A jihar Bauchi da ke arewacin Nijeriya, wani matashi mai suna Husseini Emmanuel ya rasa idanuwansa sakamakon kwakule masa su da ake zargin wasu abokansa sun yi.
Ana dai zargin wasu abokansa David da Jerry mazauna Fatakwal da yaudararsa zuwa wani rafi domin wanka, inda a nan ne suka buga masa dutse a ka lokacin da suke wankan a rafi, bayan ya suma suka cire masa idanuwan.
Lamarin ya faru ne a wani kauye mai suna Marti a yankin karamar hukumar Tafawa Balewa da ke jihar ta Bauchi. Abokan na Hussaini Emmanuel wanda makaniken babur ne sun yaudare shi ne da cewa sun samar masa aikin gadi a Fatakwal har suka ja shi a jika da cewa za su tafi da shi can.
Husseini ya bayyana cewa a halin yanzu ba shi da wani buri a rayuwa da ya wuce ya samu ido ko da guda daya ne, domin ya rika ganin gari. Jami'an tsaro na 'yan sanda sun ce suna gudanar da bincike kan lamarin kamar yadda wani kawunsa ya bayyana.
Source Rariya
Title :
Photos: Yadda Aka Kwakwalewa Wani Matashi Ido A Bauchi
Description : A jihar Bauchi da ke arewacin Nijeriya, wani matashi mai suna Husseini Emmanuel ya rasa idanuwansa sakamakon kwakule masa su da ake zargin ...
Rating :
5