Gidane d'an 'karami mai dau'ke da d'akuna biyu ,falo d'aya,sai tsakar gida,kwance take a falonta mai tattare da 'kazanta,tana sanye da zani daban ,riga daban ,haka zalika d'ankwali,munshari take zabgawa,tayi wata irin kwanciya,ta ware kafafu kamar ba mace ba,miyau yana mai dilala daga bakinta,sanadiyar mafarkin da takeyi wai gata chan tana cin tsiren hanta da madara,firgigit ta farka tana sosa kanta tare da tand'ar bakinta kamar wata mayya,agogon da'kin idanunta suka yi mata tozali da,2:00pm idanunta suka gane mata,da hanzari ta suri mayafinta dake kan fanka,tayi bol da kwanon da taci d'anmalele tun shekaranjiya dake kwance a tsakiyar falon,ta shuri silipas da 'kafarta,sannan ta fice daga gidan tare da 'kulle 'kyauren gidan da kwad'o... * * * Zaune yake akan benci,ya zabga uban tagumi yana mai tunanin rayuwa,jin ana buga gate da 'karfi yasa ya dawo hayyacinsa tare da tashi da hanzari ya nufi gate d'in yana tambayar wanene, 'ni ce!' ta bashi amsa da 'karfi,da sauri ya bud'e gate d'in tare da cewa 'HIBBATU lafiya ,meya faru' ,harara ta zabga mai tare da tureshi gefe ta shigo tana cewa 'ina lafiya kuwa ga talaka irinka ,da har zakayi tsammanin lafiya a kowanne lokaci,cefane na biyoka in amsa' tana mai yatsina fuska,a sanyaye yace'cefane kuma hibbatu!' ,'eh cefane,ko ka bani ne kafin ka taho nan?','amma naga akwai ragowar kwakin dana siyo jiya,kiyi ha'kuri ,ki kwad'anta kici mana',da sauri ta dakatar da shi tana cewa 'nayi maka kama da matar da kwaki zai samu matsuguni a tumbinta,wallahi ni tsiren hantar danayi mafarki nake son ci!','tsiren hanta kuma?' ya maimata ,tace 'eh tsiren hanta mai zafi da wadatacciyar 'kuli_'kuli' ,'bani da kud'i!' ya bata amsa yana mai kauda kansa gefe ,tsalle tayi ta dire,ta cire mayafi ta d'aure a 'kugunta,tana tafa hannayenta tana cewa 'kan ubanchan d'arin biyun ce baka da ita dan jaraba,wallahi BILAL dole ka nemo kud'i yanzunnan,in ma ta kama, ka shiga cikin gidannan kayi masu fashi da makami mana ,ka tsaya kana ce mini baka da kud'i,rashin kud'inka bazai sa in fasa cin tsiren hanta ba,ahtoi!,kai kunya ba kaji ,in taho maka da karamar bukata irin wannan amma ka kasa biya min ita!' ta cigaba da surfa mai masifarta da bala'i ,bai tanka mata ba,ya zuba mata na mujiya kawai... Karar Horn! Din da akayi ne daga wajen gate ne,yasa Bilal ya juya ya bar ta anan,da sauri ya wangale gate d'in,wata arniyar azababben mota mai numfashi ce ta danno kai.....ido,hanci da baki bud'e hibbatu ta bi motar da kallo.
Source Abdulaziz
Title :
Mijin Haya Part 1
Description : Gidane d'an 'karami mai dau'ke da d'akuna biyu ,falo d'aya,sai tsakar gida,kwance take a falonta mai tattare da 'k...
Rating :
5