Assalamu alaikum Mallam dafatan kana lafiya.
Mal. ina cikin yin jinin al'ada ta ne sai nayi mafarkin da ban gamsu da shi ba (wato mafarkin Jima'i) kuma ban san ko na fitar da wani abu ba.
Toh mallam in na tashi wanka niyya biyu xanyi ko daya? Nagode.
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
In dai lokacin da kika farka baki ga komai ajikinki ba, to wankan janabah bai wajbta akanki ba.
Shi wanka ana yinsa ne idan aka hakkake (tabbatar) da fitar Maniyyi ko ta dalilin mafarki ko afarke tare da jin dadi. Ko kuma ta dalilin boyuwar kan gaban Namiji ajikin Mace, koda bai yi inzali ba.
- Don Qarin bayani aduba wadannan litattafan : Matnul Akhdariy, Matnul Al-Ashmawiyyah, Iziyyah, RISALATUL QAIRAWANIY (Dukkansu aduba cikin babin dake magana akan Janabah).
WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU (12-05-2016).
Title :
Mafarki A Lokacin Jinin Haila
Description : Assalamu alaikum Mallam dafatan kana lafiya. Mal. ina cikin yin jinin al'ada ta ne sai nayi mafarkin da ban gamsu da shi ba (wat...
Rating :
5