Muryar meera ne ya katse shan ruwan o.r.s ga Hibbatu,'ke me kikeyi
anan,zo muje mu kai masu drinks' ,hibbatu tayi magwas tare da 'karasawa
ta d'auko glasscups tana wankewa,meera ta d'auko tray ta bude firij ta
lodi drinks tare da cewa 'hibbatu ki biyoni da cups d'in' ta fice
,hibbatu kirjinta na dukan 3 3,domin bata shirya fuskantar mutanennan
ba,idanunta suka hango mata ragowar flour a bowl,da sauri tasa ruwa ta
kwa6a tare da shafawa fuskarta ,sannan ta d'auraye hannayenta,ta d'ibi
cups d'in ta nufi parlour kafafunta suna hard'ewa, a sanyaye tayi
sallama tare da russunawa ta gaishesu,meera kuwa kamar ta sha'keta don
takaici,haka ta karbi cups d'in tayi serving drinks ga iyayen
imad,alhaji ya dubi hibbatu yace 'meye samu fuskarki' ,washe hakora tayi
tace 'kesbi ne ya fesomini akan fuskar' ta juya da hanzari ta bar falon
ta wuce kichin,tana sauke ajiyar zuciya ,meera ce ta shigo kichin d'in a
fusace tace 'ke hibbatu wani irin iskanci ne wannan ,me kika shafawa
fuskarki,da kin firgitasu fah,me yasa baki da nutsuwane,komai naki babu
kimtsi,bagidajiya kawai,makaryaciya kawai,ko a gidan uban wa kika samo
kesbin oho'' ta had'a da jan dogon tsaki ta d'ora da cewa 'hibbatu
kinada problem wlh ,i tink mental problem '' da sauri hibbatu ta d'aga
hannu ta katseta tare da cewa 'dakata ameera,ki kama harshenki ,wasa
bakin naki ya isa haka,me kike ta'kama dashi ne,har kike mini wani gani
gani,kamar yadda kike yar gata ga iyayenki ,shekara shida da suka wuce
nima yar gatan ce,kamar yadda kike ta'kama da yin karatu a kasar waje
,shekara shida baya na kamalla karatuna a kasar waje ,kar ki nemi kice
zaki zageni ameera,domin mutanen da kike rawar 'kafa agaresu har kike
neman cimin mutunci a kansu toh iyayena kinga na fiki ala'ka dasu,imad
d'in dakike kulaficinsu so ,d'an uwana ne ,uwa d'aya uba d'aya,kinga
kenan nafiki kusanci dasu fiye da ke '' .... Toh anya hibbatu ba sharota
tayi ba?Abdulaziz Ismail
Title :
Mijin Haya Part 8
Description : Muryar meera ne ya katse shan ruwan o.r.s ga Hibbatu,'ke me kikeyi anan,zo muje mu kai masu drinks' ,hibbatu tayi magwas tare ...
Rating :
5