Meera ta shirya tsab,taci abin kari,ta d'auko cooler ta zuba abinci,ta
zuba oat a flask,ta jera acikin basket,sannan ta kira direba ta aikeshi
gun bilal da ya 'kar6o mata adireshin gidansu,bilal sai da ya sha jinin
jikinsa,sannan yayi wa direba kwatance,direba ya gayawa meera cewa gidan
ba nisa ,meera ta bashi umarnin suje ya kaita ,bayan ta yiwa hajiya
sallama! Daidai kofar gidan direba ya sauke meera,hannunta rike da
basket d'in abinci ,ta tura kyauren ta shiga da sallama ,hibbatu da ke
tsugune tana dirzar wanki ,ta d'aga kanta ta amsa sallamar,ganin meera
ce,sai kawai ta cigaba da wankinta ba tare da tayi yunkurin barin wankin
ba,meera ta ajje basket d'in ,ganin hibbatu bazata kulata ba yasa ta
nad'e hannun rigarta ,ta janyo kayan da hibbatu ta wanke tana daurayewa
tana shanyawa,uffan hibbatu bata ce mata ba,har suka gama wankin
tas,hibbatu ta sha mur zata shige daki,meera ta tsaidata ta hanyar cewa
'hibbatu kiyi hakuri ki Yafemin,nasan kalamai na gareki,basu miki dadi
ba,ina son ki manta komai ,mu fahimci juna' ,hibbatu ta dubeta tare da
maimata kalmar 'fahimci juna?' ,'eh mu fahimci juna,ina son sanin
tarihinki,ina son sanin wacece ke' ,hibbatu ta kanne ido d'aya dan
jaraba tace'yar jarida ce ke,ko kuma yar rahoto' ,meera ta marairaice
tace 'hibbatu dan Allah kiyi hakuri ,ki manta da komai,inci arzikin
hajiya mana',hibbatu tace 'toh naji ,ki shigo ciki muzauna',meera ta
dauko basket din abinci ta bi bayan hibbatu suka shiga falo,bayan duk
sun zauna ,hibbatu take cewa bara na fita in siyo maki ko purewater
ne,meera tace never mind ,i'm ok,ga abinci na taho maki dashi ,ta mi'ka
mata basket,hibbatu daman yunwa take ji ,domin ta aikatu yau saboda tayi
gyaran gida sosai kuma rabonta da abinci tun jiya,haka ta kar6i basket
ta dauki kula ta bude ta fara aikawa cikinta abincin tana lumshe idanu
tare da shiwa hajiya da meera albarka a zuciyarta,tas ta cinye,ta d'auko
cup ,ta di6i oat tasha iya shanta ta gyatse ,tana sakace da harshenta
,ta dubi meera tace 'nagode sosai',meera tace 'bakomai,hajiya ma tace a
gaisheki',hibbatu tace ina amsawa,meera ta d'au waya ta kira direba tace
mai ya tafi kawai,zata kira shi in tagama,sannan ta dubi hibbatu a
sanyaye tace 'hibbatu dan Allah ina son ki bani tarihinki,ina son sanin
gaskiyar Ala'karki da imad ,domin na ta6a ganin hoton wata yarinya a
gidansu imad,dana tambaya wacece ita sai ammi tace yayar imad ce,abbu
kuma yace amma ta rasu,haka zalika imad ,ammi ce kawai ban ta6a jin tayi
zancen rasuwar ta ba,hibbatu ki taimaka ki warware min komai',hibbatu
ta goge hawayen da ya zubo mata tace'meera tabbas ni matacciya ce a
garesu,kuma alaka tsakanina dasu babu ita tun daga ranar dana kai bilal a
matsayin mijin da zan aura',sunana.......
