Hibbatu ta cire silifas d'inta tare da sa hannu ta d'auka ta
rungumesu,tana mai raba idanu,wata 'yar dattijuwa ta gani ta fito daga
wata kofa zata shiga wata kofar ,d'aga murya tayi tana mai kwatsa
sallama ,chak matar ta tsaya ta juyo tare da amsa sallamar, cikin sakin
fuska tace 'baiwar Allah sannu da zuwa,daga ina?' ,hibbatu a ranta bata
raba d'ayan biyu wannan itace matar alhaji ,mahaifiyar meera ,haka dai
ta 'karasa gareta tare da russunawa,a ladabce tace'hajiya daman bilal
maigadin gidannan,kuma mijina ,ya bani umarnin inzo tayin aiki gidannan,
domin yau 'yar alhaji zata dawo daga turai ',hajiya ta murmusa tace
'ALLAH sarki bilal ,ya ko kyauta,daman yar aikin tawa ta tafi gida,taso
mu'karasa kitchen d'in ki kama min in gama,gashi ameerar ta iso ban gama
girki ba,ya sunanki? ',hibbatu ta mi'ke tare da bin bayan hajiya,tana
sanar da ita sunanta,hajiya ko sai fad'in kirkin bilal take ,tana mai
cewa hibbatu tayi sa'ar miji,haka dai suka kamalla girke girke da abin
sha,wanda yawun hibbatu duk ya gama tsinkewa ,jurewa kawai takeyi,bayan
sun jera akan dinning,hibbatu tayi wanke wanke tare da gyara kitchen
d'in,hajiya ta shigo da fara'arta tana mata sannu da aiki,sannan ta
umarceta da ta kwashi coolers din abincin chan ta tafi dasu ita da
mijinta suci had'i da bata dubu biyu ,hibbatu tasa hannu biyu ta kar6i
dubu biyun , ta washe jajayen ha'koranta tana zuba godiya ta d'ebi
coolers ta fice tare da yiwa hajiya sallama,ta 'karasa gun bilal dake
zaune kan benci ya zuba tagumi yana zaman jiran fitowarta,zama tayi tana
mai washe baki ,ta kunce ha6ar zaninta ta 'kulle dubu biyunta ,sannan
ta bud'e kular(cooler) kaji tasa hannu ta d'au cinya ta kai baki tana
lumshe idanu ,bakinta cike da tsokar nama tace 'amma Allah ya tsunduma
hajiya a aljanna ' ,ta 'kara kai chafka da ha'kwaranta ta yago tsoka ta
taune ,dad'in na ratsa kunnenta ,idanu a lumshe ta dubi bilal tace 'kasa
hannu muci mana ka tsaya kallona'....... Ko kune mezakuce wa hibbatu
Abdulaziz Ismail
Title :
Mijin Haya Part 3
Description : Hibbatu ta cire silifas d'inta tare da sa hannu ta d'auka ta rungumesu,tana mai raba idanu,wata 'yar dattijuwa ta gani ta fit...
Rating :
5