Wani asibiti dasuka gani a hanyar barin garin Jigawa suka tsaya,Barraq ya dauko ta suka shiga ciki, kin dubata sukayi waisai suntaho tareda police dakuma record din abunda yafaru dahar aka mata wanan mugun dukan. fitowa sukayi Barraq ya shigar da ita baya,ya kwantar da ita a kife saboda yanda bayan ke jini,ya kalli Muzzamil yace”mutafi Abuja kawai,zan kira family Doctor dinmu ” yakoma gaba ya zauna Muzzammil ya tada motar suka dau hanyar Abuja.
Wuraren 5 na yamma suka isa Abuja yace ma Muzammil” just kaini gida,kaisai kawuce kasan friends dinmu na nemanka yanzu” Muzammil ya saukeshi akatafaran harabar gidansu Barraq yadan mishi murmushi yace” thanks for everything, katafi they need you more than I” Muzammil ya kada mishi kai kawai Barraq ya fito ya bude kofar baya yasa hannu ya dauketa yay side dinshi da ita, ahankali ya kwantar da ita kan gado, yacire tazarcen dake jikinshi yafito daga bedroom din yafita daga dakin zuwa dakin Amma, da sallama ya shiga, Amma ta amsamai da murmushi tace”ahh mutanen biki har an dawo” yay murmushi yace “eh amma”, yadan Sosa kai yace”emm Amma dama damuna mota nakira Dr Faruk nacemai muhadu a gida yazone?” Amma tadanyi dariya tace”oh,tsufa yasoma kamani,abunda fa zan fadama kenan, yazo dazu yanama falon baki” Barraq yace “ok ina auta?” Amma tace “auta tatafi islamiyya” yace “ok”.
yajuya zai fita Amma tace “kaine bakada lpy?incedai ba nama kaci dayawa ba?” Ya girgiza kai tareda fadin “no Amma bani bane” yasakai yafita daga dakin, dakin baki yaje yasamu Dr Faruk a wajen suka gaisa sanan yace “muje ka ganta”. yana gaba Dr Faruk na baye dashi,har bangaren shi, bedroom yabude suka shiga kwance take rubda ciki saidai fuskarta na kallon hanyar kofa, mamaki yahana Barraq magana saidai yadaga hannu yana nunata,da kyar bakinshi ya iya furta “Ku..kur..ma! Dama kece Rufaida??” danshi kwata kwata sai yanzu ya lura dama fuskanta,sai yanzu ya kalli fuskarta. Dr Faruk dake bayanshi yace”lpy Barr naga ka tsaya ne” Barr yadan girgiza kai tareda fadin no,shigo kaduba bayan ya matsa ma Dr Faruk yakaraso cikin dakin Barr ya jingina da bango yay shiru yana mamaki to maizai sa farkon haduwarshi da Rufaida tamai karya? Maganan Dr Faruk yadawo dashi daga duniyar tunanin daya lula yace”amm Barr zan samu light shimi haka da karamin bowl” Barr yace “eh,I think so”. yafita zuwa shashin Amma kitchen ya shiga ya dauko karamin bowl saiya wuce dakin auta, wani Babban akwati daya kawomata lokacin dayaje Russia ya dauko ya bude wani shimi na mata mara nauyi mai dan girma ya dauko yafito daga dakin yakoma shashin shi, ya shiga bedroom din yabama Dr Faruk ya karba,almakashi Dr yasa ya yaga rigan dake jikinta daga sama zuwa kasa ta baya, bayanta gabaki daya ya bayyana, duk tabon bulala sai fitar da jini suje, Dr Faruk yajuyo ya kalli Barr yace”dis is child abuse, waye ya daketa haka 4godsake?”Barr yay folding hannu a kirji ya sauke ajiyan zuciya ahankali yace”her Grandma, labarin nada tsawo” Dr Faruk ya girgiza kai kawai yabude jaka ya ciro wayansu gora guda biyu da allurai biyu ya yanko auduga da almakashi ya tsoma audugar a cikin ruwowin daya hada a bowl sanan yakai bayanta yadaura kan ciwon ihu tasaki tareda kama zanin gadon da karfi tana shure shure da kafa, Barr ya lumshe ido, ganin bazai iya daurewa ba yasa yafita daga dakin ya zauna akan kujera ya dafe kanshi yana huci, jiyake kaman ya dauke mata ciwon.
