Bilal ya juya ya dubeta da kyau ,amma ya kasa cewa komai ya kad'a kansa a
sanyaye ya fice daga d'akin... * * * a bangaren meera a daren jiya ta
raya darenta da salloli,ta kai kukanta ga Allah bisa wnn lamari in har
aurenta da bilal akwai alkhairi toh Allah ya tabbatar da hakan,in kuma
akasin hakane toh Allah ya tarwatsa lamarin ya kuma za6a mata mafi
alkhaira bangaren meera a daren jiya ta raya darenta da salloli,ta kai
kukanta ga Allah bisa wnn lamari in har aurenta da bilal akwai alkhairi
toh Allah ya tabbatar da hakan,in kuma akasin hakane toh Allah ya
tarwatsa lamarin ya kuma za6a mata mafi alkhairi! Misalin karfe 7:00am
meera ta fito daga wanka zuciyarta fes,ta shirya cikin wani
material,tayi light make up,a kitchen ta tadda umma ,bayan sun gama
kamalla had'a breakfast sun jera a dinning,alhaji ya fito shima ya
samesu a dinning ,suka hadu sukayi b/fst ,bayan meera ta kwashe kwanukan
ta wanke,ta dawo ta samu iyayenta a falo,gefen abba taje ta zauna
,kanta a sunkuye,abba ya dubeta fuskarsa dauke da murmushi yace 'ameera
lafia,meyafaru' ,meera tayi jim tare karanto addu'oi a ranta sannan tace
'abba na samu mijin aure,kuma yana son a bashi dama ya turo
magabatansa','toh toh masha Allah,wanene shi,d'an gidan waye,kuma aikin
me yake?' alhj ya tmby ,meera kanta a sunkuye ta tattaro kalamai da kyar
tace 'bilal ne ,maigadin gidannan' ,umma me zatayi in ba salati ba tana
tafa hannaye tace 'ameera ! Bilal mai gadi zaki aura ,wato mijin
hibbatu,wannan i cin amana ne da tsantsar son kai,haba ameera me hibbatu
ta tare maki da zaki saka mata da aure mata miji',alhji ya katseta yana
cewa 'meye haka hjy,menene a ciki,laifi ne idan ta aureshi naga yana
damar ya auri mata hud'u,ku fa mata tunaninku karami ne wlh wani
zubin,in dai sun aminta da juna ,i shikenan! Ke ameera kina son shi,kuma
kun aminta da junanku?' 'eh abba' ,'toh tashi ki tafi ,zamuyi magana da
bilal d'in ,sum sum meera ta tashi ta bar falon ,hjy ta rakata da
harara,alhaji kuwa kishingida yayi tare da yabawa da za6in 'yarshi a
zuciyarsaa ,domin ya yaba da halayen bilal! * * * meera tana shiga d'aki
ta ji wayarta na ringin,sabuwar number ta gani ,tana d'auka taji muryar
hibbatu tana cewa 'ameera yaya,kin gayawa abba kuwa?' ,meera ta
labartawa hibbatu yadda suka yi da iyayenta,hibbatu tace 'toh shikenan
zanzo gdan anjima,ki bar ni da hajiya kawai zata sauko ne....
Bilal zuciyarsa a kuntacce ya gama shiryawa ya fito zai tafi gidansu
meera,kicibus sukayi da mutum a kofar gda ,mutumin yayi wa bilal sallama
tare da mika masa carkey yana cewa'wai gashi abawa haj.hibbatu ,angama
yiwa motar komai' bilal ya koma cikin gda ya gayawa hibbatu ta fito ana
nemanta ,hijab ta saka ta fito ganin mutumin yasa ta washe baki ta amshi
mukulli tana cewa 'komai is ok ko',sannan ta koma cikin gda ta d'auko
kudi ta bashi,bilal da ya gama tsinkewa da lamarin hibbatu,kawai sai ya
kada kansa ya tafi gdan aikinsa...
