Me meera zatayi in ba dariya ba,ta yiwa hibbatu kallon raini tace 'toh
shahararriyar makaryaciya,idan kina shirgawa su umma karya suna yarda,ni
baxa kiyimini ba in yarda,ki nemi wani garan irinki ki mai wannan
tatsuniyar bani ba' ,hibbatu ta watsa hannayenta tare da ta6e baki
tace'daman ban gaya miki hakan ba domin ki yarda ko akasin sa ba,na gaya
miki hakane domin ki san cewa ni ba ba'kuwar arziki bace,kuma ni ba
jahila bace,kaddara ce ta mai dani haka' ,shigowar hajiya ne yasa sukayi
shiru ,hajiya ta dubi meera tace 'ameera kizo ki tayani serving
d'insu,domin suna kan dinning table' sannan ta dubi hibbatu tace 'akwai
matsala ne' ,'a'a' hibbatu ta bata amsa ,suka fice suka barta a
kitchen,sink ta nufa ta wanke fuskarta ,tana sauke ajiyar zuci ,shudewar
mintuna 5 ,meera ta shigo ta dubeta tayi dariya tace'na dawo gareki
hibbatu,wai ke dan Allah bakya jin kunyar yin 'karya ,toh ina son ki
bud'e kunnewanki da kyau ,daga yau bana son na 'kara ganinki a
gidannan,domin kwata kwata ban aminta dake ba,saboda banga ta yadda
halitta irinki zata zamto d'iya ga wannan prestigious family d'in ba ,u r
a liar ,a bloody one',hibbatu idanu jajir ta dubi meera tace 'ameera
enough is enough,i cant take this anymore ,i hve tolerated enough,dnt
mke me loose my temper' ,a mamakance meera ta dubeta baki bud'e,domin
hibbatu's speech was a blow to her,a daidai lokacin mahaifiyar imad ta
shigo kitchen d'in,sai kace an korota ,tana zare idanu kamar wata mara
gaskiya,ta karasa ga hibbatu tana cewa 'hibba ashe kece,idanuna basu min
karya ba, kina raye,ke ce kika zama haka,hibba ashe zaki iya rayuwa ba
tare da kin neme ni ba' ,hibbatu ta rintse idanu tana ja da baya tace
'ammi kiyi hakuri,nisanta kaina daga gareku shine zai zamto dorewar
zamanki a gidan aurenki,ni matacciya ce a gareku ,ammi dan Allah ki koma
falo,kar abbu ya fahimci cewa nice, domin ganin mu tare da ke na nufin
tsinkewar igiyar aurenki da shi,ammi ina kaunarki amma ba yadda na iya'
,ammi ta goge hawaye da ya zubo mata ta fice daga kitchen d'in ba tare
da ta waiwayo ba,meera sandarewa tayi dan tsananin mamaki... Toh fah!
Hibbatu tamu WACECE ITA? Hibbatu hawayene ke zuba daga idanunta,saboda tunowa
da rayuwarta a baya shekaru shida suka wuce,muryar hajiya sukaji tana
cewa'ameera zasu tafi ,ki fito kuyi sallama ' ,meera ta dawo hayyacinta
ta fita suka rakasu mota ,tare da yi musu sallama,kyautar check na
miliyan biyu abbu ya bata,hajiya taso ta hana ,amma abbu yace sam kar ta
kuskara domin meera d'iya take a gareshi,ammi taso su ke6e da ameera
amma ba hali ,haka suka shiga mota suna masu d'aga wa juna hannu,hibbatu
itama tana le'kensu ta tagar kitchen ,bilal ya bud'e gate suka fice
tare da convoy nasu na bodyguards,suna dawo wa falo,alhaji ya dubi meera
yace 'toh ameera,yazama dole ki cire imad daga cikin zuciyarki domin
dana yiwa mahaifinsa maganar aurenku cewa yayi imad is too young
,gaskiya bazai iya aurar dashi ba ,sai ya kamalla ph.d ya samu aiki
tukun ,nayi mai maganar a d'aura aurenku ,in yaso sai ki tare in yayi
settling down ,nan ma yace bai amince ba,in zaki jira imad ki jirashi
kawai,ni kuma nace mai gaskiya bazan zuba ido ina kallonki ,ki tsofe
mini a gida ba,aurar da ke zanyi ,yanzu haka gobe zasu koma kasar da
imad d'in ke karatu ,domin yace 'kila basa 'kasar za'a ayi aurenki,haka
yasa ya baki kyautar naira miliyan biyu,ameera na fita hakkinki na baki
sati biyu ki fitar da miji ko kuma ni in za6a miki mijin aure',meera
