Ina zaune a ofis ina marking assgnmts,sai naji ana knocking,ban d'ago
kaina ba,nace 'come in',da sallama ya shigo sannan yace 'maam i'm here 2
submitt my assgnmnt',tsaki naja tare da cewa 'what took u so long ..'
maganar tawa ta katsene a dalilin tozalin danayi da idanuwansa,na nemi
masifar na rasa,tsigar jikina duk ya tashi,wani strange feeling naji a
tattare dani,kame kame na fara yi tare da mi'ka hannu na kar6i assgnment
din,nace 'ur name pls' ,'bilal khamis' ya bani amsa ,na lumshe idanuna
sannan nace 'u can go',marking din dana kasa yi kenan ,tunanin bilal ya
hanani sukuni,a yadda na lura ,he's gentle nd cool,kuma bashi da
hayaniya kamar other students,yana da kyaun fuska da sura,uwa uba
tsabta,duk da dai kayan da yake sawa ba masu tsada bne,kuma shigarsa is
simple nd moderate,and he's kinda matured ,unlike the other students!
Hmm
Ameera wasa wasa ba daman in zauna ,sai tunanin bilal ya fad'o mini a
rai,na zama wata so sluggish,ko da lecturing nake da zarar ya shigo
class ,sai nakasa yin komai ,kuma kullum a makare yake shigowa
class,bana ta6a samun shi class,sai after na shiga ya ke shigowa, amma
nakasa d'aukan mataki ,dana had'a ido dashi ,sai naji zuciyata ta tsinke
!
Rannan na fito daga ofis,hannuna ri'ke da takardu,ina sauri in tafi gida
domin i'm in the period of my month gashi kuma ya min zuwan bazata ,
kuma i 4gt in sa pad a bag d'ina,mota ta na nufa nasa key na shiga
,thankGod black abaya nasaka balle a ga stain,na tada motar tare da yin
reverse ,na fice da parkn space ,sannan nayi hanyar fita daga gate,kuuu!
Naja burki sanadiyar na bige mutum akan keke ,da hanzari na fito
,jikina na rawa na nufi mutumin ,bilal nagani zaune yana karkad'e
rigarsa,cike da hanzari na russuna ina fad'in 'sorry,dafatan baka ji
ciwoba',na tattare masa books d'insa ,tare da saka masa hularsa da ya
fad'i,mikewa yayi yana cewa 'bakomai banji ciwo ba,karki damu
malama',toh in bazaka damu ba,kasa keken naka a but d'in motata ,sai na
sauke ka a gida','i can manage dnt mind',nace 'dis is an order nt a
request ' ,sannan na bud'e but yasa kekensa a ciki ,sannan na bud'e masa
kofa ya shiga na rufe,na zagaya na shga na tada motar muka fice daga
makarantar.....
sai
da muka hau kan titi sannan nace 'malam bilal ina muka nufa',tiryan
tiryan ya mun kwatance har muka iso gidannan,na saukeshi ,na bud'e but
ya d'au kekensa,yana min godiya,nace 'malam bilal ka rike
godiyan,alfarma nake nema a gunka dan Allah in bazaka damu ba',wacce
irin alfarma malama,i kinfi karfin ki nemi alfarma a guna' ya fad'a tare
da russunawa,hannu nasa a jakata na ciro paper da biro na rubuta mai
address din gdanmu tare da lambar wayata ,na mika masa ina cewa 'ina
gayyatarka gidan mu anjima da yamma please',sai da yayi jim sannan yace
'toh malama Allah ya kaimu zanzo insha Allah',murmushi nayi tare da jan
mota ta na bar wajen zuciyata fes,domin yau nayi alkawarin sai na amayar
masa da abinda ke cikin zuciyata,haka na shiga gida raina fes,zuciyata
fal da farinciki,ammi da abbu sai tambayata suke dalilin wannan
farinciki nawa ,ce musu nayi kawai haka na tsinci kaina a hakan,na wuce
daki na kimtsa kaina ,wajajen karfe shida na kamalla had'a girke
girke,sannan nayi wanka na fesa kwalliya cikin wani hadadden gown na
atamfar ghanafabric wato kante ,na kafa d'auri ,na yafa mayafi ,na nemi
gu na zauna a palo ina kallon agogo,karfe 6:40 naji wayata na ringing
,in na d'auka muryarsa naji yana min sallama tare da sanar dani cewa ya
iso,maigadi na bawa umarnin ya shigo dashi ya kaishi guest
parlour,sannan na nufi falon bayan na kara gyara kaina,sai da nagama
jera abincin a kan dinning din palon,sannan na isa gareshi nace 'sannu
da zuwa malam bilal,hope ban takura maka ba',murmushi yayi tare da cewa
'girmanki ne malama babu takurawa sam',iso nayi mai izuwa kan dinning
,sannan na fita na bashi wuri domin ya samu ya ci abincin da kyau,bayan
kamar awa daya ,na koma falon na tadda shi zaune a kan cusion,ma'ana ya
gama cin abinci,murmushi nayi nace 'malam bilal ,na bar ka kai ka dai
