dariya hibbatu tyi,tace 'ameera ku zan tmby,masoyan zamani,kinga in
takaice miki,haka na cigaba da lallashinsa,har ya samu ya kwantar da
hankalinsa,washegari yaje gdanmu ba tare da ya gayamin ba,abbu ya 'kare
masa cin mutunci da wulakanci wanda hakan ya jawo ya kudiri aniyar bawa
mara d'a kunya ,wayarsa ya siyar ,ya kuma had'a da saurin kudin allowee
d'insa yayi mini lefen akwati d'aya cike da atamfofi kala 5,takalmi daya
,jaka guda d'aya,sai undies da sauran irin sabulai da takarce,fad'a
nayi masa sosai da ya kawo kayan,sai da kaka tasa baki na hakura na amsa
,bayan sati biyu da dawowarsa muka je b.u.k ya kar6o result dinsa
,lecturers sai mamaki suke ganin yadda na koma,ni dashi muka bazama
neman aiki,kullum tun safe muke fita ,sai yamma zamu dawo gda,amma ba'a
dace ba,ko kuma ace mu dawo gobe,in mun koma sai a bamu hakuri a maido
mana da cv d'inmu,yan kudaden bilal suka fara 'karewa ,domin kud'in mota
ya soma gagara,hakan yasa bilal ya fito da kekensa aka sawa taya
iska,haka yake goyani muje neman aiki,amma duk bbu sa'a ,har ta kai
teaching mun nema ,amma ba'a bamu ba,duniya tayi min baki kirin daman da
takarduna na dogara ,domin nasan da zarar mun samu aiki,komai xai dawo
nrml,amma ina sai ma ta6ar6arewa,kaka abin na damunta matu'ka,tana
tausaya mana,hakan yasa ta kamu da hawan jini,kud'in siyamata magani ya
gagara,d'an kunnen daham d'in da ke kunnena, dana tsira dashi aranar da
abbu ya koreni,shi na d'auko ,mu kaje kasuwa ni da bilal muka siyar,muka
siyawa kaka magani da kuma kayan abinci,satin kaka biyar tana jinya ta
rasu,munji mutuwarta ,amma munsan cewa mutuwar ita ce gata a gareta ,a
haka rayuwa ta cigaba da tafiya komai na gidan yana 'kara lalacewa,neman
aiki bamu hakura da nema ba,duk inda mukaji ana nema sai munje,hatta
aikin lebura mun nema,mun samu amma muna komawa washegari suka ce sun
fasa d'aukar mu,a cikin wannan rayuwa muka shafe shekara hud'u
,makotanmu duk sun tashi daga gidanjensu sunyi arziki,kayan d'aki da
kichin d'insu ,suka kawomin kyauta,domin zaman lfy mukayi dasu ,hakan
yasa kikaga gdan da kayan daki,duk da wasu ma saidasu nayi,naso nayi
aikin aikatau amma bilal ya hanani,shi yake fita dako da kwasar kwata ,a
biyashi muci abinci da kud'in',hibbatu ta dubi meera tace 'ameera
talauci bai yi ba,sunansa bai yi ba,domin talaucine ya maidani
'kazama,bagidajiya,kwadayayyiya,masifaffiyarkarfi da yaji ,domin yau da
gobe ,bata bar komai ba,kuma har yau banyi 6atan wata ba,dukanmu bamu
damu ba ,domin talaucin da muke fama da shi ya ishemu,bilal ya cigaba da
kujiba kujiban neman aiki,domin ni na hakura,kekensa ma siyarwa yayi
muka siyi kayan amfani irinsu sabulu,man goge baki,da kayan abinci,yanxu
haka shekarar mu shida da yin aure ,sati biyu da suka wuce ya had'u da
alhajinku a masallaci wai yana neman maigadi,bilal baiyi 'kasa a gwiwa
ba ,yaje gdanku ya kai kanshi,alhajin ya daukeshi,munyi murna sosai
domin gani muke karshen talaucin mu ne yazo,hakan yasa kwana uku da suka
wuce da nayi mafarkin tsiren hanta,sai na farka na tafi gidanku wajen
bilal da zummar amso dari biyu...(ku duba chapter 1)' ,baya n hibbatu ta
