Jikinta na rawa,kirjinta na bugawa da karfi saboda tsoro, juyawa tayi tafara tafiya da sauri duk ta rude tace “wlh ni banda kudin ka,banda kudin dazan biyaka”.
Barr Barraq ya lumshe ido, dan gabaki daya kanshi juyawa yake, jiri yakeji sosai,da kyar yadaga kanshi daga jikin glass din motar ya maida akan kujera.
ahankali yake kukkulle ido harya rufesu ruf.
Kaman ance takara waigowa,tanako waigawa taga hayakin dake tashi daga motar yafi nada ma, girgiza kanta tayi hawaye yadan zubo ahankali ta furta ” wlh bazan iyaba,baida lpy ai,naga jini a goshinshi” da gudu ta fanfala zuwa wurin motar, hannu tasa ta rike mabudar motar taja, sai taga motar yabude, ta tsugunna agaban motar tana kuka tace “kafito mubar nan, motarka na hayaki” sai taga ko motsi baiyiba, hanunta na rawa takai kan cinyarshi tadan girgiza shi tace “kaji, katashi motar ka na hayaki”,Ganin ko motsi batayi yasa tafashe da kuka tana kallon fukarshi,cikin kuka tace “mutuwa kayi?” Kara sautin kukan tayi tana girgiza kai “dan Allah karka mutu, kanada kirki kaji dan Allah”.
Goge Hawayen ta tayi ta kalli gabas,kudu,yamma da arewa kozata ga wani mahalukin dazai tayata fito dashi daga motar, amma bataga ko mutum daya ba, dayake kusan duka yan kauyen da safe suke zuwa rafi diban ruwa,basu zuwa da rana. Kifa kanta tayi akan cinyarshi takara kecewa da sabon kuka,kaman wacce aka tsikara ta tashi da gudu ta fanfala zuwa inda tulun ruwanta yafashe kozata samu ruwa a wurin, cikin ikon Allah taga wani dan bangaren tulun da akwai dan Karamin ruwa akanshi tsugunna wa tayi ta dauka ahankali ta juyo tana tafiya, koda tafito fili saitaga tsabagen hayaki bama ta ganin motar da kyau,hayakin yariga ya rufe motar, sauri takara batai wata wata ba ta shige cikin hayakin ta tsugunna tana laluban bakinshi da hannunta, taba lips dinshi yasa tagane bakinshi ne, tashi tsaye tayi da ruwan ta daga hannunta dake dauke da ruwan ta Kara ajikin lips dinshi tace “kasha dan Allah”,ta juye akan lips dinshi kadan ya shiga bakinshi sauran ruwan ya zuba a kirjinshi hakan yasa yaji sanyi ya saki numfashi tareda bude idonshi kadan “ahhhhhh” kokarin lumshe idonshi yake yasa ta kama fuskarshi da hanunta biyu ta girgiza shi “katashi dan Allah, kaji katashi motar na hayaki, mufita daga ciki”, bude idonshi yay da kyau saidai kash baya iya ganin mai wanan zazzakar muryar,gashi kanshi na masifar juyawa saboda buge kan dayayi sosai, ganin yanda ya tsareta da ido yasa tace “kaji” Hawaye ya gangaro daga idonta ta daura hannayenta akan nashi tace “ga hannuna ka rike mufita”kasa kama hannunta yayi kawai saita cire tsoro takama nashi tace “yauwa to tashi” taja hanunshi, da kyar ya iya tattaro karfinshi ya damke hanunta da karfi yatshi yafito daga motar. yakara rike hannayenta gam tana tafiya da baya da baya shikuma yana binta ahankali kanshi na juyawa jiri na dibarshi sosai.
Sunyi kusan taku ashirin(20) yana layi, adaidai lokacin motar ta kama da wuta, tsabagen tsoro ganin motar yakama da wuta yasa Rufaida tafara sauri tana janshi da sauri,mugun tuntube taci da dutse, dayake dabaya take tafiya tafadi akasa timm, batare dayasan maiya afkuba shima yaci tuntube da dutsen ya fada kanta dan ba ganin gabanshi yakeba.
Ihu tasaki da karfi” wayyo Allah na,ka dagani”.
