Ta tand'e bakinta kamar wata mayya (don ta ambaci d'awisu),sannan ta
fara had'a kan kwanika ta wankesu,ta share gidan,tayi wanka,ta sa
kayanta masu d'an kyau,har ga Allah batajin yunwa (ina yunwa ga mutumin
da yacinye abincin mutane biyu),ta suri kulolin ta fice tare da kulle
gidan,gudu gudu sauri sauri ,har ta iso gidan ,ta buga gate ,bilal ya
tmby wacece ,ta bashi amsa da nice ,ya bud'e ta shige ,sannu da duty
tace mai ta wuce ciki ,ganin bakowa a falo yasa ta zarce kichin anan ta
tadda hajiya tana had'a b/fast,gaisheta tayi cikin ladabi,ta ajje kuloli
,ta cire mayafi ta tamke a kugu ta fara zuba aiki,hajiya na shi mata
albarka ,ita ko cewa take ,'yiwa kaine hajiya,ni nan zan maye miki
gurbin yar aikin ki har sai ta dawo',haka suka had'a komai aka jera
dinning,alhaji da meera duk sun hallara,haka zalika hajiya ,kafin afara
cin abinci ,alhaji ya dubi meera yace 'ke ya batun aure ne wai,wlh
wannan karatun ma ba'a son raina na barki kika tafi ba ,amma haka na
hakura na barki,kuma kin kamalla sai ki fidda miji in aurar dake' ,meera
a shagwabance tace 'IMAD ne dai za6ina' ,alhaji ya dubeta yace 'kin dai
san mahaifinsa yace bazai yi masa aure ba sai ya gama ph.d ya soma
aiki', 'nasani abba zan jirashi ya gama din ' ,'ba dai a gidana ba,in
barki ki tsofe,kina jiranshi ,ki fito da miji kawai nan da sati biyu ,ko
kuwa ni in za6a miki,period',hajiya tace 'ku bar maganar nan mu ci
abinci' ,fuu meera ta tashi cikin fushi ta wuce d'akinta ,duk abinda ya
faru akan ido da kunnen hibbatu akayi,'karasowa tayi ta gaida alhaji
tace 'alhji a d'inga hakuri ,yaran yanzu ne sai a hankali' ,dayake
alhaji yasan wacece ita hajiya tayi mai bayani,hakan yasa yace 'kyaleta
kawai,ni dai nagama magana' ,hibbatu tace 'bara na kai mata abin kari in
lalla6ata taci ,kar ta zauna da yunwa' ,ta d'au plate ta zuba dankali
da farfesun kayanciki,ta had'a custard da zabga madara,sannan
tace'hajiya ina ne d'akin ameerar' ,hajiya tayi mata nuni ,ita kuma ta
wuce d'akin ri'ke da b/fast d'in meera.... Hakkin mallaka :ABDULAZIZ ISMA'IL
Title :
MIjin Haya Part 6
Description : Ta tand'e bakinta kamar wata mayya (don ta ambaci d'awisu),sannan ta fara had'a kan kwanika ta wankesu,ta share gidan,tayi ...
Rating :
5