Ammi ta dubeni tana mai girgiza kai tace'hibba ba dani zakiyi wannan
ya'kin ba ,da abbunki zakiyi ',wucewa nayi na bar ammi a gun na nufi
palon abbu ,ganin affan da iyayensa a palon yasa na russuna na gaishesu
fuskata bbu yabo bbu fallasa,sannan na wuce d'akin abbu,nayi sallama ya
amsa min tare da bani izinin shigowa ,idanuna jajir na dubeshi cikin
harshen larabci nace 'abbu kai ka gayyato affan da iyayensa ',dubana
yayi sosai sannan yace'eh ni na gayyatosu,kasancewar mahaifinsa amini
na,kuma kema kinsan da haka ,kinga kenan ba ba'ki bane su ',muryata na
rawa nace'bisa wacce manufa sukazo?','manufar da baza su bar gidannan ba
sai da ke a matsayin matar affan','abbu amma kasan nafad'a maka bana
son shi' ,'toh hibbah wa kike so', 'bilal' na furta a sanyaye,cike da
6acinrai abbu yace'idan kika kara furta wannan sunan a gidannan sai na
tsine miki,zan iya aurar da ke ga kowa ,amma bazan iya ta6a aurar da ke
ga wannan yaron ba',idanuna na zubda hawaye nace'abbu dalili? saboda
bashi da arziki da dangin uba...' ,abbu ne ya katseni yace 'saboda
ubanki,tashi ki 6ace min daga nan ,kafin in mangare ki,mara kunya
kawai',jikina har rawa yake na tashi na fita ,idanuna na zubda
hawaye',hibbatu ta dubi meera a sanyaye tace'har yau na rasa dalilin da
yasa abbu bayason aurena da bilal',meera cike da tausayawa tace 'toh ke
kin ta6a tambayar shi bilal d'in ko wani abu ya ta6a had'ashi da abbu'
,hibbatu tace'na tambayeshi ,amsa d'aya ce kawai ,wai wlh bai san abbu
ba sai a ranar da na gayyatoshi gdanmu' ,meera ta sauke ajiyar zuciya
tace 'ni ko zuciyata tana hasashen wani abu game ga kiyayyar abbu ga
aurenki da bilal ,amma kawai cigaba da bani labari,ya kuka 'kare da
affan da iyayensa?'.... Hakkin mallaka:ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL. MIJIN
HAYA [24] na ILILEE Affan d'in nasamu na ja masa kunne da yayi gaggawar
janye batun aurena in ba haka zai fuskanci masifa,bala'i,kata'i da
rashin mutunci daga gareni,sai ya gwammace mutuwarsa da aurena,domin
babu tarayya tsakanin 'kiyayya da soyayya,da kanshi yaje wajen abbu yace
ya fasa aurena domin bazai auri matar da bata sonshi ba,ran abbu ya
6aci sosai ,domin kad'an ya rage ya tsine mini,haka affan da iyayensa
suka tattara suka bar mana gida,abbu kuma yace ingayawa bilal ya turo
magabatansa,waya na bugawa bilal na sanar dashi ,bilal kuwa kawunshi ya
bugawa waya wato yayan ummansa,ya rokeshi da yanason dan Allah suje su
nema masa aurena,kawun ya amince da kyar sannan yace zai gayawa sauran
yan uwa sai aje,adireshin gdanmu ya tura masu ,ni kuwa da bilal ya sanar
dani ydda sukayi da kawu, satar jiki nayi naje gdansu bilal gun
kaka,bayan na gabatar da kaina a gareta ,sannan na dauki dubu hamsin na
bata nace ta bawa su kawu yadda zasuji dadin zuwa neman auren nawa,bayan
kwana biyu bilal ya bugomin waya wai gobe su kawu za suzo ,na sanar da
ammi zuwansu ,ita kuma ta sanar da abbu,washegari bayan sallar la'asar
abbu ya dawo gda dashi da limamin masallacin gdanmu,karfe 5 ,kawunnan
bilal guda hud'u sukazo ,palon ba'ki abbu yace akaisu ,bayan sun zauna
,abbu da liman suka shigo suka zauna ,basu kai ga gaisawa ba balle su
fad'i abin da ya kawosu,a wulakance abbu ya dubesu yace'dafatan kun taho
da sadaki,domin ba doguwar magana nakeso ba',inda Allah ya taimakesu
cikin dubu50 dana bawa kaka ta basu ,sunci dubu20 sauran 30,haka suka
had'o dubu30 suka bayar ,abbu ya bawa liman umarnin da ya kar'bi kudin
ya d'aura auren,liman ya karba sannan aka shafa fatiha,sukansu kawunnan
bilal sunyi mamaki ,domin tambayar aure kawai sukazo yi,abbu ne ya
dubesu yace'ina zuwa ku jirani',cikin gida yashigo ,muna zaune ni da
ammi a falonta,abbu ya shigo fuskarsa ba walwala ya dubeni yace 'ke
tashi ki d'auko min key d'in motarki,atm card,creditcrds,check,passports
da wayoyinki da duk wani gadgets dana siya miki',jiki a sanyaye na je
na tattaro masa na kawo masa ,harara ya zabga min yace'tunda kin nace
sai kin auri wannan yaron ,toh bismillah an daura aurenku,sai ki tashi
ki bar min gida ki tafi gdan mijinki',ammi hannu akan kirji tace'aure?