Hadadden Hall ne cike da jama’a kowa yaci gayu,kida kawai kateshi kana ganin fuskokin mutanen wurin kasan suna cike da farin ciki banda mutane biyu, Muzzamil dayasha blue shadda ta bugu sai sheki take da Matar dazai aura Beeba. kwata kwata natsuwarshi baya tareda shi karkada kafa yake yana kallon agogon hanunshi. kakkyawan amaryan shi dake gefenshi itama cikin damuwa ta matso da bakinta saitin kunenshi tace “Honey wai har yanzu Uncle B bai isoba? gashifa 4 yayi” cike da damuwa Muzzamil yace “wlh nima ban saniba baby” tace ” to kodai wasa yakema sai gobe zaizo?”
Muzzamil ya girgiza kai”abu daya dana Sani game da abokina shine baya karya,baitaba karyaba, tunda yace yataso yataso dinne” amaryan tace”ok,Allah kawoshi lpy to” Muzzamil ya mike tsaye yace “baby bari naje nakira Dad just na sanar dashi”.
Zagawa bayan Hall din yayi inda ba kida sosai yaciro wayarshi yay dailing number Daddy Barraq, ringing daya Dad ya dauka,kafin yay magana Muzzamil yace”Daddy na damu wlh har yanzu Barraq bai isoba ” da sauri Dad yarufe newspaper hanunshi yace”Barraq din?,yanzu fa is 4,yaron da tun sassafe yamin salllama yatafi”,Muzzamil yace”Dad inata kiran wayarshi baya shiga,wlh nadamu” Dad yace “don’t worry Muzzamil it might be motarshi tasamu yar matsala a hanya ne, idan yakai har mangariba bai isoba just let me know,mubashi nan da 7’oclock ” Muzzamil ya numfasa yace”to Dad ” ya katse wayan yakoma Hall din badan ranshi yasoba.
*****
Da kyar ya iya Jan jikinshi ahankali ya sauka zuwa gefenta,numfashi ta sauke mai karfi tareda tashi tsaye tana kakkabe jikinta, ganin yana juye juye yasa ta tsayar da kakkabe jikin datakeyi ta kalleshi, kafin ta Ankara taga yafara Kwara amai a kwance ya rike cikinshi, warin petir din daya Shaka ya batamai ciki,tsugunnawa tayi a gefenshi a raunane tace “sannu” ya mugun galabaita daga kanshi yayi kawai dan jikinshi yay zafi, dankwalin kanta ta cire ta mikamai tace “gashi ka share rigan ka” hanunshi ya mika yana laluben abunda take bashi, Rufaida ta kalleshi muryanta na rawa sosai tace “baka ganine?” Kanshi yadaga mata ahankali, kuka yaci karfinta tsugunnawa tayi ta share mai aman daya bata gaban riganshi, sai bayan tagama cikin kuka tace “tashi muje gidanmu nabaka nabaka magani” da kyar ya iya mikewa yadan cije lebe tareda rike kanshi dayakeji kaman zai cire, sannu tace mishi sanan ta mika hanunta yana rawa tarike mai tafin hannu, wani dan yanayi taji ya ajikinta sanan tace “muje” ahankali yake daga kafa hanunshi daya na rike da kanshi, sundanyi tafiya kadan jin zaifadi yasa yace “sister zan huta” akasan wani bishiyan lema ta taimaka mai ya zauna,itama ta zauna kusa dashi jikinshi yay zafi radau, sanan tace “zaka iya tafiya yanzu?” Ya gyada kai sanan suka mike akalla sun bata kusan awa daya kafin sukai gida saboda suna tafiya yana hutawa,zazzabi sosai yakeji da ciwon kai banawasa ba.
Gidan suka shiga, hamdala tayi tadaga Duduwa bata gida bukkarta ta shigar dashi ta zaunar dashi akasa sanan tace “ina zuwa” fita tayi da gudu takoma tsohon dakin mamarta nada, tsofaffin kayan mamanta da labulaye ta kwaso dayawa ta shigo dakin tasame shi harya kwanta akasa shame-shame ya rike kanshi, shinfidasu tayi akasa ta daura wani akan wani saboda yadanji taushi tazo ta tsugunna agabanshi tadan tabashi ya bude idanunshi dasukai jajir tace “taso ka kwanta akan shimfida”,ta rike mishi hannu, tashi tsaye yayi da taimakon ta yadan kwanta akan shimfidar.
Ta Kara tsugunnawa tace”bari naje nasiyo ma magani kaji,kai bacci dan Allah duk Wanda kaji yay magana karka amsa kaji?ko Duduwa tai sallama karka amsa” Bai amsataba,tai fuskan tausayi tace “in sha Allah zaka warke kanada kirki” ta tashi da sauri tadau yar karaman jakan buhu taciro naira Darin da Baba yabata tafita daga dakin da gudu.
