Hibbatu ta dubi meera tace 'toh ,sauke numfashi nayi ,idanuna taf da
hawaye na dubi bilal nace'a gsky malam bilal kaga rayuwa ,na tausaya
maka,kuma na jinjinawa kakarka,ni kuma sunana hibba shoaib' ,haka dai na
bashi tarihin rayuwata,dana gama bashi ,sai ya dubeni yace 'kina nufin
ke balarabiyar kasar oman ce' ,'kwarai kuwa but born by a hausa
mother',murmushi yayi yace'no wonder malama kike da kyau',hakan yayi
daidai da shigowar abbu ,russunawa bilal yayi ya gaidashi ,da fara'a
abbu ya amsa ,sannan ya dubeni yace'in kin gama ,kizo ina neman
ki',bayan abbu ya shige sannan na dubi bilal nace 'malam bilal
tsakaninka da Allah,ka dubi girman Allah kar ka 6oyemini,ka dubeni,ka
manta da matsayina,ka manta da cewa tsakanina da kai akwai banbancin
rayuwa,kar ka 6oye mini sirrin zuciyarka,bilal zaka iya aurena,zaka iya
rayuwa dani a matsayin matarka,zaka iya tarayya dani wajen had'a
dangantaka dani,wato dangantakar zuci,bilal na kamu da sonka a ranar
dana fara dora idanuna akan idanunka ,sanin cewa bazaka ta6a tunkarata
da zancen so ba ,yasa ni na bayyana maka sirrin dake raina ,bilal kana
sona?',bilal dimuwa da gigita ne suka masa dirar mikiya ,hakan yasa ya
dukar da kansa,yana mai murza yatsunsa,domin he nvr expect such words
4rm me,kasa dago kansa yayi,dubansa nayi tare da goge hawayen da ya zubo
min domin ni kadai nasan yadda xuciyata ta harbu da son bilal ba tare
da na shirya ba,nace 'bilal dare nayi ,zaka iya tashi ka tafi,ka bar
kaka ita kadai a gida,sai da safe' ,sannan na tashi jiki a salube....
>Tunda ita hibba bata ja aji ba,inaga bilal sai yaja,ko ya kuka ce? jin ya ambaci
sunana,yasa na tsaya chak! Tare da juyawa,dubana yayi yace'hibbah ko da
ban san ke wacece ba,nasan cewa ni ,kin fi karfina,ke yar gata ce,yar
asali,yar sarauta,yar dangi kuma yar boko,tayaya tarayyar so zatayi
tasiri a tsakaninmu ,rayuwa ta da taki akwai banbanci',idanu jajir na
dubeshi nace 'bilal ka daina tunanin haka ,domin arziki da talauci ba
zai zamto mizanin da zan auna soyayyarka a xuciyata ba,malam bilal
soyayyarka da amincewarka shine cikar buri na' ,bilal ya rintse idanu
yace 'na aminci' ,murmushi nayi tare da yin taku izuwa gareshi nace
'bilal dago ka dubeni ,ina son ka dubi tsakiyar idanuna ka fad'a min
gaskiyar xuciyarka',ya dago ya dubeni yace 'ina son ki,ina kaunar
ki,zuciyata ta aminta da ke, kuma bazan daina son ki ba hibba,kin min
halacci hibba,halaccin da har abada bazan manta dashi ba,ki yarda
dani',farin ciki ne yasa ,na juya da sauri na fice daga palon,na isa
kofar palon abbu ina sauke numfashi,fitowar ammi ne yasa na d'aga ido na
dubeta,cewa tayi 'yawwa daman ke zan je in kira ,wacce irin hira ce
haka ,baki san dare yayi ba,kuma wanene shi',murmushi nayi nace'ammi
mushiga palo sai muyi maganar gaba d'aya',muka shige palon bayan na
zauna ,na labarta masu lbrn bilal kamar yadda ya bani lbri',tun kafin in
kawo karshe abbu ya katseni yana mai yatsina fuska ,a kausashe yace
