Hibbata ta tura d'akin ta shiga da sallama ,meera bata d'ago ta dubeta
ba,hakan yasa hibbatu ta nemi waje ta zauna,ta kurbi custard d'in sannan
ta dubi meera da fara'a tace 'ameera kenan,ba a fushi da abinci' ,wani
kallo meera ta zabgawa hibbatu tare da cewa 'wacece ke,me ya kawo ki
d'akina',hibbatu ta d'ebo dankali da ferfesu da yatsunta ta kai baki sai
da ta taune ta dubi meera tace 'sunana hibbatu ,matar bilal maigadin
gidannan' ,meye kawo ki dakina? Hajiya ce tace na shigo nan in zauna in
ci abinci' ,tsaki meera taja tare da kauda kanta ,hibbatu ta cinye
abincin tas,ta shanye custard d'in tas,sannan tayi wata hadaddiyar
gyatsa ,hakan yasa meera ta juyo ta dubeta,hibbatu tana lashe yatsunta
tace'ameera mahaifinki yayi gaskiya, ya kamata kiyi aure ,amma tukunna
wanene imad d'in nan,mai kud'i ne' ,a kasaushe meera tace 'keep ur mouth
shut and get lost',hibbatu ta mi'ke tana goge hannu jikin zaninta tace
'dakata y'ar nan bani na kar zomon ba',ta kwashi cup da plates ta fice
tare da sakin wani gyatsar,a falo take cewa hajiya 'ameera tana da
kirki,kinga taji lallashi ta cinye abincin tas,ku kyaleta dani,fushi
take daku,kar ku shiga d'akin' ,hajiya ta yi murmushi tace 'hibbatu kin
kyauta da ameera ta samu ta ci abinci nan',hibbatu ta bata amsa da cewa
'tas kuwa ta cinye'! me zaku ce game da abin da hibbatu tayi
kitchen,bayan hajiya tace ta d'au abin karinsu a kicin,
ita da bilalta dauka ta kaiwa bilal tace 'ya ci kuma ya
ajje mata sauran zata wuce dashi gida..in ta tashi
tafiya * * * karfe 2:00pm suka kamalla had'a abincin
rana,meera kuwa tana d'aki bakin ciki da fushi ya
hanata fitowa ,kuma hajiya bata le'ka dakin nata ba
,domin hibbatu tace ta kyaleta,hajiya ta dubi hibbatu
tace 'je ki kira mini ameera tazo tayi having lunch',
'kyaleta hajiya ,kar a matsa mata ,na manta ban gaya
miki ba tace tsiran hanta zata ci' ,'tsiran hanta?', 'eh
tsiren hanta,ana siyarwa anan bayan layi,ki kawo kud'in
na siyo mata' ,hajiya tace 'toh',taje ta d'auko dubu
d'aya ta bata,da sauri hibba ta fice bayan ta karbi kudin
,wajen tasiu mai tsire taje tace ya zuge mata tsiren 700
daban ,na 300 daban,amma zata dawo ta d'auki kullin
na 700 d'in ,ta karbi kullin na 300 ta dawo gidan,dakin
meera ta nufa ,tana shiga ,har meera zata fara masifa
,hibbatu ta katseta tare da jefa mata kullin tsiren tana
cewa 'ungo kici in kin ga dama ,domin wannan fushin
da kikeyi,wuri kika samu ,gata da sangarta ne suka miki
yawa ,amma in ba haka ba me abin fushi da har zakiyi
wa kanki horan yunwa,hmmm banga laifinki ba ,domin
kin saba cin dadi,dole yau kiyi yajin aiki' ,bata bari
meera tayi magana ba,ta fice daga dakin,a hanyar
shiga kitchen ta had'u da hajiya tace 'na kai mata
tsiren,ni zan wuce',hajiya tace 'nagode hibbatu da
dawainiya,ki dau abincin naku,kuma dan Allah gobe
kizo da wuri zamuyi ba'ki',sannan ta bata dubu d'aya
,hibbatu ta amsa da 2 hands tana cewa 'nagode hajiya
Allah ya kaimu goben',ta nufi kitchen ta kwashi kulolin
abincin ta fice ,ta ajjewa bilal nashi abincin,ta d'au abin
karin da yaci ya rage mata da safen,ta had'a da
abincinta na yanzu, ta mai sallama ta fice ,ta nufi gun
mai tsire ta karbi kullin tsirenta ,ta nufi gida da abinci
ni'ki ni'ki,tana murna da jindadin garar da ta samu
yau.... Kunga laifinta?
meera ta rasa me zatayi,kuka ko
dariya,kamshin dake fita daga ledan ne yasa ta kunce 'kullin ,tuni
bakinta ya had'a miyau abinka da mutumin da bai ci abinci ba tun
safe,hakan yasa ta cinye tsiren hantar tas ,sannan ta fice ta nufi
kitchen ,ta samu ruwa tasha ta gyatse ,hajiya ta dubeta tayi murmushi
tace'ameera anga daman fitowa ko? ,meera ta fuske ta kau da kai, 'gobe
iyayen imad zasu zo,ina son ki zauna cikin shiri',da gudu meera ta
rungume hajiya tana cewa 'umma dagaske' ',kwarai kuwa ,hakan yasa meera
ta huce ,ta manta da duk wata damuwa da zancen hibbatu * * * washegari
hibbatu ta tashi da guduwa ,amma haka ta kokarta ta yi wanke wanke ta
gyara gida,tayi wanka ta shirya,domin bilal a shirye ya shigo gdan ya
sameta ,tayi mai sannu da zuwa tare da ce mai ta rage masa tsiren hanta
,tayi mai sallama ta cicci6i kuloli tare da ce masa sai ya iso... Bilal
murmushi yayi ,ya gyad'a kansa,8:00am hibbatu tana cikin gidan alhaji,ta
gaida hajiya,sannan ta fara da goge goge da share share ,bisa umarnin
hajiya ,bayan an gama yin breakfast,hajiya ta had'a hibbatu da direba ya
kaita kasuwa tayo cefane .... Karfe 2:00pm suka fara had'a lunch
,different varieties of dishes,snacks nd drinks,har da meera a
kitchen,domin ita ce jagora saboda gwana ce a fannin girki ,sai
tsangwamar hibbatu take in taga tasa hannu a wani abun ,sai da hajiya ta
tsawatawa meera,sannan ta kyaleta ,hibbatu kuwa tana gefe tana raba
eyes ,aikinta wanke abinda aka 6ata,a haka aka kamalla dafe dafe da soye
soye ,aka jera a dinning,hajiya da meera suka wuce d'aki domin su fesa
wanka da kwalliya ,hibbatu gefe ta samu a kitchen ta zauna ,ta cika kofi
taf da ruwan O.R.S tana sha tare da lumshe ido.....dirin motoci da taji
suna shigowa hakan yasa ta le'ka ta tagar kitchen,motoci ne sun kai 7
sukayi parking,wasu mutane da ba'ka'ken coat suka bud'e kofofin wata
bakar limo ,dattawa ne mace da namiji taga sun fito daga motar,alhaji ya
nufi namijin ya rungume yana cewa 'welcome my friend' ,hibbatu ta
gigice da ganin wannan mutanen hakan yasa cikinta yayi wani irin
juyawa,da sauri ta kafa kofin ruwan o.r.s a bakinta tan d'id'd'ika tana
sauke ajiyar zuciya akai akai,hakazalika bilal da ya maida gate ya rufe
,ya koma benci ya zauna tare da zuba tagumi yana mamakin ganin mutanen
nan a gidan alhaji..... ABDUL ISMA'IL
Hibbatu ta
wuce