kuka take kamar ranta zai fita tace 'abba shikenan na yadda da
hukuncinka gareni,amma ka kara min sati biyu kan satin biyun da ka bani '
,alhaji yace'shikenan ameera na baki wata d'aya,ALLAH yayi miki
albarka',hajiya tace 'amin ', hibbatu kuwa fitowa tayi ta fice ba tare
da ta dubesu ba ,hajiya tana kiran sunanta amma haka tayi kunnen uwar
shegu ta fice daga gidan gaba d'aya ,bilal kuwa bai nemi ya tsaidata ba
,domin shi kanshi yasan cewa ganin iyayenta a gidannan ba karamin tada
mata hankali zai yi ba..meera kuwa haka ta tashi jiki sanyaye ,ta had'a
kan kwanuka ta wankesu ,ta kira direba ta bashi abincinsa tare da na
maigadi,dakinta ta wuce tana mai tunanin abubuwa guda biyu ,rabuwarta da
imad ,gaskiyar lamarin hibbatu....Hibbatu kwata kwata bata nemi abinci
ba,domin tunanin rayuwarta a baya ne ya addabeta,da kyar ta samu tayi
salloli tare 'kudurtawa a ranta babu ita babu zuwa gidan alhaji daga yau
.... * * * washegari ko da bilal yazo yin wanka ,gaisheshi kawai tayi
,amma kwata kwata bata bashi fuskar da zai yi mata maganar iyayenta
ba,asalima toilet ta shiga tayi zamanta akan masai ,ya gaji da jiranta
ta fito ,sai knocking kofar yayi tare da cewa hibbatu lafiyarki kuwa ,ta
daga murya tace lafiyata kalau ,ba hayar ce akwai tauri ,yace 'toh ni
na wuce ,adawo lafia kawai tace masa,sai da ya fice daga gidan ,sannan
ta fito ta fara aikace aikacenta.... Meera kuwa tun daren jiya take
trying imad a waya,amma not available,tayi masa message ta whtsapp ,nan
ma not delivered,hankalinta ya tashi ,ta rasa yaya zatayi ,damuwa tayi
mata yawa,a haka hajiya tashigo d'akin ta sameta tace 'ameera lafiyarki
kuwa baki fito ba,kar fa kisa damuwa a ranki,ki fawwalawa Allah
lamuranki' ,meera tasa hannu ta riko hannun hajiya ta zaunar da
ita,'umma ko kad'an bana damuwa ga hukuncin da abba ya yanke a
gareni,domin ya bani time ,kuma ya so na auri imad,amma abbu ya
hana,damuwata shine rashin samun imad a waya ,tun jiya da daddare nake
trying wayarshi not available,kuma umma ina son muyi wata magana',hajiya
ta shafa fuskar meera tace 'ina jinki,menene',meera tace 'kin tuna
lokacin da mukaje gidansu imad ,munga family picture d'insu ,har nake
tambayar wacece yarinyar dake cikin hoton,ammi tace yayar imad ce,kuma
abbu yace amma ta rasu ',hajiya tace 'tabbas anyi haka ,itace 'yarsu ta
fari ,sai imad ,amma Allah yayi mata rasuwa kamar yadda abbunsu ya
fad'i'' ,meera ta sauke ajiyar zuciya tace 'umma ni ko wannan yarinyar
tana kama da hibbatu ,ko ke baki lura ba',hajiya ta d'an yi tunani tace
'hakane kuwa ,sai da kika fad'a ,na lura da haka,amma kinga kamanni ne
kawai,amma nasa basu da ala'ka da hibbatu,gashi kuma hibbatu lafia
batazo ba,jiya ma kamar a fusace ta bar gidan Allah yasa lafia' ,meera
tace 'aww kina nufin yau bata zo ba' 'eh bata zo ba gashi it's already
to eleven'',meera tace 'bara na shirya ,sai in kar6i address gun mijinta
in dubata ',hajiya a mamakance tace 'ki dubuta? ,yaushe kuma kuka
shirya,bayan naga jiya sai hantararta kike ',meera tayi dariya tace
'umma bazaki gane ba,kin manta kince min ta kawomin abun kari ta
lalla6ani na cinye ,kuma kinga danace ina son tsire kamar yadda tace
miki,kinga da tasiyo naci,kinga kenan mutuniya tace ' ,a zuciyarta kuwa
cewa take 'hibbatu da 'karya kamar kudin cizo,amma ya zama dole in je
gurinta domin sanin wacece ita ,is she imad sister',amma a zahiri ta
dubi hajiya tace'bara nayi wanka in shirya' ,ta tashi ta shige
bathroom.... ABDULAZIZ ISMA'IL