Hibbatu tana tafe
rungume da kuloli tana rera wa'kar 'ahayye sama
ruwa kasa ruwa samarin duniya wazobia',har ta
iso gida ,ta sauke kuloli ta ciro ma'kulli ta bud'e
kwad'on da ta kulle kyauren ,ta kwashi kulolin
abincinta ta shige ,falo ta nufa ta ajjesu sannan
ta fito tayi alwala ta had'a azahar da la'asar ta
sallacesu,ta janyo kulolinta ta fara aikawa
tumbinta friedrice hannu baka hannu kwarya tana
had'awa da tsokar kaji,tana karkad'a kafafu tana
juya kai kamar wata yar maye,kwarewar da tayi
ne yasa tace 'oh hajiya ta manta bata had'oni da
lemu ba,ita kuma haka akeyi,abaka abinci bbu
abin sha',ta lashe yatsunta ta mike ta sa mayafi
ta fita kantin saleh ta siyo sprite d'in roba biyu
da purewater cikin dubu biyun da hajiya ta bata
,ta dawo gida ta d'ora daga inda ta tsaya ,ta
cinye abincin tas,ta taune kasusuwan kajin
murus,sannan ta kora da sprite da ruwan leda,sai
gyatsa take fesawa tare da shiwa hajiya
albarka... * * * washegari da safe bilal yazo yayi
wanka ya chanja tufafi,da yake gidan nasu babu
nisa da gidan dayake gadi ,sannan ya umarci
hibbatu da ta bashi kulolin ya tafi dasu ,ita ko
tace batasan zance ba,wllh da kanta zata maida
masu,wato ba'kin ciki yake mata ,haka ya hakura
ya fice daga gidan ,ita kuma tana ce mai sai ta
iso,a ranta tana cewa 'ni shashar ina ce da zan
baka kuloli ka mayar,i ni duk abinda zai sada ni
da wannan gidan son sa nake,ina sane na taho
da kulolin ehe! Inaga yau 'kila su yanka
d'awisu,ina zan bari wannan abin arzikin ya wuce
ni' .... Muje xuwa menene ra'ayinku game da
hukuncin hibbatu ?
Title :
Mijin Haya Part 5
Description : Hibbatu tana tafe rungume da kuloli tana rera wa'kar 'ahayye sama ruwa kasa ruwa samarin duniya wazobia',har ta iso gida...
Rating :
5