Gidan wata mata dake saida magani a kauyen taje,saidai matar batanan sai yayan ta yan mata guda uku da bazasu wuce sa’ointa ba.
Sallama tayi suka amsa suna mata kallon banza tace “abani maganin ciwon kai da zazzabi” tashi daya daga cikinsu tayi ta dauko mata wani kullin maganin gari guda biyu. Rufaida ta karba ta mika naira hamsin, yarinyar tana karba tace”jar ubanchan,lallai nema yarnan, dan kin rainamin hankali antaba saida maganin zazzabi da bauri naira hamsin?ko angaya miki na gadon ubankine?” Rufaida girgiza kai tace “wlh hamsin gareni,dan Allah kiyakuri wlh Mara lafiya zanba “sauran yayyin yarinyar biyu suka taso sukace “maiya faru lami”yarinyar tace “ba wanan jikar Duduwan bace wai magani naira dari taban hamsin” da sauri Rufaida tace “dan Allah kubini bashi wlh Mara lpy zanba” takarasa maganan da muryan tausayi, Babban yarsu tace “zaki kawo cikon kudin gobe, inba hakaba wlh saimun tareki abakin rafi mun miki dukan tsiya,mu daki kudinmu”. Rufaida tace “na yarda, tajuya tabar gidan da gudu tabiya shago tasai buredin ishirin sai madara cow bell ta goma da choco na goma sai sigan goma.
Ta shiga gidan hartana tuntube saboda sauri,har alokacin Duduwa bata dawoba,kofi ta dauka ta jika mishi garin maganin,sanan tadau wani kofi ta kada mishi tea da ruwan sanyi duk takai dakin sanan ta tasheshi, “ga magani kasha”, da kyar ya zauna ya jingina da bango daukan kofin maganin tayi takai bakinshi tace “bude bakinka” bude bakinshi yayi ta zubamai maganin, feso maganin yayi a fuskatta batare daya saniba ya yamuse fuska saboda wani azaban daci d bauri dayaji, ta share fuskan ta batare data damuba tace” kasha dan Allah” girgiza mata kai yayi. Tace” ga tea kasha” shima girgiza mata kai yayi ta tashi daga wurin takoma gefe tana kallon yanda yake mutsu mutsu. Kara dawowa kusa dashi tayi tarike mai hannu tafashe da kuka sosai, dudda cikin ciwo yake amma saiyaji kukan kaman na kurman yarinyar nan dayahadu da ita a Minna. Tace”Dan Allah ktashi kasha,kanka naciwo,wlh bazan iya inta kallonka kana ciwo ba kaji,kanada kirki Allah” wani iri yaji datana kuka ahankali yace “ban nasha”daukan magananin tayi tabashi da kyar yasha rabin kofi yana tabe baki sanan yakoma ya kwanta zama tayi a gefenshi tasa hannu tacire mai takalmin kafanshi sanan tadau mahici tana fifitashi ganin yana zufa.
Gafaradai mutan gida. Sallaman Duduwa yasa Rufaida tayar da maficin ta mike tsaye ta rike kirji Duduwa tadawo,arude tasa bakinta a kunnenshi tace “kakata tadawo dan Allah karkai magana taji kaji?” Tsigar jikinshi yatashi yarr, tashi tayi tafita daga bukkan ta rufo kofan ta tsaya a wurin tana kallon Duduwa dake kallon ta, “ina ruwan danace ki debo?” Rufaida takara makewa ajikin bango tana makyarkyata “Duduwa wlh tulun yafashe ahanya, ba laifina bane Allah bom… Duduwa ta daka mata tsawa ” ke! yimin shiru shegiya mai kama da ifiritu, wlh tunda kika fasamin tulu wlh saina fanshi abuna ajikin ki zaki gamu Dani,laifin ki biyu baki debo ruwa ba ga fasa Randa, bazaki zo nanba ina magana dake kina kallona da bakaken idonki” Rufaida tunkafin takai tafara matsar kwalla,Takai gaban Duduwa ta tsugunna “gani”, katuwar buhun danyar gyadar dake kanta ta jefa mata ajiki, Rufaida tasaki ihu mai karfi wanda yasa Barr Barraq tashi zaune da sauri, wai mafarki yakeyi,yanzu yakarajin muryan kurman yarinyar nan daya taimaka a Minna, itace? Kwanciya yayi da sauri saboda yanda kanshi yasara.
