.
Yaune karshen shagalin da ake gudanarwa a
ranan bikina. Yaune dinner party wacce a ka
shirya ta ta mata zalla a golden dragon Chinese
restaurant. Ban hada dinata da maza ba
Kasancewar daga ni har angon ustazaine,
bamason abinda zai kawo nakasu a rayuwar
aurenmu. Ina zaune a gurin dinnar zuciyata fari
kal cike da madaukakin farin ciki sakamakon
Yaune ranar da zan angwance da gwarzon Mijina,
Wanda nake matukar sonsa tabbas Ina matukar
doki zakwadi da zuwan wannan rana ranar dazan
tare a gidan USTAZ AHMAD SULAIMAN SA'EED.
duk dana kasance cikin matukar sanyin jiki
sakamakon sallama da iyayena danayi da
yayyena maza wadanda basu halarci wajen dinar
ba Kuma daga nan gidan Mijina zaa wuce Dani
Kai tsaye Wanda yake nasarawa G.R.A cikin
kwaryar birnin KANO. Kowa ka Gani awajen cikin
farin ciki yake Don haka nima dole nake kago
murmushi, saboda alhini Na rabuwa da gidanmu
.
Karfe tara daidai aka tashi daga wajen dinar sai
sannan zuciyata ta sake tsinkewa na rukunkume
mamina da ita ma na lura jikinta a sanyaye yake
Don Tunda aka Fara bikin na lura Sam mamina
bata yi naam da abin ba Don dai ba yadda zatayi
ne a matsayin ta na kishiyar mahaifiyata, Batada
damar nuna hakan. Mamina da kanta ta shigar
dani dakina hannuna damke cikin nata, tana sake
karantamin adduoi a kunne na sannan ta
rungume ni tana kuka nima kukan na saka da
kyar mutane suka rarrashe mu Saidai Babu
Wanda yayi mamaki saboda ansan tsananin
shakuwar mu da mamina.
.
Tsit gidan yayi bayan kowa ya tafi sai sannan na
sake jin fargaba, Gashi har shadaya ta gota ba
Ango Babu labarin sa ni kuma inajin kunyar na
kira lambar wayarsa don Dagaske Allah ya zuba
min kunya kasance wata tsatson Fulani .
.
Sai Sha biyun dare angona ya shigo Sanye cikin
wata jallabiya data ke ta walwali sai alkyabba a
samansa. Daga gani kayan zasuyi tsada shigar
larabawa yayi sosai Kasancewar da ma ako
Yaushe shigar ustaz Dina kenan sai zanga
kamshin tsadaddun turaruka yake, wadanda ya
saba sasu a ko Yaushe har sun riga sun ratsa
shi. Da sauri na kudundune kaina duk danayi
mamakin ganin fuskar sa a hade murtuk. Duk da
kasan cewar sa maabocin murmushi ako yaushe
badai ya dariya sosai don afadarsa yawan dariya
yana rage imani. Mayafi nasake ja na kudundune
kaina don har yanzu Ina matukar jin kunyar ustaz
Dina. Ina jiyo takunsa har ya iso bakin gado ya
tsaya.
.
AYSHA yafada cikin jarumar muryar sa. Saidai
nayi matukar mamaki Don ba haka ya saba
kirana ba AYSHATA shine sunan daya saba kirana
dashi ako yaushe har kowa ma ya sani, Duk da
haka banyi nawar dagowaba da sauri na dago na
kalle shi tabbas yanayinsa ya firgitani. Ungo
wannan. Leda ya miko min daga haka ya fice a
tunanina zaije ya kimtsa amma mai yasa
ustazuna ya hade ransa haka kodai namasa wani
laifine ban saniba?
Da azama na jawo ledar na ciro kunshin kazar
yahuza suya da ice cream mai sanyi na Fara ci
Sai dana koshi sannan na jawo ledar Dan na dau
lemo .idona yakai wata envelope a tsanmanina
ustazuna mantuwa yayi Don haka na jawo kwalin
exotic na bude shi daga shi sama kawai nayi na
fara daddaka Don dama da azababbiyar yunwa
na wuni. Idona ne yakara kaiwa kan envelope din
saina ga sunanane a jiki maana Aysha imam
khalil don haka da azama Na dauko na fara
karantawa
.
Assalamu........ni AHMAD SULAIMAN SA'EED na
saki Matata Aysha saki daya. Batare da iddataba
Idan ta samu.......
.
Ai kasa karasawa nayi na runtuma ihu fadi nake.
Tabbas NAGA RAYUWA meyake shirin faruwa da
ni a daren farko a gidan Mijina abin sona ya
sakeni mai nayi masa? Kuka ne ya kufce mini
Saikuma na tintsire da dariya Dana tuna cewa
kadan daga cikin aikin da namiji kenan. Koma
zolayata yake yanaso yagawada mizanin soyayyar
sa a zuciyata, Amma kuwa anya an taba wasa da
maganar saki a daren farko? Baridai naje naji
dahir.
.