ko',sannan na gaishe shi ,ya amsa yana mai kasa had'a ido dani ,gyaran
murya nayi sannan nace 'malam bilal ina son sanin tarihinka ,ina son ka
yarda dani,ka aminta dani ,kar ka 6oyemin komai game da labarinka feel
free,kar kaji komai ,ka dauke ni a matsayin hibba ,ka manta da cewa ni
malama ce a gareka,domin bisa la'akari da yanayinka,halayenka da kuma
dabi'unka,hakan na nuni da cewa a girme ka girmeni nesa ba kusa ba
...zan so sanin wanene kai' ,bilal ya sauke ajiyar zuciya sannan yace
'malama' na katseshi nace 'jst call me hibba please' ,numfashi yaja cike
da dauriya yace 'hibbah' ,ameera wlh sai da na kusan shid'ewa don dadin
jin yadda ya kira sunan in a romantic way,ameera ta yi dariya tace
'hibbatu kenan,ni dai cigaba da bani labari kawai domin na 'kagu inji
dalilin da yasa rayuwarki ta dawo haka.... hibbatu ta dubi meera tare da gyara zama tace
'toh ameera bilal ya cigaba da cewa 'ni ba kowa bane kuma ba d'an kowa
bane' ,katseshi nayi nace 'dakata malam bilal ,ka gayamin lbrnka kawai
',numfashi yaja yace 'na kasance maraya bani da uwa bani uba,a hannun
kakata na girma wato mahaifiyar umma ta ,a yadda kakata ta ban labari
,an had'a umma ta da mahaifina aure ne batare da an binciki asalinsa
ba,kasancewar ummata da kakata an tsanesu agidan sanadiyar so da suka
samu daga gun kakana har rasuwarsa hakanne ya janyo masu tsana mai
tsanani daga gun abokan zaman kakata da kuma dangin kakana, shiyasa da
mahaifina ya nemi auran ummata da gudu dangin mahaifin ummata suka bashi
ita ,domin yayi masu 6arin kud'i,kuma sunga cewa halfcast ne daga
jinsin larabawa ya fito kuma gashi dan kasuwa ne,amma kakata ta manta
sunan kasar mahaifin nawa,haka akayi auran ,ummata ta tare a gidan da ya
siya ya damka mata takardun gidan,ba'ayi shekara da yin auran ba,ummata
ta samu cikina,an haifeni da wata biyu ,mahaifina yayi tafiya izuwa
kasarsu da niyyar in ya dawo ,sai yazo ya tafi damu ,domin ba'a san yayi
aure ba a can kasar tasu ,tafiyar da yayi kenan,domin labarin mutuwarsa
ce ta riski ummata ,sanadiyar had'arin jirgi da ya ritsa dashi,ina da
wata goma sha uku ,ummata ta rasu,hakan yasa rikona ya dawo hannun
kakata,tsangwama da tsanar da ake nuna mini a gidansu ummata,yasa kakata
ta tattara ta dawo gidan gadona,wato gidan da iyayena suka mutu suka
bar mini,da dadi ba dadi haka rayuwa ta cigaba da tafiya,da kyar na
had'a secondary bisa jajircewar kakata don ganin na samu ilimi,talauci
ne yasa ban cigaba da karatun ba,nayi sana'a kala kala,saida
rake,mangwaro da agwaluma,nayi dako ,nayi aikin yaron shago a kasuwa,da
yan kud'in dana samo nake samu muci abinci ni da kaka,a haka na shafe
shekara uku ,daga baya na nemi teaching a wata private ,suka bani,nayi
shekara hudu ina koyarwa a makarantar domin na fidda rai da karatun
degree,kasancewar ina da kwazo sosai wajen koyarwan,hakan yasa mai
makarantar ya nemi yaji lbrna,ya tausaya mini sosai da yaji lbrina,hakan
yasa ya d'au nauyin karatuna,ya nema mini addmission a buk,sanadiyar
fara karatun degree d'ina kenan course din economics,ynxu nake lvl 4
finalyear,kuma kika daukar mu lecture' ,ya goge guntun hawayen da ya
zubo mai ya dubeni yace'kin ji labarina hibba,ni ba kowa bane ,bani da
kowa sai kakata,bani da kadara sai keke na da gidan gado da aka bar min
muke zaune da kakata,kuma kinga gidan dazu da kika saukeni,watanni biyu
da suka wuce Allah yayi wa wanda ya d'au nauyin karatuna rasuwa
!',hibbatu ta dubi meera tace 'ameera na tausayawa mai matu'ka domin
bilal ya cancanci tausayawa daga xuciya mai imani' ,meera tace 'tabbas
hibbatu kin yi gsky ,amma tmby ta itace wannan gidan da kuke ciki shine
gidan gadon ,kuma ina kakar tasa ',hibbatu tayi wani marayan murmushi
tace 'eh gidanne ameera ,kakarsa ta rasu ne bayan aurena da bilal da
shekara d'aya',da sauri meera ta katse hibbatu tace'yawwa zanso in san
ya akayi har kukayi aure ,kuma kika tsalleke daular gidanku kika fad'o
wannan rayuwar,wato rayuwar bilal.... Hakkin mallaka :ABDULAZIZ ILILEE
ISMA'IL