Gidan miji? ,abbun hibba ban gane ba',abbu ya dubi ammi yace 'tabbas
aure wanda kika sani ,na daura mata aure da wanda ta ke so,yanzu sai ta
tashi ta fitar mini daga gida',sannan ya juyo ya dubeni yace 'daga yau
bamu ba ke hibba,ki manta da cewan kina da iyaye a doron 'kasa ,daga yau
ke matacciya ce agaremu ,haka zalika mu matattu ne a gareki,u hv no
blood ties with us' ,ammi ce ta katseshi muryarta na rawa tace 'abbun
hibba kasan me kake cewa kuwa' ,tsawa ya daka mata yace 'look woman! Kar
ki kara alakantani da wannan yarinyar mai kafiyar tsiya,ni imad kad'ai
na haifa',ni kuwa jikina rawa kawai yake,na rasa me zanyi farinciki ko
ba'kinciki,tsawa abbu ya daka mini yace 'me kike jira don ubanki tashi
ki fice ',ammi ce ta dakatar dashi tace 'haba abbun imad ,in ma
kafiyarce ,gado tayi,ku koma menene i kabari ta had'a kayanta ko ,anjima
in kira yan uwa a rakata d'akinta','wllh tllh ynzu zata bar min
gida,kuma kada ta kuskura ta dauki ko tsinke daga gidannan,kuma kar ki
kuskura inji wai kin bata kudina,kai ko gdanta kikaje,a bakin aurenki'
,ammi kuka ne ya subce mata da gudu ta fice daga palon ,ta dawo hannunta
ri'ke da credentials d'ina da hijab,ta mika mini tana cewa 'ungo
hibbatullah ,iliminki yanzu shine gatanki,ki tashi ki tafi,kar ya
wula'kantanki' ,kasa mi'kewa nayi domin ban ta6a zaton hakan daga gun
abbu ba ,fincikar hannuna yayi,ya mi'kar dani tsaye, ya fice dani ,bai
tsaya a ko ina ba sai a palon ba'ki ya jefa masu ni ,yana cewa 'gatanan
ku tafar masa da ita',sannan ya amshi sadaki daga hannun liman ya
jefamin yace'ga sadakinki nan,sai ku fice mini daga gida,bamu ba ke har
abada.... Hakkin mallaka:ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL. MIJIN HAYA {25} na
ILILEE Hannu nasa na d'au sadakina tare da sanya hijab d'in da ammi ta
bani,na dubi abbu nace 'abbu dan Allah kar ka...',d'aga min hannu yayi
tare da daka min tsawa yace 'bana son jin kalamanki ,ki tafi kawai' ya
dubi su kawu yace'me kuke jira ,gata nan ku tafar masa da ita',d'aya dga
cikinsu zai budi baki yayi magana ,abbu ya katseshi yace'kindly get the
hell out of my house',da sauri suka fice domin sunga lamarin abbu babu
wasa ,haka na bisu a baya ina mai jan 'kafa,muna fita suka tare d'an
sahu guda 2,su uku suga shiga d'aya,d'ayan kuma muka shiga guda d'aya
dashi ,ba'a tsaya a ko ina ba sai 'kofar gidannan,bayan mun sauka naga
sun fara kame kame,cikin kud'in sadakina na ciri dubu na mi'kawa masu
adaidaitan,sannan na juya muka shiga gidan,kaka ta fito daga daki da
taji ana sallama,ta amsa sallamar tare da tmbyr lafiya na ganku
haka',nan suka kwashe lbrin yadda akayi a gdanmu suka gaya mata,kama
baki tayi tana salati,basu jira mai za tace ba,suka kad'a rigarsu suka
fice daga gidan suna masu farin cikin faruwar wannan lamarin,bayan na
basu dubu 2,kuma na ro'ki alfarmar dan Allah kar su gayawa bilal ko da
sunyi waya,kaka ta 'karaso gareni ta d'agani daga tsugunon dana yi tana
