Majalisar Wakilan Nigeria ta dakatar da tsohon shugaban kwamitin kasafin kudinta, Abdulmumini Jibrin, na tsawon watanni shida, bayan da ta same shi da laifin karya ka'idojinta.
Dan majalisar, wanda ke wakiltar Kiru da Bebeji a Kano, ya shiga takun-saka da shugabannin majalisar ne bayan da ya zarge su da yin cushe a kasafin kudin kasar na shekarar 2016.
An kuma haramta masa rike kowanne irin mukami a majalisar har zuwa karshen wa'adin wannan majalisar - wato 2019.
Kazalika sai Jibrin ya rubuta takardar neman afuwa tukunna kafin ya dawo zauren majalisar, ko da wa'adin dakatarwar ya cika.
Kwamitin da'a na majalisar ne ya bayar da rahoton binciken da ya yi kan zargin bata sunan majalisa da kuma saba ka'idojinta, wanda mafi yawan 'yan majalisar suka amince da shi.
Sai dai Honourable Jibrin bai halarci zaman ba, yana mai cewa ba za a yi masa adalci ba.
Ya kara da cewa lamarin na gaban shari'a.
BBC Hausa
Title :
Majalisar Wakilai Ta Dakatar Da Abdulmumini Jibrin Na Kwana 180
Description : Majalisar Wakilan Nigeria ta dakatar da tsohon shugaban kwamitin kasafin kudinta, Abdulmumini Jibrin, na tsawon watanni shida, bayan da ta s...
Rating :
5