Jami’an ‘yan sanda sun sami nasarar damke ‘yan fashin da suka yi wa shahararren dan wasan kwallon kafa na kungiyar Super Eagles Onazi Ogenyi sata da kuma raunata mahaifinsa a gidan shi dake Jos, jihar Plateau ranar talata data gabata.
Dan wasan ne ya bayyana haka a shafinsa na yada zumunta na Twitter, inda ya nuna godiyarsa ga ubangiji akan nasarar da aka samu ta kama wadannan miyagu.
Onazi Ogenyi, mai shekaru 23, da haihuwa a shafin nasa ya bayyana cewa "godiya ga ubangiji da ya taimaka aka cafke wadanda suka yi mana fashi, da kuma raunata mahaifi na a unguwar Epe dage Jihar Legas".
Ranar Talatar da ta gabata ne dan wasan ya fadawa manema labarai cewa wasu ‘yan fashi sun shiga gidansa dage Jos a jihar Plateau, kuma sun yi awon gaba kaddarori da dama da kuma raunata mahaifinsa.
Title :
Photos: Yan Sanda Sun Cafke Yan Fashin Da Suka Yi Wa Dan Wasan Super Eagles Onazi Ogenyi Sata
Description : Jami’an ‘yan sanda sun sami nasarar damke ‘yan fashin da suka yi wa shahararren dan wasan kwallon kafa na kungiyar Super Eagles Onazi Ogenyi...
Rating :
5