Barayin Shanu Sun Yi Hadari Bayan Sun Dauko Shanun Da Suka Sato
Daga RARIYA
Asirin wasu barayin shanu ya cika yau a garin Kiri dake karamar hukumar Taura a jihar Jigawa.
Barayin wadda suka gamu da mummunan haddarin mota bayan sun dauko shanun da suka sato, akan hanyarsu ta zuwa Kiri-Tafice zuwa Majia bayan da 'yan kato-da-gora suke biyo bayansu.
Barayin sun samu damar sato shanu guda bakwai, inda suka dauko guda biyar suka kuma bar biyu a can.
Biyu daga cikin barayin sun gudu, inda sauran kuma suna asibiti domin amsar magani.
Title :
Photos: Barayin Shanu Sunyi Hadari Da Shanun Da Suka Sato
Description : Barayin Shanu Sun Yi Hadari Bayan Sun Dauko Shanun Da Suka Sato Daga RARIYA Asirin wasu barayin shanu ya cika yau a garin Kiri dake karam...
Rating :
5