¤ ¤ ¤
Bilal zaune akan benci ,ya zabga tagumi, duk abin duniya ya
isheshi,saboda hibbatu tagama shayar dashi ruwan mamaki,alhaji ne ya
karaso yana mai masa sallama da sauri bilal ya amsa yana mai
russunawa,alhaji ya amsa tare da bashi umarnin ya tashi ya zauna zasuyi
magana,bayan alhaji ya zauna akan bencin , gyaran murya yayi sai ya dubi
bilal yace 'mal.bilal ameera tazo min da wani batu d'azunnan da
safe,wai kunyi amanna da junanku ,kuma kana neman ixinin ka turo
magabatanka a yi maganar aurenku' bilal sai da ya had'iyi wani mugun
yawu ,kanshi a 'kasa ya fara labartawa alhaji yadda sukayi da hibbatu da
safen nan da kuma duk abinda ta gaya masa akan batun MIJIN HAYA! 'MIJIN
HAYA?' alhaji ya maimata ransa a 6ace 'ni ameera zata mayar abokin
wasanta,wato ni zata rainawa wayo ko?,imad ya gama hure mata kunne
ko,toh me marabar wannan aure da auren kisan wuta ' alhaji ya cigaba da
masifarsa ,bilal dai shiru kawai yayi ,alhaji ne ya ja numfashi sannan
ya dubi bilal yace'zan so ka gayamin asalinka da labarinka?' bilal bai
ji ko d'ar ba ya labartawa alhji labarinsa daga A har Z, bai rage komai
ba ,alhaji wanda tuni idanunsa yayi ja don tausayi,ya dubi bilal yace
'kana nufin kai surukine ga alh.shoaib,hibbatu kuma 'yarsa ce da yake
cewa ta rasu?' 'kwarai da gske,hakane alhaji',alhaji yasa hannu ya dafa
kafad'ar bilal yace 'bilal kar ka damu,rayuwa ta gaji kalubale daban
daban,amma zan taimaka maka ,kuma zan baka aiki a kamfanina,ka kawo min
takardunka gobe' bilal ya durkushe yana zabgawa alhaji gdy,alhaji yace
'kar ka damu bilal ,ynxu ni da kai mun zama d'aya,domin a yau na kara
tabbatar da cewa kai mai ri'ko da gaskiya ne,alfarma d'aya nake son kayi
mini bilal in babu takurawa',da hanzari bilal yace 'haba alhaji kafi
karfin neman alfarma a guna,sai dai kabani umarni in bi' alhaji ya ja
fasali sannan yace 'zan baka sadaki,zan baka kud'i ka had'a lefe,zan
baka gida da mota,kuma zan baka ameera a matsayin matarka ta aure,bana
fatan saki ya shiga tsakaninku da ita,ita matar taka ka barta kawai ka
bita a haka,tunda hakan ta za6awa kanta,ka barta ta ci kud'in uban
ta,nima nan baxan nunawa ameera cewa nasan gskyr manufarsu game da
wannan auren ba,zan koya masu hankali duk su ukun(hibbatu,meera da
imad),ka shirya nan da sati biyu zan aura maka ameera!.....