Fitowar Dr yasa ya dago kanshi ya kallai tareda fadin “hw far Dr?akwai any ciwo?” Dr Faruk yace “no any ciwo,kawai yarinyar na bukatan hutu tareda abinci mai kyau,yanzu tana bacci zata iya farkawa yau, hala kuma sai gobe ko jibi ma self,cus nabata allurai dazasu sa jikinta yay relax” Barr yace “to thank you” yamikamai hannu sukai sallama yatafi. fadawa kan kujera yayi tareda fadin “why Rufaida? Maisa kikaimin karya? Duda kin ganni a kauyen Ku baki taba nuna kinsani ba”, da sauri yace “to kodai shine d reason y take yawan cemin inada kirki? Ko saisa ta taimake ni cus nima nataba taimakon ta?” Ahankali ya furta yess hakane yanzu na samamma tambayata amsa. Dan murmushi yayi yace “in sha Allah wahalar ki takare,is a promise Rufaida, saina share miki hawaye, iyayenki dakika rasa saina maye gurbinsu” lumshe ido yayi tareda gyara kwanciya akan lumtsatsiyar kujeran yadaura hannu kan zuciyar shi saikuma yarufe ido da sauri yanadan murmushi daban gane maanar shiba.
Ringing din dayar wayarshi daya bari a gida yasa ya mike a kasalance ya jawo wayar dake kan center table,ganin sunar daya bayyana a screen yasa yay murmushi ya dauka harda daga kafa yace” mana!I missed yhu” daga dayan bangaren naji matar da yaren turenci tace” my baby I missed you ya kk?” Yay murmushi yace “mee too mummy ya jikin ki? Hope kina zuwa check up dinki?” Tace “yes ina zuwa”. bayan sunyi dan maganganunsu na da da uwa sanan ta magana cike da damuwa tace ” son har Yanzu bakaga yarinyar dakace zaka kawomin ba,nagaji da zama nikadai no grandson, no in-law, inason wani dazan kula dashi and pamper with luv”murmushi yayi yace”Mummy na ganta,but batada lpy”arude ta tambayi maiya sameta? ya sanar da ita komi kan Rufaida, kuka sosai Mum din Barraq tai a waya da kyar ta iyayin shiru sanan tace”son I beg yhu duk yanda zakayi kayi kamata visa yau tomorrow ka kawomin ita,I need to shower her with my luv,zan zame mata uwa data rasa,banga Rufaida ba amma inason Rufaida, banga Rufaida ba amma Rufaida tadawo yata,just try son, ka kawomin ita gobe,I need to take good care of her” ajiyar zuciya yayi sanan yace”ok mummy, in sha Allah gobe zankawota” sukai sallama ya katse wayan sanan yatashi ya shiga Bathroom yay wanka anan bayin falon,yawuce bedroom dan dauko kayan dazaisa yatafi yaga ko zai iya samarmata visa, bude kofa yayi adaidai lokacin tana fadin “Umma tsuntsun,zai kamani,wayyo Umma yana Jana yana bina”.. Da sauri yakarasa cikin dakin ya tsugunna agaban gadon yana hura mata iska a fuska tareda shafa zufan daya gani a goshinta,ya saka hanunshi cikin nata yana kallon fuskarta dayay fayau, gashi gashin gefen fuskarta sun kwanta lub tai wani irin simple kyau, ahankali yakai bakinshi kan goshin ta ya sunbaci goshin tareda sa hannu ya share wurin yana murmushi yana kallon fuskarta yace” wani tsuntsu ke damun min baby na? Koma wani tsuntsu ne just go, yabarmin baby na tai bacci” ahankali yaga ta sauke ajiyar zuciya tacigaba da bacci tareda kankame hanunshi sosai.
