الحمد لله
Addu'ar da ake yi yayin yanka dabbar layya itace. Bayan mai yankan ya dora kafarsa akan wuyan dabbar sai yace:
ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ، ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻫﺬﺍ ﻣﻨﻚ ﻭﻟﻚ ، ﻫﺬﺍ ﻋﻨﻲ . ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺗﻘﺒﻞ مني .
*Idan kuma zai hada layyar da iyalansa* Sai yace:
ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ، ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻫﺬﺍ ﻣﻨﻚ ﻭﻟﻚ ، ﻫﺬﺍ ﻋﻨﻲ . ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺗﻘﺒﻞ مني و آل بيتي
*Idan kuma wani ne ya waqilta mai yankar ya yanka masa dabbar sai yace:*
ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ، ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻫﺬﺍ ﻣﻨﻚ ﻭﻟﻚ ، ﻫﺬﺍ ﻋﻦ (ﻓﻼﻥ ) ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺗﻘﺒﻞ ﻣﻦ (ﻓﻼﻥ) ﻭﺁﻝ (ﻓﻼﻥ)
A duk inda aka ga an saka wannan fulaan (فلان) din sai a kira sunan mai layyar. "Fulaan" yana nufin "WANE"
*TARJAMA*
Bismillaah, wa Allaahu akbar, Allaahumma haaza minka wa laka, haaza ‘anni. Allaahumma taqabbal minni wa aali baiti.
Ko kuma a maimakon cewa _Allaahumma taqabbal minni wa aali baiti_ Mutum yana iya ambatar sunansa wato misali idan sunansa *Usman* sai yace _Allaahumma taqabbal min Usman wa aali Usman_ Kamar yanda Annabi (sallallahu alaihi wasallam ya ambaci sunansa da iyalansa da kuma al'ummarsa.
*Idan kuma wani ne ya waqilta mai yankar ya yanka masa sai yace:*
Bismillaah, wa Allaahu akbar, Allaahumma haaza minka wa laka, haaza ‘an [ fulaan], Allaahumma taqabbal min [fulaan] wa aali [sai kira sunan mai layyar].
Amma fa abin lura anan shine cewa *BISMILLAAH* kadai ne wajibi. Sauran duk mustahabbi ne ba dole bane.
Domin qarin bayani: Al- Bukhaari (5565), Muslim (1966), Muslim (1967), Al-Tirmizi (1521), Sharhul Mumti (7/492).
Wallahu a'alam
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك.
Title :
Me Ake Fada Yayin Yanka Dabbar Layya?
Description : الحمد لله Addu'ar da ake yi yayin yanka dabbar layya itace. Bayan mai yankan ya dora kafarsa akan wuyan dabbar sai yace: ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ، ﻭ...
Rating :
5