Sunana hibba shoaib,'ya ga
shoaib annur da samira,abbuna d'an asalin kasar oman ne,dan boko ne,kuma
hamshakin d'an kasuwa ne,kasuwancinne ya kawoshi nigeria har ya hadu da
ammina a nan garin kano,soyayya ta samu matsuguni a tsakaninsu ,suka yi
aure bayan an binciko asalin abbuna a can oman d'in, d'an sarauta ne
amma bai bawa sauratar muhimmanci ba,kasancewar itama ammina yar sarauta
ce hakan yasa abun nasu yayi kyau,abbuna ya cigaba da kasuwancinsa
tsakanin kasashe daban daban hakan yasa yakejin yare daban daban
musamman hausa tunda yana auren bahaushiya,kuma babu kasar da baya
tafiya da ammina,domin nigeriar kanta jifa jifa suka le'kota,shekara
biyu da aurensu suka haifeni,naga so ,gata,kulawa da tattali a gun
iyayena,ina da shekara 5 ,aka haifi imad,daga kanshi ammi bata kuma
haihuwa ba,family d'inmu gwanin sha'awa,tafiye tafiye abbu bai fasa
ba,domin damu yake tafiya ,wani zuwan da mukayi oman ne ,kakata wato
mahaifiyar abbu ta rikeni ,domin bata bari sun tafi dani ba,lokacin imad
ba'a yaye shi ba,a oman nafara karatun arabi ,primary da secondary,har
na kamalla,jindadi da gata duk nasamu daga gun kakanni na,iyaye na
kuwa,suna zuwa oman akai akai ,imad kuwa a lokacin ya girma yayi wayo
domin shima yana johannesburg boarding college,kwatsam sai aka wayi gari
kaka ta rasu ,hakan yasa bayan anyi arba'in ,abbu da ammi suka wuce
dani,nayi kukan rasuwar kaka domin ta so ni,ta nuna min gata,nigeria
muka dawo ,garin kano domin a lokacin kud'i sun zaunawa mahaifina
,kasashe kad'an ne baida kamfani a can,sai danayi zaman gida na shekara
d'aya,a lokaci hausa ya zauna a harshena sosai daman can mun iya domin
ammi tana koya mana,abbu ne keyi mana larabci,abbu yana son yaga munyi
ilimi mai zurfi ,hakan yasa aka sama min admission a baltimore
university..a lokacin imad yana finalyear d'insa a college ... Na wuce US
bisa rakiyar abbu da Ammi ,sai da abbu ya kamalla mini regstration a
makarantar ,sannan ya bar amanata a gidan balaraben abokinsa wanda yake
lecturer ne a makarantar ,yana zaune da matarsa da d'ansa mai suna
AFFAN,ban samu matsala ko kad'an a zamana a gdan ba,domin suna da kirki
sosai,na fara karatun had'a degree bangaren economics,cikin kwanciyar
hankali,ba ruwana da yin kawaye,gaisuwa ce kawai ke had'ani da mutum,a
haka har na shafe shekara biyu ,a lokacin affan ya yi graduating daga
skul din,affan shine abokin hira ta ,shine ya maye mini gurbin
kawaye,yana da kirki,gashi da sanyin hali,ya nuna min so ,amma ba'a je
ko ina ba ,na taka masa birki,domin kwata kwata soyayya baya cikin tsari
na ,a kwana a tashi na kamalla karatuna,na mallaki kwalin deegree
d'ina,na kuma 'kara shekara d'aya na had'a masters,su ammi,abbu da imad
sun zo convocation dina,a lokacin affan ya yiwa abbu batun yana so na da
aure ,da abbu ya tuntu6eni da zancen affan ,ba boye boye nace ni bana
ra'ayinsa ,abbu ya bawa affan hakuri,domin ba zai mini dole ba,haka
muka, dunguma muka wuce oman ,sai da mukayi wata 6 a can ,sannan muka
taho nigeria ,a lokacin admission d'in imad ya fito ,ya dad'e yana neman
medicine a medical unvrsties, amma baya samu ,wannan karan sai medical
university of cyprus ta bashi,haka ya had'a kayanshi,muka rakashi cyprus
d'in,saida muka tabbatar da yayi settling down ,sannan muka dawo
nigeria ,zaman gida da kad'aici ne ya ishe ni,saboda rashin imad ,ammi
kuma ba kowacce hira mukeyi da ita ba ,duk da dai ,ni da ita tamkar
kawaye muke ,tana jana a jiki,hakan yasa na ro'ki abbu da ya nema mini
part time lecturing a B.U.K ,cikin sati d'aya na fara lecturing a b.u.k
,economics department ,ina koyar da yan degree, level 4 ...hibbatu ta
sauke ajiyar zuciya ta dubi meera tace 'anan tarihin soyayyata da bilal
ta soma ,kasancewarsa d'alibi cikin d'aliban dana ke koyarwa.... Menene
ra'ayinku,kuyi cmmnt Hakkin mallaka:ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL