Hidima ga marayu, gani ya kori ji, layyar da kwamitin Zakka ya yi wa marayu a gundumar Illelah ta kayatar ainun.
A wannan gundumar sun yanka rakuma biyu ga marayun, sun yi abin a zo a gani. Domin tun kafin kwamitin jiha ya ba da kudin layya naira dubu 130 tuni su dama sun hada kudi naira dubu 170, inda kowanne mai rike da wata sarauta ya bada naira dubu biyar, a ka kara kudin bisa ga abin da Zakka ta basu.
A duk shekara wannan gundumar ta na kokarin yankawa wadannan marayun rakumi kuma bana ma an kai rakuma biyu!
Marayu da gajiyayyu 280 ne suka amfana, wadanda aka zakulo daga garuruwan hakiman su. Hakiman da suka zo daga nesa kwamitin ya basu kudin mota.
Tabbas wannan gunduma karkashin jagorancin Sarkin Rafin Illela Alhaji Tukur Abdurrahman, da 'yan kwamitin sa sun cancanci a jinjina musu kan wannan kokarin da fatan sauran gundumomi shekara mai zuwa za su kwaikwayi yadda wadannan suka yi ko ma dai su wuce su.
Malam Zubairu Malami Gwadabawa ne ya wakilci shugaban kwamitin Zakka Malam Muhammad Lawal Maidoki a wajen zagayen sanya ido a gundumomin yankin na ganin yadda suka yi wa marayu layya da kudin da aka ba su.
Source Zuma Times
Title :
Photos: An Yankawa Marayu Rakuma Biyu A Illelah
Description : Hidima ga marayu, gani ya kori ji, layyar da kwamitin Zakka ya yi wa marayu a gundumar Illelah ta kayatar ainun. A wannan gundumar sun yan...
Rating :
5