Tsam na Mike na shiga laluben sashen nasa
kasancewata bakuwa agidan ban Sha wahala
wajen gano kofar sashen nasa ba babban falo ne
ya rabamu a hankali na murda kofar na shiga
shiru sashen nasa sai sautin kiraa ne yake tashi
Wanda ya kunna a radio cikin muryan gwanin
nasa Malam Ahmad sulaiman. Nagama lalubena a
babban falon ban ganshiba donhaka na shiga
karamin falon.
.
Yana zaune akan sallaya na sameshi ya kife
kansa a gwiwa. Jin motsin tahowata yasa shi
daga Kai ganin nice yasa shi mayar da kansa da
wuri da alama baya son haduwar mu da shi.
Zuciyata a jagule na isa wajen sa a darare na
zauna a gefensa cikin kasa da murya nace
.
Ustazuna wata takarda nagani acikin kayan da
kakawo sainaga ina tantama da abin dana
karanta aciki ban Kuma fahimceka ba. Daga
idanunsa yayi da suka rine suka zama jajaye Duk
da Kasancewar su farare tas kamar madara
.
Duk abinda kika kiranta aciki Babu kuskure hakan
nake nufi. Saki ustaz?
.
Kwarai da gaske Don haka ki tabbatar kin fice
min daga gida kafin karfe bakwai na safe......
Daga haka ya shige daki Don kuwa kukane yake
neman kufce masa yabarni da budaddan baki.
.
Sam Banji takaicin hakan ba Don nasan kadan
daga halayyar mazan yanzu ne Amma kuwa
ustazu zaiyi dana sanin sakin nan dayayi min na
tozarci da wulakanci zuciyata fes na koma
sashena matsalata daya ce yanzu mai zan je
Nafada a gidan mu? Yaya kuma mutane zasu dau
alamarin duk wacce akaji labarin an saketa daren
farko a gidan Mijin ta tabbas sai an jefa mata
ayar tambaya tabbas NAGA RAYUWA ni Aysha
Sam na kasa runtsawa nayi a daren ranan
saboda radadi da zuciyata keyi.
Kwarai ustaz ya cuceni da kyar na samu na Mike.
Ban daki na shiga nayi alwala ina fitowa na tada
kabbarar sallah. Jallah zan kaiwa kukana ko naji
sanyi a zuciyata.
.
Tun karfe uku bani nabar kan sallaya ba sai
danayi sallar asuba sannan na Mike Duk da
tsananin sanyin da akeyi hakan Bai hanani saka
hijabina Na fice daga gidan. Motata na shige kirar
Kia nabata wuta aguje, Sai gidan mu dake
sharada phase II.
.
Duk da a tsorace nake hakan Bai hanani shiga
gidan da karfin guiwa ba yan biki ko watsewa
basuyiba gabadaya an idar da sallah an kwanta
kenan na ratsa falon. Ba kowa saboda muku
mukun sanyin da akeyi sashen mamina da tura
Sadaf Sadaf na shiga gabadaya Kanne na da
yayyena da sukazo biki sunanan baki bude suka
bini da kallo mami kuwa hangame baki tayi tace
.
Ni fadima, aysher Meya fito dake da asubar fari?
Nadama saidanafada Wa alhaji kinyi kankanta da
aure shekara Sha bakwai yanzu haka bakon al
amari kika gani ko? Lumshe ido nayi hawaye na
Gudu a fuskata mami tsam ta Mike ta shige dani
dakinta.
.
Aysher Meya kaiki fitowa Don Kinga sabon abu?
Auren fa kenan kowacce mace daga haka fa
girma yake zuwar mata Kuma ba kyau tona asirin
miji Don haka tun kafin Mutanen gida su ganki
tashi maza ki tafi kafin ma abban ki yaji kiyi
hakuri kinji Aysha.
.
Shiru nayi ina kallonta Don na fuskanci ita abin
da take hange daban sake katseni tayi da fadin
tashi mana aysher so kike har sai maganar ta
yadu ayita kallon ki a matsayin mara wayo mai
gudun miji. Sake Lumshe ido nayi cikin
dashasahiyar murya nace.mamina ya sake ni da
.me? Mami ta fada cikin matukar razana da
kidima. mika mata takardar nayi ina fadin Gashi
dai.
.
Hannunta yana rawa ta bude tana karantawa
hawaye kawai take Amma tana gamawa sai naga
tana ninkewa tana dariya tace sharrin da namiji
saiki tashi muje wajen abban ki yaga sakamakon
alkhairin da Ahmad ya aiko masa
.
Kwalalo ido waje nayi nace mami Allah bazan iya
zuwa gurin abba ba Don bansan yadda zai dau
lamarin ba .tashi nace miki muje ko iyakacinsa da
kefa fada Bai isa ya ce zai raba ki da rankiba ta
fada a fusace ta kuma fincikeni mukayi waje
gabadaya, jamaa an fito an tsaya cirko cirko yan
son kwasar gulma Tunda anji labarin amaryar da
aaka kai jiya da daddare gata ta dawo da safe
Title :
Naga Rayuwa Part 2
Description : . Yaune karshen shagalin da ake gudanarwa a ranan bikina. Yaune dinner party wacce a ka shirya ta ta mata zalla a golden dragon Chine...
Rating :
5