'toh menene had'inki dashi,me ya kawoshi gidannan',kaina a duke
nace'abbu aurena yake son yi' ,a kasaushe ya jefomin tmbyr'aure? wani
iri?',a sanyaye nace'aure dai irin wanda addinin musulunci ya halasta',
tsaki ya ja tare da cewa'daga yau ba ke ba zuwa makarantar nan da sunan
lecturing,ki rasa da wa zakiyi soyayya sai da dali6i ,dalibin ma d'an
khamis,in har aure kike so ,zan aurar da ke ,amma bazan aurar da ke ga
wannan yaron ba',a tsorace na dubi abbu ,hawaye na fita daga idanuna
nace 'abbu kasan mahaifinsa ne,ka san kasar da mahaifinsa ya fito daga '
,tsawa ya daka mini yace in fitar masa daga falo ya gama magana,kuka
nake kamar raina zai fita ina cewa 'abbu kar ka min haka,kar ka
tarwatsamin farin cikina ,wallahi bilal ne za6ina',ammi ce ta taso ta
daga ni ,ta rungumeni mu ka fita daga falon,dakinta muka je ta zaunar
dani ,ta gogemin hawayena tace' hibbatullah ,ki share hawayenki,ki yi
biyayya ga mahaifinki ..... ki bi umarninsa,domin sanin kanki ne tunda har
ya nuna baya kaunar tarayyarki da wannan yaron toh ba zai ta6a bari ki
aureshi ba',idanu jajir na dubi ammi bayan naja majina nace 'Ammi zan yi
biyayya ,kuma zan bi umarnin abbu ,zan daina zuwa lecturing b.u.k,amma
wlh tlh bazan daina son bilal ba,kuma in har ba bilal na aura ba toh wlh
tlh bani ba aure har abada ammi'',ammi ta janyoni jikinta tana
rarrashina tace'daina fadin haka hibbatullah,ki bar wa Allah komai,zan
tayaki da addu'a ,ke ma ki dage da addu'a ,idan Allah ya kaddara aurenku
da yaronnan .toh bbu mahalukin da zai hana faruwan aurenku,kuma ina son
ki hana yaronnan zuwa gidannan domin kin san had'uwar shi da abbu bazai
yi kyau ba ,in har ba so kike ya zamto abbunki wulakantashi ba',na
sauke numfashi nace 'toh ammi,nagode da kulawarki' * * * Haka na dawo
zaman gida ,ko kofar gida bana zuwa ,hakan kuma yasa abbu yaji
dadi,tsakanina da bilal kuwa soyayyace da tsantsar kauna ,amma ta waya
,domin nace masa kar yazo gidanmu saboda bana son ya had'a karatunsa da
kujiba kujiban zuwa gidanmu zance,da ya kuma nemi dalilin rashin zuwana
skul ,ce masa nayi ,kawai na gaji da lecturing d'in! ,na kuma nemi da ya
turomin accnt num d'insa,da kyar ya amince ya turo mini bayan na masa
magiya kamar wata marokiya,ko wanne wata ina turawa bilal kudi ta mobile
money transfer ,saboda siyan irinsu handout da kuma kula da kaka,a
kwana a tashi bilal ya gama degree d'insa,kuma akayi postn d'insa bautar
kasa zuwa garin edo,yaso mu hadu muyi sallama,amma hakuri na bashi da
cewa 'ya je ya dawo, ya samu aiki muyi aure',tafiyar bilal da sati 2
,kwatsam! sai ga affan da iyayensa a gdanmu ,ashe abbu ne yace suzo su
nemawa affan aurena' ,hibbatu ta dubi meera tace' ban san cewa ina da
taurin kai da zuciya ba sai a lokacin da ammi ta gama sanar dani dalilin
zuwan affan da iyayensa' ,murmushi nayi na dubeta nace 'wllh tllh NA FI
KARFIN AUREN DOLE' Hakkin Mallaka:ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL