Haba ameera ,ki hakura da imad fa kikace,gsky ki sake tunani,domin zanso
ki zama matar imad wllh',meera ta sauke numfashi tace 'nima zan so in
aure imad,musamman a ynzu da zuciyata ta fara bijiromin da wani ba'kon
al'amari'',wani irin al'amari? hibbatu ta tmby, tana mai sasukar
doya,meera ta mi'ke tsaye tana cewa 'muje kitchen in had'a mana tea
',hibbatu ta mike itama ,bayan ta danna slice d'in doya ta karshe a
bakinta,suka fice daga d'akin... * * * Bilal ya fito daga wanka,ya nufi
d'akinsa yana shafa mai,hibbatu ta shigo ,tana mai murmusawa ta dubeshi
tace 'ina kwana' ,'lfy lau' ,'ya aiki,ashe ka shigo?','eh,wanka
nayi,shiryawa zanyi in koma',hibbatu tayi jimm ,sannan tace 'bilal ya
batun albashinka ,alhji bai fara biyanka bane?','oh hibbatu kenan ,kema
kinsan ban shafe wata d'aya da fara aikin gadinnan ba,kuma a hakan ma
alhj yana ban yan chanji,su nake baki kiyi cefane,kuma kince hjy tana
baki dubu 1 ,dubu 2 haka a kullum idan kikaje gidan,toh me kika nema
kika rasa a ynz','toh naji,amma kasan cewa dai ,ina bukatar tufafi da
kayan kwalliya ko?',rungumota yayi yana cewa 'hibbatuna ,kar ki
damu,insha Allah da zarar na amshi albashina,zan baki gb daya ,kiyi
siyayyar da ranki ke so'','toh mijina ngd,',ta karasa shiryashi,ya fice
,tana ce masa sai ta iso..... *** Meera tana tsaye bakin taga, tana
jiran shigowar bilal,domin daga shekaran jiya zuwa yau ,ta tabbatarwa da
kanta cewa zuciyarta ta kamu da matsananciyar soyayyar bilal wanda ita
kanta banta shiryawa faruwan hakan ba,wanda hakan ke sawa ba ta da
aiki,illa tsayawa gaban tagar dakinta,tana kallon bilal(domin ita kanta,
ta san cewa tsakaninta da bilal sai dai kallon,don bazata iya aurewa
hibbatu miji ba)... A bangaren bilal kuwa,yana lura da tsayuwar meera a
taga tana kallonsa,amma bai bari ta gane ba,saboda shima ,tun ranar da
ya fara d'ora idanunsa a kanta (ranar data dawo daga cyprus @mijin haya
1&2),yaji wani bakon al'amari a gareshi,amma a kullum yana karyata
al'amarin ne,domin tunawa da matsayinsa na maigadi wanda talauci yayiwa
kamun kazar kuku,da kuma wassiyar kaka a gareshi,kafin ta rasu ,yasa
yake kudurtawa ranshi ,cewa 'ko da zai d'ige da soyayyar meera ,yasan
cewa ba zata ta6a iya zama mata a gareshi ba'...
Turo gate d'in da bilal
yayi ne ya katsewa meera tunanin da takeyi,ta sauke numfashi tare da
zubawa bilal idanu,bilal kuwa kasa jurewa yayi shima,domin a yau bai
hana idanunsa sauka akan fuskar meera ba,kallan kallon zallar so da
kauna suke yiwa junansu , domin a yau suka tabbatar da tasirin SO a
rayuwarsu,a yau suka tabbatar wa zukatansu cewa soyayyar da suka riska a
baya ba soYAYYA bace ,face had'uwar jini da kaunar juna,amma SO shine
abun da suke ji a zuciya da ruhin jikinsu a yanzu... Hibbatu ce ta turo
gate d'in,hakan yasa meera ta sauke labule tare da barin gun tagar,zama
tayi akan gadonta wasu zafafen hawayena suka zubo daga idanunta,ta ri'ke
kanta da hannu biyu tana mai ayyanawa a ranta cewa 'zuciyarta bata mata
adalci da ta kamu da soyayyar Mijin hibbatu,ya zama tilas ta yakice
bilal daga zuciyarta,ko da kuwa hakan na nufin salwantar rayuwarta',
bilal kuwa saukar da idanunsa yayi daga kan tagar da'kin meera tare da
kai dubansa ga hibbatu,fuskarshi d'auke da murmushi,'sannu da duty' tace
masa, tare da shigewa ciki,ya dubi hanyar data bi yana mai ayyanawa a
zuciyarsa cewa 'SO bai masa adalci ba,da har zai yi tasiri akan macen da
ba hibbatu ba,hibbatu wacce ta masa halaccin so a rayuwa,ya zama tilas
,ya goge soyayyar meera daga cikin zuciyarsa,ko da kuwa hakan na nufin
kuntatawa zuciyar tasa'... Hibbatu ta tura kofar d'akin meera ,harshenta
d'auke da sallama,meera ta amsa a sanyaye tare da yi mata sannu da
zuwa,tana goge hawaye daga kan fuskarta,hibbatu ta 'karaso ta zauna kusa
da meera,hannu tasa ta dafa kafad'arta tana cewa 'ameera,nasan cewa
rabuwa da masoyi akwai zafi ,amma ya zama tilas ki farantawa abbanki rai
a yanzu ta hanyar fitar da mijin aure!,na yi tunani akan mafitar da
imad ya nema maku na cikar burinku na mallakar junanku a matsayin miji
da mata ba tare da kun 6ata wa iyayenku rai ba,kuna da chance akan
soyayyarku ,tabbas babu mafita a al'amarinku ,illa ki auri MIJIN HAYA a
yanzu,kamar yadda imad ya fada miki,domin aiwatar da hakan ne kad'ai zai
zamo mafita a gareku! Ameera ,ina son ki buga masa waya kice masa kin
amince zaki auri MIJIN HAYA',meera ta dubi hibbatu da jajayen idanunta
fuskarta d'auke da d'imbim mamakin kalaman bakin hibbatun...,hibbatu
bata damu da kallon da meera tayi mata ba ,ta cigaba da cewa 'tsuntsu
biyu zan harba da dutse d'aya ,in har bilal ya zamto MIJIN HAYA a
gareki!........ [this is just the begining]na ILILEE Mamaki,d'imuwa,tsananin murna yasa meera ta
zama beben karfi da yaji,domin baki bud'e ta ke kallon hibbatu,hawayen
farin ciki na zuba daga idanunta ,wanda hibbatu ta d'auka hawayen zafin
rabuwa da imad ne...'nasan zaki firgita ga jin kalamaina meera,amma nima
danayi tunani akan batun MIJIN HAYA , sai naga babu wanda ya dace ya ci
wad'annan makudan kud'i face ni danake yar uwa ga imad,da akan akaiwa
wani 'katon banza wannan kud'i yaci kuma ya 'ki sakin ki,gwara ni da
mijina mu cisu,domin nasan bilal a matsayin 'kanwarsa ta jini zai
d'aukeki,meera ina son ki d'auka a ranki cewa auren mijina a matsayin
MIJIN HAYA yana nufin zaki zauna gidanmu a matsayin wacce take zaman
HAYA,wato zaman wucin gadi,ki d'auki bilal a matsayin d'an uwanki na
jini,shakikinki,har zuwa lokacin da imad zai dawo ,a sake ki,ki dawo
gida kiyi idda,duk da dai iddar ba ta hau kanki ba,dan kaucewa zargi
zakiyi iddar,mu kuma kudadennan da zamu kar6a ,zai zamo mana magani ga
talaucin mu da muka shafe shekara 6 a cikinsa,wato riba biyu
kenan,killacewa d'an uwana matarsa,ga kuma arxiki da zamu tako,ameera
zan kyaleki kiyi shawara da zuciyarki,amma ina son ki duba lamarin nan
ta fuskar fahimta,domin bazan so imad ya rasaki ba,kuma haka zalika
zanso wannan kudin HAYAr ya shigo hannunmu',hibbatu ta tashi ta gyara
zaman mayafinta tare da ficewa daga d'akin ba tare da ta jira meera tayi
magana ba...meera wani ni'imtaccen ajiyar zuciya ta sauke,ta sha'ki
wani iskar tana lumshe idanu, tare da cewa a fili 'bilal zai zama
mallakina,mijina,mahad'in rayuwata' ,d'aga hannayenta sama tayi tare da
cewa 'ALLAH UBANGIJI YASA BILAL YA AMINCE,NAYI IYA KOKARINA GANIN NA
YAKICESHI SOYAYYARSA A ZUCIYATA SABODA HIBBATU,AMMA GASHI DA KANTA TAYI
MINI TAYIN AURENSA,KO A GUNKA YA ALLAH BANI DA LAIFI, DOMIN DA ZARAR NA
SHIGA GIDAN BILAL A MATSAYIN MATARSA BA SHAKKA MUTUWA CE KADAI ZATA
RABANI DA WANNAN GIDA,ALLAH KA CIKA MINI BURINA BILAL YAZAMA MIJINA
HALAK MALAK' ta sauke hannayenta tana cewa 'hibbatu kenan,bayan
'kafiya,'karya da 'kwadayi ! Wauta da sakarci suna dawainiya da ke,zan
cigaba da bin ki a yadda kike so,har lokacin da zan tare a d'akin aurena
da bilal,a lokacin zaki tabbatarwa da kanki cewa ke mai 'karamar
kwakwaluwa ce,kuma zaki tabbatarwa kanki cewa bilal MIJIN AURE NA NE ba
MIJIN HAYA ba.....ta 'karasa tagar d'akinta ta d'aga labulen tana mai
zubawa bilal idanu da ke zaune kan benci ya kafa radio a kan kunnensa... ¤BAYAN KWANA UKU¤ Meera ta gaji da
uzzurawan da hibbatu ta uzzura mata akan ta amince ta auri bilal a
matsayin MIJIN HAYA! Meera tana ta avoiding issue d'in, domin tana mai
tausaya hibbatu nan gaba,domin ita kanta meera tasan cewa da zarar ta
auri bilal,mutu ka raba wlh,ko da shi bilal d'in baya sonta... Yau kamar
kullum ,hibbatu ta shigo d'aki ta samu meera a kwance,bayan meera ta
amsa sallamar ,sai ta kauda kanta ,kuma batare da ta dago daga kwanciyar
da tayi ba,a sanyaye hibbatu ta ce 'ameera yau kwana uku kenan,kin 'ki
cewa komai dangane ga maganar da nayi maki,pls ki amince ki auri
Mijina,kar ki bari kud'innan su su6ce mini' ,meera ta juyo ta dubeta
tace'toh naji sista,na amince zan auri MiJiNKI,amma duk abinda ya biyo
baya ,kiyi kuka da kanki',hakora a washe tace ,'babu abinda zai biyo
baya face alkhairi,yaushe zai turo kud'in ?,kuma dan Allah ya cikashe 8
d'in ya dawo 10!','toh naji zan nemeki idan nagama waya da shi',hibbatu
ta tashi ta fice zuciyarta fes,meera taja dogon tsaki bayan hibbatu ta
fice tace 'a shirye nake in biya ko da miliyan dubu ne,in har hakan zai
sa bilal ya zama mijin aurena',wayarta ta d'auko ta kunna domin tun
ranar da suka gama waya da imad akan MIJIN HAYA ta kasheta',sakonninsa
ne suka fara shigowa,bata kai ga karantasu ba,kiransa ya shigo,ta d'auka
tare da yin sallama,imad ya sauke ajiyar zuciya ya amsa,ba kai ga yin
magana ba meera tace 'na amince da auren MIJIN HAYA,ka turo kud'in' 'da
gaske kike?' ,'eh nayi tunani akai,there's no way out,HUSBAND FOR HIRE
is the only solution 2 d situation we are in' ,i love u so much
meera,wanene mijin,had'ani dashi a waya in jaddada masa
sharud'ana','talaka! matsiyaci ne! kar ka damu ,zan killace maka kaina
har xuwa lokacin da zaka dawo ya sakeni ,ka aureni,just trust
me','shikenan meeralovita ,i'm so happy wllh and i trust you',suka
cigaba da hira yana gayamata yadda yayi missing d'in muryata a kwana 6
da suka wuce,in ya kira wayarta a kashe..... Washegari meera ta samu
alert d'in miliyan takwas is transfered in to her account, tana gama
karantawa tayi murmushi tace 'hibbatu & imad the two of them hve
smethn in common 'WAUTA da SAKARCI' ,shiryawa tayi cikin wata doguwar
riga mai ratsin sky blue da dark blue,tayi light make up,ta dau handbag
ta saka wayarta,checkbook dinta,da kuma check d'in 2million da abbu ya
bata kyauta,sai kuma empty mini luggage bag da ta Washegari meera ta
samu alert d'in miliyan takwas is transfered in to her account, tana
gama karantawa tayi murmushi tace 'hibbatu & imad the two of them
hve smethn in common 'WAUTA da SAKARCI' ,shiryawa tayi cikin wata
doguwar riga mai ratsin sky blue da dark blue,tayi light make up,ta dau
handbag ta saka wayarta,checkbook dinta,da kuma check d'in 2million da
abbu ya bata kyauta,sai kuma empty mini luggage bag da ta dauko! Karfe
10:00 hibbatu ta shigo gidan,bayan ta gaishe da hajiya ta wuce d'akin
meera,tana shiga d'akin meera ta wurga mata luggage bag d'in tana cewa
'ri'ke jakar,ki rakani bank in ciro miki kud'in HAYAR MIJINKarfe 10:00
hibbatu ta shigo gidan,bayan ta gaishe da hajiya ta wuce d'akin
meera,tana shiga d'akin meera ta wurga mata luggage bag d'in tana cewa
'ri'ke jakar,ki rakani bank in ciro miki kud'in HAYAR MIJINKI.....IHakkin Mallaka:ABDULAZIZ ILILEE
ISMA'IL