Murna!,kuka!,farin
ciki!,suma!,shid'ewa! Bilal dai ya rasa wanne zai yi,kawai sai ya kama
yiwa alhaji godiya ,sannan yace 'amma alhaji,wani hanzari ba gudu
ba,kakata kafin ta rasu ta yi min wasiccin da in rike hibbatu amana ,kar
na kuskura in musgana mata ta hanyar yi mata kishiya ',alhaji ya
murmusa yace'bilal kar ka damu da wannan,naga ita matar taka ce ta bada
HAYARKA ,wato dai ita ce tayi ma'karkashiya wajen had'a wannan aure ,ka
kyaleni da ita kawai,sai dai kuma in ameerar ce ba kaso,sai a fasa auren
,domin baxan so in tilasta maka ba',a hanzarce bilal yace 'ko kad'an
alhaji ba nufi na kenan,ko da ameera ba ta kasance jininka ba,matar so
ce ga duk namijin da ya san ciwon kansa .....! Alhaji yace 'shikenan
Allah ya tabbatar mana da alkhairi,kar ka manta gobe kazo da takardunka'
,sannan ya tashi ya shige cikin gida ya bar bilal da farin cikin
zuciya! Hibbatu ce ta turo gate d'in ,tana sanye da doguwar hijabi,kallo
d'aya bilal yayi mata ya d'auke kansa,karasowa tayi gareshi tana cewa
'sannu da duty,alhaji yayi maka zancen?,kunyi magana da shi?,ganin bai
bata amsa ba,sai ma tashi da yayi ya d'auko radio yana kokarin
kunnawa,hakan yasa juya 'keyarta ta shige cikin gidan ,a falo ta tadda
alhaji da hajiya a zaune,bayan tayi sallama sun amsa,sai ta zube tana
kwasar gaisuwa,alhaji ne yace ta zauna zasuyi magana ,hibbatu kuwa tuni
ta tsure tazata asirinsu ne ya tonu ita da meera,haka dai ta xauna a
kasan carpet,alhaji yayi gyaran murya yace 'hibbatu ,ina son kiyi hakuri
,ki yarda kaddara ,domin ko wanne bawa akwai tashi kalar kaddara,ina
son ki yayyafawa zuciyarki ruwan sanyi' ,sannan ya cigaba da cewa
'mijinki ne ya ke son ya 'kara aure' ,a razane hibbatu ta d'ora
hannayenta a kan kirjinta ta maimata 'aure?' ,hajiya tace 'dole ki
razana mana ,ana son an ci miki dunduniya',hibbatu tace 'tirkashi,namiji
ledan guduwa,yanzu bilal aure zai 'kara,lallai ya nuna min halin maza
tsirararsa' ta cigaba da surfa maganganu,hajiya ita ma tana tayata
[hibbatu tana sane sarai, tayi hakan ne kawai dan kar ta nuna zalamarta!
Shima alhaji yana sane ya biyo mata ta hakan],can alhaji yace 'ku
dakata haka,ya isa haka' ya dubi hibbatu yace 'shikenan zan sa bilal ya
janye maganar auran,daman ameera ce taxo min da zancen wai yace xai turo
magabatansa,domin sunyi amanna da junansu,na kuma tuntu6eshi da
zancen,yace hakane,amma ke yake jiyewa,ni kuma nace in har baki amince
ba,toh sai dai su hakura da junansu' ,hibbatu tayi sauri tace 'alhaji
kana nufin ameerar gdan nan bilal yake son ya aura ,wallahi na amince,i
dana san itace matar da bazan ki ba,haba i ameera yar uwata na d'auketa'
hajiya sororo ta tsaya kallonta sannan tace 'hibbatu wato kin amince
ameera ta zama kishiyarki' ,'yar uwa dai hajiya ba kishiya ba,domin
tunda har ta iya son mijina kuma ta amince ta aure shi ta zauna damu,ba
tare da tayi duba ga talaucin mu ba,toh ni saboda me zan 'ki ta,hajiya
kar ki damu wllh na amince',alhaji yace 'toh shikenan masha Allahu,ALLAH
yayi maku albarka ' kanta a sunkuye tace 'amin'... Alhaji ya d'auko waya ya bugawa direba waya ya bashi
umarnin da ya turo masa bilal, bayan wasu 'yan mintuna sai ga bilal ya
