wata had'addiyar balarabiyar matashiyar budurwa
daga motan yasa bilal ya biyewa hibbatu wajen
kallon wannan had'addiyar budurwa a ransa yana
mai tasbihi ga Allah...hibbatu ta maido dubanta
ga bilal,ganin ya saki baki shima yana kallon
wannan budurwar ma'abociyar kyau yasa a take
kibiyar kishi ya soketa,tasa hannu ta bugi
'keyarsa tana cewa 'haba bilal,akwai wata halitta
da zata gigita ka bayan ni?' ,murmushi yayi a
sanyaye yace 'babu kam hibbatuna,ina ni ina yar
masu gida,tsakanina da ita sai dai kallon ,ke d'in
ma danake aure ya na 'kare ,malajawa kawai kike
dani' ,dariya hibbatu tayi tare da kunce d'amarar
da tayi da mayafinta tana cewa 'ashe baka manta
da matsayinka,hakan na da kyau ',sannan ta yafa
mayafinta tana mai cewa cikin rad'a 'kace kuma
yar masu gidan ce,waya gaya maka haka' ,ya
bata amsa da cewa'alhaji da kanshi yake ce mini
wai yau d'iyarsa MEERA zata dawo daga cyprus
domin ta kamalla karatu' ,hannu akan kirji
hibbatu ta maimaita 'sifurus?' ,sannan ta juya ta
nufi cikin gidan tana cewa 'banga ta zama
ba,dole in 'kulla aminci da wannan 'yar ,ko nima
zan yagi rabona' wuf ta shige kofar da zai sadata
da cikin gidan,bilal ya koma kan bencinsa ya
zauna bayan ya rufo gate d'in yana mai mamakin
hibbatu,ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa
'ALLAH yasa kar hibbatu tayi sanadin rasa aikina'
Title :
Mijin haya part 2
Description : wata had'addiyar balarabiyar matashiyar budurwa daga motan yasa bilal ya biyewa hibbatu wajen kallon wannan had'addiyar budu...
Rating :
5