A yanzu haka Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi II yana can birnin Assisi na Italiya domin halartar wani gagarumin taron duniya akan zaman lafiya da sulhu tsakanin mabiya addinai.
Da yake tofa albarkacin bakinsa a taron da aka yi yau mai taken "Kishirwar samun zaman lafiya a duniya " mai martaba sarki yace akasarin tarurruka irin wadannan, masana sun fi sha'awar tattauna harkokin gwamnati da tattalin arziki maimakon yin tsokaci akan halin kaka-ni-kayi da talakawa ke ciki. Sarkin ya kara da cewa laifin shugabannin Afrika ne na halin ko-in-kula yake jefa matasan Afrika cikin matsanancin hali da har wasu matasan ke gwammacewa su jefa kansu a hallaka ta hanyar ketawa ta teku da nufin tsallakawa kasashen Turai don neman managarciyar rayuwa. A ta cewar Sarki jagorancin gaskiya da adalci da tausayi sune kadai abubuwan da zasu canja tunanin matasan Afrika kuma a samu zaman lafiya.
Sarki Sanusi II har ila yau yace yanzu addinin musulunci da addinin Kirista sun rarrabu zuwa kungiyoyi da dama ta yadda babu wani mutum ko kungiya da zasu bugi kirji suce sune ke magana da yawun ilahirin wadannan addinai. Ya kara da cewa kuskure ne a dauka cewa kasar Saudiyya ko kasar Iran sune ke wakiltar musulmin duniya, bayan ga sauran kasashe nan dake da dumbin al'ummar musulmi kamar Maroko da Indonesiya da Indiya wacce musulmi tsiraru ne a kasar amma duk da haka sun fi musulmin dake daukacin kasashen Larabawa yawa.
Za'a ci gaba da wannan taro inda ake sa ran Paparoma Francis zai halarta a yau Talata kuma zai gana daya da daya da wasu zababbun mahalarta taron ciki kuwa har da Sarkin na Kano inda daga bisani shugabannin zasu ci abincin rana tare da wasu marayu da yake-yake a kasashensu ya tagaiyara.
Manyan jiga-jigan addini da shugabannin da suke halartar taron sun hada da wakilin shugaban mabiya addinin Bhuda wato Dalai Lama, da babban shugaban cocin angalican kuma Archbishop na Canterbury, da wakilan mabiya addinin Musulunci da Yahudanci.
Wannan taro dai shine na 30 tun lokacin da aka kirkireshi a shekarar 1986 musamman domin tattaunawa akan hanyoyin wanzar da zaman lafiya da adalci da kuma samun maslaha tsakanin mabiya addinai daban-dabam na duniya. Wakilai da shugabannin addinai kamar 450 ne daga sassa na duniya ke halartar taron.
Wadanda aka gayyata daga Nijeriya baya ga Sarkin Kano akwai
Cardinal Onaiyekan da Bishop Mathew Hassan Kukah da kuma Bishop Kaigama.
RARIYA
Title :
Photos: Sarkin Kano Ya Halarci Taron Sulhu Na Duniya A Italiya
Description : A yanzu haka Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi II yana can birnin Assisi na Italiya domin halartar wani gagarumin taron duniya ...
Rating :
5