bakomai abba kinmayar dani abokin wasan ki
kenan kukane ya kufcemin na shiga rantse masa
akan ba komai mikewa yayi tareda fadin Allah
yasa ba koman nan da Kwana hudu daurin
aurenku. Wani shok naji ya shigeni yayin danabi
bayan abba da kallo shin da gaske ne aurena da
ustaz ko kuwa wasane farinciki ya shiga zuciyata
damuwata daya ce yanzu Mamina ya ilahi
yazaayi Mamina ta fahinceni kuma menene
kamomar karatuna Kashe gari da sassafe ina
tashi ko makaranta banjeba na roki direba ya
kaini gidansu Mamina Idan lokacin tashi yayi ya
dauko ni Amma kada ya gaya wa kowa. Daya ke
muna dasawa dashi da wuri ya amince yakaini
hotoro gidan su mami. Da sallama na shiga
baban falon gidan su ba kowa sai kakata Hajiya
Bilki babar Mamina da fara a ta tareni tana fadin
GA amarya GA amarya a kunyace na durkusa ina
gaishe ta rankwashina tayi hade da fadin jaira
Yau kuma kunyata kikeji ina bakin tsiwar na
gyara gilashina nace wai ma cemiki nayi kunyarki
nakeji an gayamiki ina da wani mijin bayan
wannan tsohon mijin naki mai ran karfe.
Eh lallai kwarai bakinki yana nan bai mutuba yar
nema Don kinsan ba yanzu bane tariyar taki nan
shashashar uwarki tazo tana mana kuka saboda
zaa aurar dake ai kuwa taci kaniyar ta wajen
alhaji Don yace koshine ustaz Ahmad yazo yana
son yarsa ko a firamare take zai cireta ya aura
masa tace kema wai dan shashanci ba kya son
auren aini na gode masa ma daya matso da
auran kusa Idan yaso ku mutu keda uwar taki
can ya aurar da ke Idan kin gama jarabawar
Masha shagalin biki ki tare........ Harara na watsa
mata tare da fadin ni kindameni da surutu ina
Mamina take.. Tace tana can uwar daka tunda
alhaji ya fatattaketa yace kada ta sake ya dawo
ya sameta agidansa kije can ki sameta mikewa
nayi na haye saman gidan zuciyata cike da
tausayin Mamina Maison taga na zama wata aba
a rayuwa. Sai Gashi burinta baicikaba ta kawo
Kara kuma anki goyamata baya wannan shi ake
kira rana zafi....... Ahankali na tura kofar dakin
Mami na hango ta akan sallaya da alama sallar
walha ta idar ta zubomin ido gabadaya idanunta
sun sauya da gudu na karasa na karasa na fada
Kanta ina kuka da sauri ta rungumeni tana
shafamin Kai
.
Kada kiyi kuka Ayshata ki rungumi kaddara kamar
yadda nima na runguma Sam mahaifinki yakasa
fuskantata hakan har takai mu ga samun
mummunar sabani abinda bamu tabayiba
shawara daya zanbaki Idan kin tare a gidan ki ki
jajirce wajen ganin kinci gaba da karatunki ki
tabbatar baki zama bagidajiya ba wajen kulle
kanki agida babu ilimi kinji. Daga kaina nayi
Hawaye na zirara daga idaniyata soyayyar
Mamina tana Kara kwarara a zuciyata. Karfe
shabiyu mami ta dauki akwatinanta data lafto
kaya Muka fito da niyar tafiya gida Hajiyan mami
ta dubeta tana murmushi Fatima yar rigima har
yanzu rigimar ki nanan Saura Idan kin koma ki
sake tayar da wata rigimar kinajidai abin da
babanki yace ya riga ya gama magana babu
yadda zaayi kihana mutum iko da yarsa dagake
har yar taki ababen ikon sane karatun me zaa
tsaya yi duk da baiwar da Allah ya bata na
gamda katar da mijin kwarai abin nema ruwa a
jallo a zamanin nan ke ba abin farin ciki da
tinkaho bane ace yarki ta samu wannan
santalelen mijin koya ya shaideshi agarinnan Koni
daya zo gaishe mu banga wani aibu a tattare da
shiba don haka ki kiyaye India ba so kike ki nima
musaka kafar Wanda daya dakeba kamar
mahaifinki. Ki tashi ki tafi Allah ya miki albarka
.
Mami jikin ta a sanyaye taja hannuna muka tafi a
motarta
.
Umma da faraarta ta tare mu tana fadin Ashe
diyar taki ba makaranta ta tafi ba wajen ki ta tafi
mami hararar wasa ta zuba wa umma Hade da
fadin ita dayake ta damu Dani ai taje Biko umma
shiru kawai tayi mata ta shige daki don tasan
halin mami sarai
.