Rufaida tace “Duduwa kiyakuri bazan karaba” saida Duduwa taga tana zufa sanan ta janye buhun gyadan daga jikinta tace “dan ubanki tashi kije ki wankesu ki daura a wuta, inyayi zakikai dandali,sai bayan kin dawo zanci ubanki kuma wlh saikin biyani tuluna” ta sakar mata rankwashi aka,Rufaida ta share hawaye ta dauko langa ta juye gyadar ta wanke ta,taje ta hura wuta da kyar sanan ta daura akan wuta, kuka take acikin kitchen din tana Sosa jikinta rabonta da wanka kwana 5 kenan Duduwa tahanata jikinta kaikayi yakeyi sosai,kullum kaya daya take sawa salla ko saida da daddare tayi su duka aboye dan Duduwa bata barinta salla daga safe har dare aiki take bata zama hutawa ko sau daya arana.
Karfe bakwai Muzzamil yakara kiran Dad yace “Dad har yanzu bai isoba fa,nadamu wlh,nasan ba lafiya ba,Dad I can feel it”Dad yace ” me too Muzzamil, yanzu yaza ayi?” Yace”Dad zanbi hanya Nagani” Dad yace “ka sanar da police, in sha Allah inhar bakuga komiba very early gobe zan biyo flight” Muzzamil yace “to”tareda katse wayan. Daukan keys yayi yafita daga hotel din dashi da friends dinshi sukai lodging.
*****
Sai Wuraren mangariba tagama dafa gyadar, idanunta sunyi jaa saboda zafin hayaki, tsumma ta dauka tarike tukunyan zata juye gyadar a langa garin juyewa ruwan ya zuba a hannunta ihu tayi ta saki tukunyan a wurin ragowan gydar tazube akasa,da sauri Duduwa tafito daga daki tana sallallami “Allah yasa ba zubarmin da gyada mayyar nan tayiba” ta shigo kitchen din Rufaida dake kuka tarike hanunta tana ganin Duduwa takara rudewa tafara ja baya, bata ankaraba taji takara taka rushi a kafanta ihun dayafi nada tasaki zata gudu Duduwa ta damki hannunta”zonan ballagaza”iche ta dauka ta bubbuga mata ajiki “kika bararmin da gyada,kinsan da Yaya nasamu nasiyo gyadar nan akasuwa kuwa?” Rufaida tsabagen azaba tama kasa kuka sai ihu “bazan karaba Duduwa, yakuri bazan karaba, wayyo Umma na” saida Duduwa taga tana neman sumewa sanan ta ajiye ichen ta wurgota tsakar gida, ta kwashe gyadar kasan sanan ta fito tazuba gyadar a faranti ta daura gwangwani Kwara daya akai da fara leda tazo gaban bukkan da Rufaida ke kuka tace “dan ubanki tashi kuwuce dandali inba asiyaba komin dare kije har bakin titi ki tsaya sai ansiye tass sanan zaki dawo, kina jina?” Rufaida ta girgiza mata kai,Mari to koda mata tace “cemin to” Rufaida tace “to” tana kuka. Duduwa tasa hannu ta tunbuke dan kwalin kanta ta barbaza gashin kanta dake wari saboda rashin wankewa tace “ahanka zaki tafi saboda aga tsayin gashinki asiye gyadan duka”,ta daura mata farantin gyadar dakeda zafi akai tace “wuce kitafi, gwangwani daya naira goma ne” haka ta tafi,tana tafiya tana dingishi saboda konewar kafanta,tana tafiya tana girgiza hanunta dayay bororo saboda zafin kunar,garin ma yay duhu dan tuni akai sallan mangariba.