cewa 'anya 'yar nan ayi haka kuwa,ki za6i namiji akan iyayenki,ki baro
daular gdanku ,ki taho ga taulacin gdannan,ina mai baki shawara da ki
chanja tunanin ki koma gdanku ki ce kin fasa auren bilal' ,sai a lokacin
hawaye ya zubo mini ,na d'inga kuka ,kuma na rasa kukan meye,duban kaka
nayi nace 'zamana da bilal mutu ka raba,domin banga dalilin da zaisa
abbu ya hanani aurensa ba,bazan ta6a danasanin auren bilal da izinin
Allah,kuma arziki da talauci duk na Allah ne,kaka kar ki damu kanki ,mu
cigaba da addu'a Allah zai shige mana',hibbatu ta dubi meera a sanyaye
tace 'haka na shafe wata 9 a gidannan,bana fita ko ina,ina gda ,tufafi
kuwa sai yar makociyar na bawa kudin sadakina taje kasuwa ta kwaso mini
kayan gwanjo,vaseline,omo,sabulu,man goge baki da sauran takarce irinsu
katifa mai arha,dad'inta ma akwai kayan abinci a gidan,kuma duk wata
bilal yana yiwa kaka aike da kud'in allowee dinsa ,haka dai na cigaba da
rayuwata a gidan, da dad'i ba dad'i,kaka kuwa a kullum tausayina
take,ni kuwa dagewa nayi na rufe babin iyayena a zuciyata, jiran dawowar
bilal nake in nemi izininsa in fita neman aiki da takarduna ,a wani
yammaci ne ina zaune gaban coalpot ina hura charcoal,kaka kuma tana
tsintar shinkafa ,kawai sai mukaji sallama,bilal ne ya shigo sanye da
tufafin n.y.s.c,turus yayi da ya ganni ,ya bini da kallon mamaki,tashi
nayi ina goge hannuna a jikin zanina ina cewa'oyoyo mai gidana',na sa
hannu na kar6i jakar dake hannunsa,sororo ya tsaya kallona,tabarma na
shimfad'a masa ,naja hannunsa na zaunar dashi,na d'ebo masa ruwa a randa
na kawo masa',da kyar ya budi baki yace 'malama yana ganki haka ,me ya
kawo ki gidannan,me kuma ya samu wayarki ,na kira switch off',kaka ce ta
fashe da kuka ta tashi ta shige d'aki ,hakan ya bani daman ce masa
'bilal Allah ya cika mana burinmu,mun zama miji da mata' ,'tayaya?' ya
tmbyni ,'ta dalilin aure mana' na bashi amsa,tashi yayi jikinsa na rawa
ya shiga d'akin kaka ,kaka ce ta dubeshi ta zayyane masa yadda aka daura
aure na dashi ,fitowa yayi daga d'akin yana mai zubda hawaye ya
rungumeni yana cewa 'me yasa kike sona da yawa ,anya hibba kin yi wa
kanki adalci kin tsallake iyayenki da jin dadin gidanku saboda ni,me
kika gani a tattare dani da har kika kasa hakura dani? Hibba why? Why do
u love me so much?',bubbuga bayansa nayi nace 'ka daina kuka bilal
,soyayyar da nake maka ta fi karfin in wofintar da ita bisa dalili mara
tushe,bilal ina tare dakai duk runtsi duk wuya ,bazan ta6a guje maka
ba,ina son ka ri'ke amanata ,kar kasa inyi danasani a rayuwa' ,kankameni
yayi yace 'ina sonki matata,zan jajirce wajen ganin na faranta miki
,domin kin yi min halaccin so',meera ta sauke ajiyar zuciya,tare da goge
hawaye da ya zubo mata tace 'tirkashi! Do such love still exist?....
Makaranta sai ku bata amsa ,mu hadu a 26, commentbox d'in pic d'in
bilal.. Hakkin mallaka:ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL