Dariya meera tayi tana zuba abinci a kula tana cewa'sis hibba,ki rage
kwaɗayi da ƙarya pls .daga shigowarmu kinyi ƙaryar ciwon kai.kuma gashi
yanzu kina kwaɗayin juice' ."ameera kenan .shekara 6 cikin talauci ba
wasa bane.ki daina alaƙanta halayyata a yanzu da kuma labarina dana
baki.hakan zai sa.ki daina ganin gazawata wajen danne kwaɗayina',meera
ta miƙa mata kular abinci ta ɗauko mata carton ɗaya na jus daga cikin
store.tana cewa "ALLAH ya kyauta" "amin",hibbatu ta ɗora katon ɗin jus
akanta,ta rungumi kular abinci.tana zuba godiya ,meera ta raka hibbatu
bakin gate!
* * *
misalin ƙarfe 10 na dare.meera tana kwance ,ta kasa bacci ,tunanin lbrn
hibba da bilal ya addabin hoton bangon zuciyarta ,musamman bilal da
tayiwa laƙabi da jarumin maza,wayarta ta fara ruri,ko bata duba ba tasan
imad ne,domin special ringtone na musamman tasa masa,ɗauka tayi tare da
karawa akan kunnenta tayi sallama,a ɗaya ɓangaren aka amsa cikin muryar
kuka .hakan yasa meera ta zabura ta tashi zaune tana faɗin "imad lafiya
kake kuka".dole in yi kuka meera,abbu yana son tarwatsa min
zuciya,meera ina sonki i cnt afford 2 loose u,dole mu nemi mafita wajen
ganin burin mu ya cika ' ,kyaɓe baki tayi tace "mafita itace kawai mu
haƙura da juna mu yiwa iyayen mu biyayya,ni abbana bai da matsala,domin
ko a yau ka shirya aurena ,zan baka ni,amma abbunka ne yace u r still
young,ni kuma abbana ba zai zubamin ido yana kallona, ba tare da nayi
aure ba,zancen dana ke maka a yanzu ya bani 1month in fitar miji ko kuma
shi ya fitar min da miji",'meera kina nufin zaki yarda ki auri wani
bani ba' "ya kake son inyi,in har kaddara ta so hakan' ,"dole in nema
mana mafita meera","toh imad ,amma duk mafitar da zaka nema mana ,ka
tabbatar da cewa mafitar ba zai zamto ɓacin rai ga iyayen mu ba"',a haka
suka gama wayar .ko wannensu da nashi kalar tunanin......
Hakkin mallaka:
meera ta cigaba da hira da zuciyarta tana cewa 'ya zama dole in yakice
imad daga cikin zuciyata,haba sai kace na rasa masoya,ko kuma wacce aka
ce jeki kya gani,ayi tayin abu ɗaya ,in banda abba yana da saukin kai
,wani uba ne zai dinga bin amininsa da zancen d'ansa ya auri ƴarsa,sai
kace wanda ya ke neman kai dani,ya zama dole in ha'kura da kai imad ,ko
da kaine autan maza,abba ya bamu dama ,amma abbunka yayi watsi da
daman,bisa wani ra'ayi nashi mara tushe' ,a haka har bacci yayi awon
gaba da ita...
***
washegari misalin 'karfe goma na safe,meera ta fito daga wanka ,wayarta
ta fara ruri ,ko bata duba ba tasan imad ne,,hakan yasa ta d'anyi tsaki
,domin daga jiya zuwa yau ,lamarin abbu ya gama sire mata ,musamman idan
ta tuna da lbrin hibbatu,haka ta mi'ka hannu ta d'au wayar tare da
amsawa ,ta kara akan kunnenta,imad bai jira tayi magana ba ya fara cewa
'meera na samo mana mafita wacce da ni da ke zamu cika burin mu ,ba tare
da mun 'batawa iyayenmu rai ba',''imad kenan ,ina sauraranka,meye
mafitar' ,sai da imad yayi jim sannan yacigaba da cewa ' meera!!,mafita
guda d'aya ce tak,tabbatar aure tsakaninki da MIJIN HAYA!' 'MIJIN HAYA?'
