A ci gaba da gudanar da shagulgulan Sallah da al'ummar Musulmin duniya ke yi gwamna jihar Adamawa Alhaji Muhammad Umar Bindow Jibrilla ya yi bikin Sallah a sansanin 'yan gudun hijira na Malkohi dake wajen birnin Yola.
Gwamnan dai a cewar shi ya yi hakan ne domin ragewa 'yan gudun hijiran radadin halin da suka tsinci kansu a ciki.
Wata 'yar gudun hijira a sansanin ta shidawa Zuma Times cewa ba su yi tsammanin ziyarar gwamnan ba, a daidai wannan lokacin, amma sun ji dadin hakan.
Sansanin na Malkohi dai na daya daga cikin sansanonin dake dauke da dumbin 'yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba su da gidajensu.
Title :
Photos: Bindow Ya Yi Bikin Sallah A Sansanin 'Yan Gudun Hijira
Description : A ci gaba da gudanar da shagulgulan Sallah da al'ummar Musulmin duniya ke yi gwamna jihar Adamawa Alhaji Muhammad Umar Bindow Jibrill...
Rating :
5