An bukaci jama’a, da suyi nazarin sakonin da fina finai suka kunsa da alfanun sa ga al’uma kafin a yanke hukumci cewa suna gurbata tarbiyar yara.
Rabiu Ibrahim, wanda aka fi sani da sunan Daushe ne ya furta haka a wata hira da wakiliyar dandalin voa Baraka Bashir.
Ya ce ya zabi bangaren barkwanci ne domin ya nishadantar ya kuma wa'azantar mussamam ma ga matasa da suke neman mantawa da al'adun.
Misali kamar yadda malam Bahaushe ke kirkirar karin magana da ma yadda yake juyata a cikin maganarsa ta kuma yi ma'ana tare da nunawa matasa kayan malam Bahaushe da na asali domin a cewarsa ta sun lura matasa na neman mantawa da al'adunsu. Kamar su 'yar shara da shakwara da huluna, da janpa da sauransu.
Title :
Mummunar Fahimta Rashin Adalci Ne - Rabiu Daushe
Description : An bukaci jama’a, da suyi nazarin sakonin da fina finai suka kunsa da alfanun sa ga al’uma kafin a yanke hukumci cewa suna gurbata tarbiyar ...
Rating :
5