Ahankali ya zame hanunshi daga nata yadau kayan dazaisa yafita daga dakin yaje falo ya shirya tsaf ya fesa turare, sanan yadawo dakin ya tsaya a gaban gadon yana kallon ta hanunshi ya zura cikin aljihu ya dauko wayarshi ya tsugunna ya dauketa hoto yana mai murmushi ahankali yace”sleeping beauty, maybe I can use it as her passport”. yadau car keys yafita daga dakin.
******
Bayan kwana biyu.
Yau takama litinin,fitowarshi daga kotu kenan shida PA,sai murmushi yake,kokari press suke suga sunmai yan tambayoyi danyau ya kayar da Babban mai saida miyagun kwayoyi,yatona mishi asiri shida mukarraban sa inda aka kaisu gidan yari amma baida lokacin amsasu dan tafiya gareshi yau. Tun kafin yakai wurin mota aka budemai ya shiga da sauri yana duba agogon hanunshi tareda dafe kai”Lord! Nakusa lattin flight to Russia ” ya kalli bodyguard dake tuki yace” kai sauri 5 flight dinmu zai tashi and dis is already 4:00pm”.
Suna isa gida yafito daga mota, yana cikin sauri yaje dakinshi yaji an fado bayanshi ana “uncle B oyoyo”, juyota yayi yana murmushi yaja kunnen ta “auta bakiji ko”, tadanyi Kara ya sake kunen, rikemai hannu tayi suka cigaba da tafiya tana bashi labarin school yau, saida yakai bakin kofa ya tsaya. auta ta kalleshi, yay mata murmushi yace “yauwa Auta oya tafi kinji anjima zanzo, ki gaida Amma” ta noke wuya tana murmushi. yadan daure fuska tareda fadin “tafi mana”tai zuru-zuru tana kallonshi tace” uncle B kullum kullum yanzu baka bari nashiga dakin ka why? Abu kake boyemin ko?amma ai kace ni kawarka ce ko? Kuma ina fadama all my secrets” tabashi tausayi dakuma dariya yadan rage tsawo tareda sa hannu ya share dan guntun hawayen daya zubo a idonta yana murmushi ya girgiza kai yace “kinsan banason kuka ko?” Ta dagamai kai, yace” ok, ai mun riga mun kulla fadama juna secret, banason ki shiga dakinne cus is too dirty, kuma nasan bakison datti ai,oya tafi anjima zansa a gyara sainakira kizo kinji” Ta girgiza kai tareda juyawa dan tafiya shikuma ya bude kofa ya shiga dakin.
Auta na ganin ya shiga tajuyo tana dariya,”ai wlh sainaga yanda dakin Uncle B yay datti,dama Amma tace dakinshi baya datti wai yanada tsafta, yau sainaga dattin dayayi ” tasa hannu ta bude dakin a ahankali ta shiga, ganin bataga datti a falon ba yasa tai dariya tareda kwafa, tayi hanyar bedroom dinshi tasa hannu ta bude kofan a hankali dan karyaji motsinta, ganin mace a kan gadon Uncle B bayanta a bude duk shaidan bulala dasukai wani iri ba kyan gani ga gashin kanta duksun barbasu akan gadon hakan yasa Auta tasaki ihu tareda kankame jikinta.