gama bawa meera lbri, meera ta sauke ajiyar zuciya tace 'tabbas hibbatu
kunga rayuwa ,kuma rayuwa ta ganku',kiran sallar azahar da sukaji ne
,ya katse masu hirar ,hakan yasa suka tashi ,hibbatu ta zuba masu ruwa a
buta domin yin alwala suyi sallah. Bayan sun idar da sallah,hibbatu ta fita ta yo
cefane da kudin da hajiya ta bata,ita da meera suka had'u suka bararraka
jolop din taliya,bayan sunci sunyi nak ,hibbatu ta dubi meera tace'ni
ko in tmbyeki mana' ,'ina jinki' ,'tayaya kuka hadu da imad har kuka
fara soyayya,duk da nasan cewa a 'kasa d'aya kukayi karatu' ,meera ta
gyara zama tace 'toh da farko dai sunana ameera salis goni ,ni ce y'a
daya tilo ga abba da umma ,wato alhaji salis goni da haj.nafisa,na
kasance yar gata ,shalele ga umma da abba,amma hakan bai hana su tsaya
tsayin daka wajen ganin nasamu ingantaccen tarbiya ba,domin abba mutum
ne wanda dimbin dukiyarsa bata rufe masa ido ba,kasancewa shine
mamallakin [goni motors ]kuma bai dau duniya da zafi ba ,haka zalika
umma ,tun gama secondary d'ina ,abba yaso ya aurar dani,amma dayake na
nace sai nayi degree ,da kyar ya amince nayi ,na nuna sha'awar yin
karatu a kasar waje ,amma sam yace bai amince ba,sai da umma ta sa baki
,sannan ya amince ,bayan nayi masa alkawarin zan kare mutuncina ,na fara
karatuna tiryan tiryan a bangaren masscomm ,ina da shekara biyu a
univrsty of cyprus,wata rana na kamu da matsanancin rashin lfy,a lokacin
su imad sunzo medical excursion daga skul dinsu xuwa tamu makarantar
,danaje skul clinic,sai akace one of the student doctors 4rm medical
university ne zai dubani,imad ya zamto student doctor d'in ,domin bani
gado akayi ,shi ya kula dani,ya bani magani da allurai ,a lokacin dana
warke ,sai na fara yabawa da kirkinsa gareni ,domin bayan an sallameni
,ya karbi numbrta,muna waya ,muna chtn ,a haka muka shaku sosai ,har ya
zamto ya furta min kalmar so,kasancewar shi ne d'a namijin da ya ta6a
furtamin kalmar so a rayuwat,hakan yasa na amince masa ,domin banga aibu
a tattare dashi ba,a lokacin da abba ya zo dubani ,na gabatar masa da
imad a matsayin mijin da xan aura ,abba ya nemi da yaji asalinsa ,bayan
imad ya gaya masa ,anan ne abba ya gano cewa imad d'an amininsa shoaib
ne da sukayi secondary tare a 'kasar oman,hakan yasa abba ya kar6i numbr
din abbu gun imad,suke sada xumunci ta waya, suka shirya had'uwa a
kano,nan abbana yayi wa abbu xancen aurena da imad ,yana son ayi aurenmu
in yaso sai a siya mana gda a cyprus d'in muyi xaman mu har mu kamalla
karatu,amma abbu ya nuna rashin amincewarsa,wai imad is too young 4
marriage ,abba ya nemeni a waya ya gaya mini ydda sukayi da abbu ,ni
kuma nace badamuwa,nima kawai bara in kamalla karatuna ,inaga xuwa
lokacin abbu xai hakura ayi auren ,a wani hutune dana xo gda nigeria
,mukaje gidanku tare da abba da umma,a lokacin naga hotonki a album kina
yarinya ,dana tmby wacece ke ,sai ammi tace min ke yayar imad ce ,amma
abbu ne yace kin dade da rasuwa,bamu kara tada xancen ba,ni da imad muka
cigaba da soyayyarmu ,har naxo na kamalla karatuna na baroshi a can
