Wasu mutane shida sun rasa ransa a wani gidan karuwai dake garin Umahia babban birnin jihar Abia.
Wata majiya ta bayyana cewa mutanen dake kan gudanar da sharholiya a cikin gidan sun fara jin maye haka kurum ne har ta kai ga an samu dan hatsaniya, daga bisani bayan rikicin ya lafa, sai aka samu wasu karuwan 'yan mata su uku da wasu maza kwastomominsu su uku duk sun rasa ransu.
Lamarin da ya fi daurewa jami'an tsaron kai a yayin da suka zo daukar gawarwakin shine yadda mutanen suka mutu ba tare da rikicin ya kai ga an raunata kowa ba.
Rariya
Title :
Photos: Mutane Shida Sun Rasa Ransu A Wani Gidan Karuwai A Jihar Abia
Description : Wasu mutane shida sun rasa ransa a wani gidan karuwai dake garin Umahia babban birnin jihar Abia. Wata majiya ta bayyana cewa mutanen dak...
Rating :
5