Dandali takai ta zauna a gefe guda,tana kuka ahankali babu Wanda yazo yasai gyadarta amma anata siyan na sauran dasuka kawo duk Wanda yazo gabanta saidai yace mata kazama suwuce ganin babu Wanda yasiya yasa ta roki yarinyar kusa da ita ta daura mata gyadar akai saboda hannunta dayay bororo,aiko ta daura mata haka tayi tafiya har takai asalin bakin titin garin tasamu guri kusada wani mai saida lemu da ayaba ta zauna, tai shiru tana kallon hannunta bororon yakara girma, kwalla ta share ta daga kai tana kallon motoci dake wucewa kan titi dare yayi amma batasan karfe nawaba yanzu,sanyi da isakan titin da wahalan dukan datasha yasa taji wani wahalallen bacci mai dadi yay gaba da ita a wurin. jin ana shafa cinyarta yasa tabude ido da sauri tareda Sosa kanta tana turo baki, “Ahha lallai jikar Duduwa nason abun jibi yanda take wani zumburo baki,alamun abun namata dadi ” da sauri ta daga kanta taga wasu matasa ne su biyu sai warin taba suke da sauri ta mike tsaye taja baya Ku rabu dani baruwan Ku dani , daya daga cikin samarin yace “baby ki kwantar da hankalin ki munsan abunda Duduwa ke miki, da zaran kin bari munyi bazamu Kara bari tabaki wahala ba,wanan gashi haka aiyau saimunyi gaskiya” turo baki tayi cike da tsiwa tace “Ku matsamin nadau gyada tani,bana magana da maza” samarin suka kalli juna sanan suka matsa mata zuwa tayi zatabi tsakiyar su tadau gyadarta bata ankaraba taji andaga sama sunyi cikin daji da ita iya karfinta take ihu amma kafin ta Ankara sun soma barka rigan jikinta, iya karfinta take ihu tana kururuwa hasken motan dasukaga ya haskosu tarr yasa suka saketa suka mike tsaye, itakuma ta tashi tsaye ta falla da bala’in gudu tafita daga dajin tana kuka da hasken farin wata ta kekketa bishiyoyin hanyar harta kawo cikin kauyen su tana kuka tashigo gida tana kuka. Duduwa ta haskota da tocula tafito daga dakinta tana gyara daurin zani, haskata tayi sama da kasa taga rigan jikinta dukya barke hartana ganin albarkatun kirjinta gashin kanta duk kasa yabata, kafanta kuwa dama ba silifas, bata damuba ta tabe baki tace” ina kudin gyadata?” Jikinta yafara rawa tace “Duduwa wasu suka dauken suka kaini cikin daji suna barkamin rigana”,Duduwa takara daure fuska “ina kudin gyadata nace?” Jikinta ya Kara rawa tace “Duduwa yabace gya..bata karasa maganar ba Duduwa ta turata tabugu da bango “wlh yau kashe kine bazanyiba a gidanan Rufaida”, Duduwa ta koda mata Mari tana jijigata ta bugata abango, Rufaida ahankali ta sulale a wurin sunamniya, Duduwa data haukace saboda ko gyadar ma bashi ta karbo akasuwa, ga yar iskan yarinyar nan ta batar, zuwa tayi ta dauko ruwa ta juye a jikinta ihu Rufaida tayi ta farfado,Duduwa ta shiga daki ta dauko wayar wuta “wlh saina kasheki” Rufaida lumshe ido tayi ta sadaqar mutuwa yau zatayi,zatabi Abba da Umma. saitaji maganar Baba yace “wlh wlh Duduwa inkika kashe yarinyar nan saimun dauko miki hukuma,da daddaren nan karfe 12 lokacin daya kamata yar yarinyar nan tana bacci shine zaki kasheta da duka?” Duduwa tace ” gafa munafukai an shigo” ta kalli Rufaida tai kwafa “zamu gamu da safe”. Tawuce dakinta tana masifa Baba ya daga Rufaida da take kuka ya shafa kanta yace” jeki kwanta Allah zai saka miki”,yabata toculan hanunshi yace “ga tocula ki haska” ta karba,da dingishi take tafiya tabude kofan bukkan ta shiga ciki ta mayar ta rufe tana kuka sosai, ga mamakin ta ganin Barr Barraq a tsaye tayi yana juye juye ahankali yace “Rufaida kece kika shigo? ban hanunki”hannunta mai lafiya tasaka a hanunshi tana kuka sosai,ya zauna itama ta zauna yama kasa magana saboda yanda ranshi ke zafi, mai wanan yar karaman yarinyar data taimakeshi tayi Duduwa ke dukanta haka? Mesa wasu mutane are just wicked? Jin kukan nata yaki tsayawa yasa yadaga hannu yana laluban kanta cikin sa’a yaji hanunshi cikin gashin kanta ahankali yace “ya isa Rufaida kidena kuka” takasa yin shiru saima Kara sautin kukan datayi tana sauke ajiyan zuciya, jin bazai iya daurewa ba,kukan na mugun tabashi yasa ya jawo kanta zuwa kirjinshi ya rungume tsam yana jijjigata.
Masu karatu ya za’ayi Barr Barraq yasamu eyeglasses dinshi?
Shin Muzzamil daya fita duba hanya zaiga Barr?
Wanan motar data haska yan shaye2 da Rufaida, motar waye? Kodai na Muzzamil ne?