Wata 'Yar Nijeriya Saheela Ibrahim Ta Shiga Sahun Matasa 50 Masu Kwazo Na Duniya
Saheela Ibrahim mai shekaru 19 'yar asalin Nijeriya ce dake nazarin halittar kwakwalwa a jami'ar Harvard ta Amurka, wacce kuma ta shiga sahun matasa 50 masu kaifin basira a duniya, saboda yadda ta yi zarra a tsakanin abokan karatun ta.
A yayin bukin yabawa kwazon 'yan Afrika dake Amurka Saheela ta bakunci fadar shugaba Obama wanda kuma ya jinjina mata tare da cewa, Amurka na alfahari da yara irin Saheela, wadanda suke amfani da baiwar da suke da ita a fagen ilimi, don cigaban duniya baki daya.
Ya ce, tarihin kasar Amurka ba zai taba mantawa da bajintar matasa irin su Saheela ba.
Mahaifiyar ta, Shakirat Ibrahim ta bayyana cewa tun Saheela na karama ta fita daban wajen nuna kwazo da nacin karatu, abin da ya sa ta yi fice a karatun da take yi.
Saheela na daga cikin dalibai mafiya kankantar shekaru da suka yi karatu a wannan fitacciyar makaranta.
Zuma Times Hausa
Title :
'Yar Najeriya Saheela Ibrahim Ta Shiga Sahun Matasa 50 Masu Kwazo Na Duniya
Description : Wata 'Yar Nijeriya Saheela Ibrahim Ta Shiga Sahun Matasa 50 Masu Kwazo Na Duniya Saheela Ibrahim mai shekaru 19 'yar asalin Nijeriy...
Rating :
5