Da sauri B yafito daga bathroom yana kallon auta dake ihu, jikinta yahau rawa ganinshi rai abace,yana tsaye inda yake yace mata “zonan” kuka tasa sosai dan tasan yau saita gane kurenta, tafara sharban hawaye tana “yakuri Uncle B, wlh zan dinga jin magana, bazan karaba dan Allah karka daken”, fizgo hanunta yayi takara fasa ihu tana” kayakuri,plz-plz-plz!” tausayi tabashi sosai,hakan yasa yafasa dukanta yace “wuce kitafi kafin na bata miki rai” juyawa tayi ba musu tafara tafiya hartakai kofa tasake juyowa tana kallonshi yace “what?” tace “Uncle B batada lafiya ne?”Tai maganan tana nuna Rufaida dake kan gado, daga mata kai yayi shima tareda kallon Rufaida dako numfashin kirki batayi, Auta ta girgiza kai “Allah sarki,Uncle indan je intabata?” Ya dade yana nazarin ta kafin ya daga mata kai, da sauri auta taje gaban gadon ta tsugunna ta kama hannun Rufaida tana kuka ahankali saboda yanda taji tabata tausayi sosai tasake juyowa ta kalli B tace”Uncle B baka kaita asibiti ba,ciwonta nata jini,kaga yama bata zanin gadon,ka kira mata Dr Faruk,wlh ina sonta Uncle ” Barr yakaraso wurin shima ya tsugunna yakama dayan hanun Rufaida yarike sanan yace”banason nasake kiranshi dan banason kowa yagane tana gidanan, yau zan kaita wurin Mummy a Russia, za’a kaita asibiti achan” .
Yasake kallon Auta dake kallon Rufaida tana hawaye,tana hura iska akan ciwon yace “Auta”, tajuyo ta kallai yace” karki fadama Amma kinga Mara lafiya adakina, is our little secret kinji?” Tasa hannunta a harshe tareda fadin “I promise uncle “. ya shafa kanta tareda fadin “good Gurl, kinsan wheelchair din Daddy dayay amfani dashi lokacin da baida lafiya?” Ta girgiza kai da sauri tace “eh nasani,ai yanama cikin store dinmu nan Amma ta ajiye” yace “yauwa jeki dauko min” tafita da gudu kafin ta shigo yagama shiryawa, tana shigowa da wheelchair din ta ajiye tazo kusadashi ta tsaya tace “Uncle yanzu zaku tafi airport? ” yace “eh”, ta kalli Rufaida sanan ta kalleshi tace “but ai wanan kayan jikinta sun baci da blood, ka chanza mata wasu” yadan tabe fuska yace”auta Ni ban iya samata kayaba, abarta ahaka kawai intaje wurin Mommy tasa mata” yay maganan kaman wani Yaro ,auta tace “laaa nidai na iya, bari na dauko mata wayanan kayan dakasiyomin manyan nan, Wanda sukamin yawa”, kafin yay magana harta fita daga dakin da gudu ko minti biyu batayiba ta dawo dauke da wani Jan dogon sket da shimi baki very light, saidan karamin hijabi da bathroom slippers mai kyau baki shima.
Ta ajiye kayan kan gado Uncle B ya matso kusa da ita yace “auta keda Amma kesa miki kaya balle har ki iya sama wani?” Buga kafa tayi a kasa tace “ai wlh na iya,ni kawai dagamin ita ta zauna saina sa mata” yay kwafa tareda fadin “ok”, ya dawo kan gadon ya dago Rufaida ahankali ya zaunar da ita akan jikinshi yace “oya samata”, Auta ta tsaya agabansu tana kallon fuskarshi yace “what again?” Tace “to Uncle baka rufe idoba, ba Amma na tace babu kyau babban namiji ya kalli jikin wata ba…” bata karasa maganar ba ya kulle ido da sauri. Auta tasa hannu tacire shimin dake jikinta da, ta samata Wanda ta dauko,sanan tace “nagama saura sket” ya kwantar da ita duk idonshi arufe Auta tasamata sket,tasa mata karamin bakin hijab, da slippers sanan tace “to bude idonka kagani”ya bude ya kalleta yaga tamai kyau Sosai murmushi yayi ya daurata akan wheelchair Auta tarakosu har wurin mota yasata a ciki,ya shiga PA ya shiga ya jasu sai airport. Suna zuwa da sauri suka shiga jirgi,jirgi ya daga sai Russia.