shigo palon da sallama ,ya nemi gu ya zauna daga gefen hibbatu bayan ya
gaishesu,alhaji yayi gyaran murya yace'toh mal.bilal,matarka ta
amince,nima na amince,sai ka shirya nan da sati biyu za'a d'aura maku
aure kuma ta tare,gobe kuma zaka fara aiki a kamfanina na saida
motoci,kuma zaka za6i gida daya daga cikin gidajena,amma dai kawai tunda
kace gidan da kuke zaune a ynzu na gadonka ne,za'a fara gyaransa gobe
in yaso gobe kai da matarka ku dawo gidannan da zama in an gyara sai ku
koma' hibbatu ta fara washe hakora tana zabga godiya tana cewa 'kaga
aure mai kashin arziki,ni alhaji ko zaka aurawa bilal mata uku,in dai
jininka ne nasu ba damuwa wllh banida haufi',murmushi kawai yayi,hajiya
itama tace 'toh Allah ya tabbatar da alkhairi,daman ke nake jiye
mawa,amma tunda kin amince,nima ina murna da wannan aure,domin ameera
tayi dacen miji' ,bilal yayi gdy ya tashi ya fice,ita ma meera tayi
godiya ta wuce d'akin meera,tana shiga ta tarar da meera tana danne
dannen waya,hibbatu tayi tsalle ta dire akan gadon tana cewa 'ameera
kina kwance a d'aki ba kisan 'kosan da ake toyawa a gidan nan ba,burin
mu ya cika,(nan ta kwashe yadda sukayi da alhaji ta labartawa
meera),meera wani sanyin dad'i ne ya kwarara a zuciyarta ,amma a fuska
sai ta ta6e baki ba tare da tace uffan ba,sai ma juyawa da tayi tana
danna wayarta,hibbatu ta gama soki burutsunta ta tashi tana cewa bara
naje in fara had'a kayanmu'...ta tashi ta fice,tana fita meera ta tashi
ta d'aga hannayenta sama tana cewa 'ALHAMDULILLAHI',sannan ta nufi
toilet,ta cire sim d'in wayarta ta karyashi ta kora a masai tana cewa
'imad ba ni ba kai har abada , zuciyata ta zama mallakin bilal!....' * *
* Washegari ko da bilal yaje gida,a shirye ya tadda hibbatu ta gama
had'a kayansu(tufafinsu data sayo masu ,sai kuma takardunsu) ta saka a
motarta,jiranshi kawai takeyi,yana shigo ta tashi ta rungumeshi ta manna
mai sumba tana cewa 'mijina gatana,kaga yadda Allah yayi damu ko,ta
silar bada HAYARKA ,gashi munyi bankwana da talauci,mun tako arziki mai
lasisi da garanti',bilal yayi murmushi yace 'amma kina ganin ya dace mu
sakawa alhaji alkhairinsa gare mu da sakin 'yarsa a duk lokacin da
kaninki ya bukaci hakan' ,'eh mana bilal,i ba zawarci xatayi ba in an
saketa,aurenta fa imad d'in zai yi,kaga mu bar maganar nan,taho mu tafi
kawai in munje can gidan kayi wankan',bilal yace 'toh sauran kayan
fah?',hibbatu tace 'in masu gyaran gidan sunzo sa san yacca xasuyi
dasu,domin ni dai akwai kud'in da zan sai mana kayan furnitures da
sauransu idan mun dawo,kuma nasan itama ameera za'a yi mata kayan daki
,kila muma suyi mana','uwar son banza kenan' bilal ya fad'a a zuci,suka
fice daga gidan,motarta suka shiga,hibbatu ta bata wuta sai gidan
alhaji,bayan sunyi parking a kofar gate,sai bilal yace 'da kud'in HAYAR
kika sayi motar nan ?' ,'eh mana' ,'toh in mun shiga me zamu ce game da
motar nan in an tambaye mu','ka kyaleni dasu,ni nasan me zance masu,fita
ka bud'emin gate in shiga' 'toh' bilal yace mata tare da fita ya je
wangale mata gate ta harba kan motarta ciki...... Hakkin
mallaka:abdulaziz ililee Hakkin mallaka:abdulaziz ililee