Da daddare abba ya shigo da katinan daurin aure
ana zaune a wajen cin abinci ya mikawa mami
yace ta rabawa makota mami tabi katin da kallo
da alama mamaki take da taga sunana acikin
katin ina kallo tasa gefen mayafinta ta goge wata
kwalla da ta zubo mata a gefen ido. Tausayin
Mamina ya kamani Don haka na Mike na nufi
dakina. Kwanciya nayi sosai akan gado ina
tunanin mafita na tabbatar yanzu ustazuna
yadaina sona tunda gashi ya daina nemana ko a
waya da alama wannan yarinyar ce ta dauke
masa hankali ko ma mu biyun duka zaa aura
masa waya sani tabbas dana shiga uku kodon
inada kishine ? Har ana gobe daurin auren babu
shi babu labarin sa gidanmu kuwa ya cika da
mutane duk da ba lokacin bikin bane duk yan uwa
na nesa sunzo Kwana. Ina kwance cikin saannina
a daki mami ta shigo tare da miko min wayata
ana kiranki tace dani sannan ta fice dakyar na
Mike zaune na kara wayar a kunnena
.
Ganin bansan lambar ba yasa nace hello waye a
layi ne jinayi ya saki ajiyar zuciya sannan yace ki
fita waje zaki karbi sako gurin direbana ki
tabbatar kin suturce jikin ki. Iya Abindaya fada
kenan ya Kashe wayar haushi manaji tamkar
bazan fita ba saidai na daure na fita
.
A tsaye na samu direban nasa bayan mungaisa
ya miko min wani akwati karami mai kyau tare da
fadin Hajiya ga sakon yallaban karba nayi na
kasa godiya nashiga gida a dakin mami na bude
akwatin wasu material ne masu kyau da tsada a
dinke suke tamkar na indiyawa sai wata
dakakkiyar shadda Kala biyu sunsha aikin surfani
da leshi da fashion sai wani english gold takalmi
da jaka Kala biyu Amma fa masu matukar kyau
da tsada sai manyan mayafai masu kauri sosai
da tura ruka masu tsadar gaske. Wani karamin
ambulan ne yaja hankalina ina budewa naga
rubutun yallabai yasa
.
Amaryar ustaz ina fatan kayan sunyi miki duk
dadai nasan ba murna zakiyiba a dalilin kin daina
so na kishirya gobe da daddare zanzo na kaiki
gidanmu don suna korafin basu sankiba
.
Murmushi kawai na yi naja kayan gefe sannan na
kira Mamina na nuna mata tabbas ta yaba da
kayan ta kuma kwashe su ta kaiwa abba da
umma suma suka gani
.
Kashe gari misalin karfe sha daya na safe
dondazon mutane suka shaida daurin aurena
wato ni aysha imam da ustaz Ahmad sulaiman
saeed tabbas an cika sosai kamar me duk Wanda
kaga bakinsa a gidanmu acikin faraa yake alamar
kowa yayi murna da auren mu ciki kuwa harda
Mamina tsaf ta shiryani cikin hadadden leshi mai
kalar sararin samaniya da adon ja ajiki tamkar
yar tsana haka na fito cas dani ko wa ya yaba da
kwalliyar saidai Abu daya daya bata kwalliyar
hawayen dayake ambaliya a idona ba kukan
komai nakeba sai na tsananin farincikin na zama
MATAR USTAZ dina.
.
Mutane kuwa Dankam a gidanmu tamkar ma
ranar ne ake bikin gabadaya, abinci kuwa kamar
zaiyi magana da bakinsa saboda yarda ake
wadaka dashi komai a wadace nasha nasha
.
Bayan an gama daurin auren ne ustaz dina ya
turo min sako wai naje na gaisa da wasu manyan
abokansa Amma na tabbatar na suturce jikina.
Murmushi kawai nake Idan ya fadi haka saboda
nuna kishin sa dayake sosai akaina kodayaushe
hakan yana da kyau mijinka ya nuna yana
kishinka alama ce ta cewa yana sonka sosai
.
Mami ce ta dora min wata alkyabba akan kayana
ta manyan matan larabawa masu ji da kansu
sannan tayi min rolling akaina da wani mayafi
mai masifar kyau tamkar diyar aljannu haka na
dawo har na Gaza hakuri na tambayi mami inda
ta siyo min wadannan kaya masu kyau.
Murmushi yayi tareda cewa kawata na bawa ta
siyo minsu a Dubai
.
Godiya nayi wa mami sosai sannan naja Asmau
kawata Don ta rakani wajen su angona ustaz
Title :
Naga Rayuwa Part 1
Description : bakomai abba kinmayar dani abokin wasan ki kenan kukane ya kufcemin na shiga rantse masa akan ba komai mikewa yayi tareda fadin Allah ...
Rating :
5