,meera ta maimaita tare da cewa 'imad ka fitar dani duhu, bangane
abinda kake nufi da kalmar MIJIN HAYA ba....
Hakkin mallaka: Imad yace'abinda nake nufi da MIJIN
HAYA shine zan turo maki miliyan takwas ,ki samu namiji
,talaka,matsiyaci kiyi HAYARSA da wannan kud'in,ki kawo wa abba shi a
matsayin Mijin da zaki aura,da wannan kudin zai kama maki gidan da zaki
zauna,yayi lefe ya biya sadaki,ya ciyar dake har na tsawon lokacin da
zan kamalla karatuna ,in dawo ya sakeki,kiyi idda muyi auranmu,batare da
wani abu ya shiga tsakaninku ba,kinga hakan kad'ai zai zamar mana
mafita wajen mallakar junan mu a matsayin miji da mata,batare da mun
6atawa iyayenmu rai ba' ,tsaki meera taja tare da cewa 'amma ka cika
d'an rainin wayo,haba sai kace a fim ,ko kuma labarai,wai MiIJIN HAYA'
bata jira yayi magana ta katse wayar tare da jan wani dogon tsaki,tana
mai ganin sakarci da wautar imad...zuciyarta a 'kuntacce ta shirya cikin
doguwar riga,tana jan tsaki akai akai ,ta nufi bakin tagar dakin, ta
tsaya tana tunanin batun imad a zuciyarta ,tare da kudurtawa ranta cewa
'ko da imad ne autan maza ,toh wlh tlh ta hakura dashi' ,tasa hannu ta
d'aga labulen tagar,idanuwanta suka hango mata bilal yana zaune kan
benci,ta 'kura masa ido tana mai yabon kyawun fuskarsa da
surarsa,natsuwarsa da sanyinsa,domin yau ta ta6a tsayawa ta kare masa
kallo daga sama har 'kasa,a take zuciyarta ta buga ,tana mai jin wani
abu na bijiro mata,yana yawo daga kanta zuwa tafin kafarta,wani irin
feelings take ji game da bilal,ba tare da tashirya faruwan hakan ba,ko
imad bata ta6a jin irin wannan abu a game dashi ba,a take ta lumshe
idanu tana cewa 'zan so ka zama MIJINA bilal' ,ita kanta bata san ta
furta hakan ba.... meera ta ri'ke bakinta tare da
tambayar kanta 'me yake shirin faruwane ,kar dai zuciyata ce ta kamu da
son bilal?, 'this can't be,it's impossible ' ta bawa kanta amsa!
Sallamar hibbatu ne ya katse mata tunaninta ,juyowa tayi tare da amsa
sallamar ,ta bar jikin tagar ta karaso ga hibbatu ,''ina kwana sista,kin
shigo ashe?'',hibbatu bakinta cunkushe da batter yam tace 'tun dazu
naxo ,na shigo nan,amma kina wanka a lkcn,shine ynzu na taho maki da
abin kari ,sa hannu muci,yyi dadi wlh,doya ce hjy ta sarrafata',ta nemi
bakin gado ta zauna,doya d'aya meera ta d'auka ta kai baki bayan ta
zauna ,tana cewa 'woh sista ,chop chop ' ,'ehe thats reminds me ,kunyi
waya da imad kuwa? ','eh munyi waya d'azunnan ma muka gama waya da shi'
,meera taja gajeran tsaki ta labartawa hibbatu yadda sukayi da imad
,sororo hibbatu ta bita da kallo ,bakinta cike da doya tace 'MIJIN HAYA
kuma ,sai kace wata haja ko kadara ,wani namiji ne zai yarda ya aureki
ya zauna dake batare da wani abu yashiga tsakaninku ba,kuma kawai ya
sake ki a duk lokacin da aka bukaci hakan?','ke ma ki tayani ji dan
Allah,akwai d'aure kai da wauta a lamarinnan,ni fa kawai na hakura da
imad''.... Hakkin Mallaka:ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL