin gwamnatin da ta wuce.
Ina jaddada cewa wannan gwamnati, tana yin aiki kullum don ceto 'yan Nijeriya daga mawuyacin halin da suke fuskanta.
Muna kuma kan aiki don kawo tsaro da kuma hana cin hanci da rashawa kwata-kwata.
Ina mai baiwa musulmai shawara da mu yi koyi da dabi'un addinin Musulunci, da kuma zama lafiya da Kiristoci don samun hadin kasa..
A yi bikin sallah lafiya.
-Muhammadu Buhari
Title :
Sakon Sallah Daga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Description : 'Yan Nijeriya, kamar yadda kuke kan shagulgulan sallar Layya, a gefe daya ina kara baku hakuri akan koma bayan tattalin arzikin kasar. ...
Rating :
5