Ta cigaba da taunar naman tana rugurguzar 'kashin cinyar kazar da
ha'koranta har sai da 'kashin ya koma gari sannan ta tofar dashi ,ta
d'auko wata tsokar(banza ta samu) ta kai baki ta yago tsoka da
ha'koranta ta mur'kushe ,bilal ya dubeta yace 'hibbatu me kuma kika ce
masu ,har kika samu guzurin wannan gara haka',kyakyacewa tayi da dariya
sannan ta lamushe ragowar tsokar da ke hannunta ,sannan ta dubeshi tana
sakace da harshenta tace 'ce musu nayi kai ka turo ni ,in tayasu aiki'
ta labarta mai dai yadda sukayi da hajiya ,bilal ya gyad'a kai yace
'hibba ikon Allah,ke kuma haka ki ka koma' ,ta dubeshi bayan ta sa yatsa
ta cire naman da ya ma'kale mata a tsakiyan hakora tace 'talauci babu
abinda baya sa mutum yayi,kai dai kawai kasa hannu kaci ',girgiza kai
yayi yace 'ci kayanki' ,ta dubeshi tace 'shinkafar ma bazakaci ba ',yace
'eh duk ki had'a kici,ki maida masu kuloli',hibbatu ta mi'ke ta gyara
zaman mayafinta ta dubeshi bayan ta d'au kuloli tace 'kayi wa kanka,kuma
kula sai gobe zan dawo masu da ita,domin daga yau gidan nan ya zama
wajen zuwana' ta juya ta yi hanyar gate tana cewa 'sai anjima',ya tashi
ya bud'e mata gate ,yana d'aga mata hannu ta fice,shi kuwa famfo ya nufa
domin yin alwalar sallar la'asar..... Menene ra'ayinku Hakkin mallaka:
ABDUL AZIZ ISMA'IL
Title :
Mijin Haya Part 4
Description : Ta cigaba da taunar naman tana rugurguzar 'kashin cinyar kazar da ha'koranta har sai da 'kashin ya koma gari sannan ta tofar ...
Rating :
5