yana housemanship a city hospital na kasar cyprus,na dawo nigeria,kuma
abba ya tare ni da zancen aure ,kinji yadda muka kaya da shi a dinning
ko? ,hibbatu tace'eh naji kam har ya baki 2weeks kifitar da miji', meera
ta cigaba da cewa 'toh zuwansu abbune,abbu ya kara jaddadawa abba cewa
imad baxai aure ba sai ya kamalla ph.d,idan xan jira in jira ,abba kuma
yace aurar dani zai yi bai xai xuba min ido in tsofe masa a gda ba,ya
nzu dai abba ya bani 1mnth in fito da MIJI.. Hibbatu ta sauke
ajiyar zuciya tace 'ALLAH sarki imad rabona da shi tun lokacin da muka
rakashi cyprus daya samu admssn,toh ku yanzu wani mataki kuka d'auka?,ko
kuma zaku hakura da junanku ne',meera tace 'toh tun jiya ina trying
wayarsa a kashe,nayi masa txt ,not deliverd,kawai hakura xanyi dashi in
nemi wani in aura ,domin gsky abba ya bani chance da dama,baxan so in
watsa masa kasa a ido ba' ,'hakane kam kinyi gsky ,amma duk da haka ki
tuntu6i imad ki ji daga gareshi,'kila ya nema maku mafita' ,'a yadda
naji lbrn abbu daga gunki,alamu sun nuna cewa shi mutum ne tsauri da
kafiya,kina ganin akwai dabarar da zata sanya abbu ya sauya ra'ayinshi',
hibbatu ta ta6e baki tace 'amma kar ki manta fa gadonsa mukayi ,nasan
in har imad na sonki dole ne ya nema maku mafita wajen ganin kun mallaki
junanku a matsayin miji da mata' ,ameera ta mike tsaye ta yafa mayafin
abayarta ,sannan ta d'au wayarta tana cewa 'ni dai na barwa Allah
komai,domin matar mutum kabarinsa,kuma ko da zan amince da mafitar da
imad zai nema mana,toh baxan amincewa mafitar da zai zamto bacin rai ga
umma da abba ba,ni zan tafi,muje ki rakani,yau munsha hira,tun safe nazo
gdannan' ,hibbatu ta mi'ke tsaye ,ta d'au hijabin sallarta tasa,ta d'au
basket d'in da meera ta kawo mata abinci a ciki tace'toh muje in rakaki
gida,daganan in gaishe da hajiya'..haka suka fice daga gidan,hibba ta
kullo gidan, da kafa suka karasa gidansu meera da yake ba nisa
daman,suna hira abunsu,har suka iso ,bilal ya bud'e masu gate suka shiga
,hibbatu tace masa sannu da duty,meera ta d'an russuna ta gaidashi ,ya
amsa yana mai sosa keya,ita kuma meera tausayinshi ne ya kamata tunda
taji lbrnsa a gun hibbatu,hakan yasa take ganin 'kimarsa domin da wani
ne wllh guduwa zai yi (tunda wanda yake da ita a duniya ta rasu wato
kaka,gani zai yi auren hibbatu a gareshi yazo masa da tsiya),haka suka
shige cikin gida,suka tadda umma a falo ,ta amsa gaisuwarsu fuskarta
dauke da fara'a tana cewa'ameera kin je kinyi biko ko?',hibbatu ta washe
baki tace'daman yau na tashi da ciwon kai ne,abin da yasa banzo ba
kenan ',sannan taja hannun meera suka shige kitchen ,bayan ta ajje
basket d'in,ta dubi meera ,muryar 'kasa kasa tace 'ina son ki min
alfarma pls,labarina dana baki ayau,ina son ya zama sirri tsakanina da
ke,kar ki gayawa kowa pls' ,'toh shikenan,labarinki is safe wit me,dnt
wrry', 'nagode ameera,ni zan tafi,sai gobe','ki tsaya in d'ibar miki
abinci,in yaso kinci anjima da dare','toh ameera,i bazan 'ki ba,zubo in
tafi da shi,kuma ki d'an had'a mini da juice pls',... Hakkin
Mallaka:ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL