Kafin Umma tabama Rufaida amsa takara jeho wata tambayar “Umma maisa naga duk sunsa gilas?Umma daga ina zukazo? “Tafadi maganar tana kallon fuskar Mum. Umma takasa magana tarasa maizata yi awanan gaban farin cikin ganin yarta,harta tunasu ko bakin cikin ta manta wayanda suka taimaketa, ciki harda abin kaunar ta,mijinta. Umma takara kecewa da kuka, Alh yay jarumtar yin magana ta hanyar kallon kanin nashi yace”Young malam meke faruwa? ?explain kasamu aduhu? Maisa ta manta mutanen dasuka taimaketa da mijinta?” Mutumin ya gyara zama yace”yaya amma Rufaida sammu ta manta iyayen ta gabaki daya,da rayuwar ta nada,ta shiga duniya kaman yanda kukaji tafada dazu, duk wani Rayuwa datayi bayan ta bar gidanku tayishi ne bata cikin asalin hankalin ta,tana cikin sammu,saisa ta manta su,amma zata tunasu nan bada jimawa ba,tashin ta yanzu taganine kaman daga bacci ta tashi,rayuwar datayi kaman mafarki ne,sai ahankali zata dinga tunasu kadan kadan,kubata lokaci zata warke duk zata tunaku,wanan bawata babbar matsala bace” Rufaida data kwantar da kanta ajikin Umma ahankali tace “maganar wa Baffa yakeyi Umma?” Umma tadan shafa kanta “zan fada miki anjima”. Sai alokacin Mum tai magana “nakasa gane dis whole thing,suyawe iyayen Rufaida dahar suka mutu?ita Duduwa data kira kanta kakar Rufaida who is she then??a ina suka san Rufaida?”. Dad yay gyaran murya” d only person dat can answer that question is Duduwa! Barraq cikin fushi yace”babu wacce zai kira matar nan gidanan, juyamin kwakwalwar mata sukayi ,dey did something to her” yakama kwalar malamin “mekama Rufaida?”kowa na falon ya mike tsaye Dad ya rike hannu Barraq “son let him go,ka sakeshi,ba abunda yama Daugther,I said let him go” da kyar Barraq ya sakeshi idanunshi sunyi ja Dad ya zaunar dashi yadawo yana bama malamin hakuri wanda ya nuna bakomi. Dad yakoma kan Barraq yana mai fada”nasha fadama idan rai ya baci kar hankali ya gushe,idan kai tunanin komi everything make sense zaiyu yaron Duduwa ya tsinci Rufaida ya dauketa saisa ma Duduwa hate her soo much,understand and get it once rayuwar da daugther tayi damu tayishi ne kaman amafarki,she will remember us amma ba yanzu ba” Barraq yay shiru ya daura kanshi akan cinyar shi,yarasa mezaiyi yaji dadi,zuciyarshi na mugun zafi,kanshi kaman an zuba garwashi” Karan wayar dayaji yasa ya dago kanshi ahankali suka hada ido da Rufaida harara ta balla mishi saboda taji haushin yanda ya shake baffan ta. Jin maganar Alh yasa kallon yakoma kanshi arude yace”garin yaya?ganinan dawowa,kuhadu ku kamata a kulle yanda bazata fitaba” ya katse wayar tashin hankali ya bayyanah karara a fuskarshi Umma ta fara tambaya “lafiya Alh?” Share gumin kanshi yayi yace “mai gadin gidan hajara(kishiyar Umma) yakirani wai Hajara ta haukace, tafito sai raye raye take tana cire kaya tana kiran Rufaida,ankasa kamata dole natafi Abuja yanzu” ya kalli Dad yace”Alh dan Allah inason keban cewa da yan uwana da Rufaida Alh” Dad ya washe baki “to ba matsala”. Yatashi Mum da Amma sukai gaba Barraq yaki matsawa daidai danan da chan Dad ya rike hanunshi suka fita daga dakin. Alh ya fuskanci yayan shi yace”yaya inaso ku saurare ni, munga Rufaida shine kuma abunda muketa addu’a akai ko?”Suka amsa da haka ne. “Amma da muka ganta mun tarar da ita a matsayin matar aure, kuma ga miji salihi mai taimako ga tausayi maikuma sonta”, tashi yayi ya matsa kusa da Umma dake kallonshi ya rike hanunta “abunda nake shirin fada nasan zaimiki wuyan yi, amma inaso ki duba mutuncin mutanen nan, dakuma abunda sukama yarmu na nuna mata so,kulawa,suka aurar da ita ga miji nagari” yadanja numfashi kafin yacigaba”Alhamdulillah mun godema Allah daya bayyana mana yarmu, dudda Rufaida bata tunasu ba bazaisa mutafi da itaba,bata karkashin mu yanzu,tana karkashin mijin ta, hukuncina shine zamu barta anan mutafi madinga zuwa dubata” yakarasa maganar yana kallon Umma dake hawaye. Ahankali ta girgiza mai kai,”na yarda da abunda kace na amince,bazamu taba karbar Rufaida daga hannun Barraq ba” ya kalli Yayan shi shima ya nuna amince warshi. Kowa na dakin ya nuna amincewar shi. Alamu Alh yay ma Umma da ido. Umma ta share hawayen ta tajuya ta kalli Rufaida tarike mata hannu tace”Baben Mama” Rufaida ta kalleta Umma tace”inaso ki zauna a gidanan da wayanan turawan zamuje gida Anty ki batada lpy zamu kaita asibiti kinji” Rufaida ta lankwasa kai”Uhm Uhm Umma nidai bazan zauna dasuba, bana sonsu banason gidan,inason naje school gobe tunda nariga nai latti yau ” Umma ta mikama Alh Rayyan dayay bacci ta juyo ta fuskanci Rufaida tace “Bebin mama inaso ki saurare ni kiji abunda zan fadan miki,…”Umma tafadin ma Rufaida komi,kan Rufaida yay chaji kalma daya kwakwalwar ta yafi rikewa “ke matar aure ce!matar Barraq!. Kanta ta chusa a cinya tafara rafka uban kuka bana wasaba, “wlh bazan yardaba,Allah bana sonshi, mutumin daya shake wuyan Baffa yanzu nan wlh bana sonshi,nibazan zaunaba, kuzan bi muje gidan mu”. Yayan Alh yatashi yazo gabanta yace”Rufaida! Ya daga mata tsawa,jikinta yafara rawa dantana mugun tsoron Baffa Yaya yacika fada,ga fushi.”idan naji kin kara cewa bakison Barraq saina karyaki,young Malam yace zaki tuna komi so dolenki ki zauna dasu,yanda kika zauna dasu da haka zaki zauna dasu yanzu,shashanci banza kawai, yanzu bamu da iko dake sai yanda mijinki yace, muba butulu bane da zamu goya miki baya ba,bazamu taba godema mutanen nan tahanyar tafiya dakeba kinajina” ta dagakai da sauri tana zaro ido. ya kalli mai gadi yace”kirasu mungama” mai gadi yafita dan kiransu. Maman Abd Shakur
Shigowa su Dad sukayi kowa yanemi wuri ya zauna Barraq idanunshi nakan Rufaida dayaga tana kuka sosai kaman yay magana saikuma yay shiru ya dukar da kanshi akasa. Alh yay gyaran murya yace “Alh zamutafi” da sauri Barraq ya dago kanshi ya kalli Alh. Alh ya sakinma Barraq tattausan murmushi kafin ya juya ga Dad yace”mun gode da kula da yarmu dakukayi da zaba mata miji nagari dakukayi nagode Alh. Babbar gaisuwata da fatan alheri gareka Barr Allah yakara daukaka ka yabaka zuri’a nagari, nagode da bama yata so da kulawa”. Barraq ya sadda kanshi kasa,Alh ya cigaba “ga Rufaida nan, in sha Allah zamu dinga zuwa dubata,Allah ya saka muku da alheri” ya juya ya kalli Rufaida yace “kima mijinki da iyayenki biyayya, inhar aka kawomin karanki saina saba miki kinajina ko?” Ta gyada kai tana share hawaye. Dad yay magana “bazaku tafi da ita tadan zauna daku ba?munsan kuna bukatar yarku itama haka,abun zai mata yawa ta warke kuma tacigaba da zama da wayanda batasani ba” Alh yay murmushi “tasan ku, saitana zama daku dinne ai zata tunaku,yanzu bata karkashin mu tana karkashin inuwar auren Barraq ne, haka Allah ya kaddara, mun gode kwarai,”ya kalli mum yace mun gode ma ya kalli Amma yace mun gode ma Umma da su Baffa suka goggode musu kafin kowa ya mike tsaye zasu tafi duk suka tashi Rufaida tarike zanin Umma tana kuka “ni wlh kidawo,banason gidanan,zan biku” Umma ta shafa kanta “banace zan dawo ba? kiyakuri kinji Baby na” Rufaida ta make kafada tana kuka. cikin Bacin Rai Baffa sarkin masifa ya daka mata tsawa “yimana shiru kafin nafasa bakinan,sake ta” bakinta tarike tana hawaye, Ya kalli Barraq yace”kaita daki tasha maganin ta tai bacci, bata gama warkewa ba bata bukatan all dis stress”. Ahankali Barraq yatako inda take ya mika mata hannu make kafada tayi da Baffa yamata wani mugun kallo batasan sanda tabashi ba tana tafiya ahankali suka fita daga dakin part dinshi yakaita yabude suka shiga. sukama su Alh sukabar gidan Dad dasu Amma suka dawo ciki kowa yana mamakin abunda yafaru yau. Suna shiga dakin ta fizge hanunta tana turo baki”kuma ni mutum yasake ni tunda dai ba hanunshi ya rike ba” Ta nemi kujera ta zauna ahankali tana cije lebe. Barraq baice komi ba saidan Murmushin dayayi aranshi yace so real Rufaida nada masifa O God save me!. Fita yayi daga dakin yatafi bangaren Amma yaganta tareda Mum yace”Mummy ina magungunan ta?” Mum ta dauko tabashi ya juya zai fita takirashi Son ya dawo “kabi Daugther ahankali, kayi hakuri dakome zatayi kaji, karka bata mata rai, kadaiga batada lpy anjima zan shigo naganta” ya juya yafita koda ya shiga dakin ya tarar da ita a zaune tadena sai kumbure kumburen datakeyi. ya dauko goran ruwan faro da maganin daya kamata tasha ya ballo ya mika mata “sha maganin ki Baby na”ta kalleshi ta ballamai harara “ni bazan shaba malam, kumani kabani kayan sawana zanyi wanka na chanza kayan nan” yadade tsaye yana kallon yanda take murguda mai baki. Tsugunnawa yayi agabanta yace”naji but plz take it and drink,baki da lafiya” “ance baza ashaba,wai ni dole ne wlh niba ruwana da mutum, wai mijina ne, aibani nace inaso ba, nigidan mu zaka kaini gobe ehe” tana karasa maganan tabi ta gefenshi tayi hanyar wata kofa data gani,tasa hannu ta bude tabi wurin takara ganin wani kofa ta bude taga bedroom takarasa shiga dakin tanemi bakin gado ta zauna da kyar. Ta sauke ajiyan zuciya tana shafa cikinta “wai meyasa cikina ke ciwo?wayyo zapi wlh” tafada araunane. zip din rigarta ta zage, ta cire rigar daga jikinta dan warin asibiti rigar yake mata wanda hakan keson yasata amai. Yarage daga ita sai sket da Bra, ta tashi tsaye tana kokarin zage zip din sket din taji an bude kofa an shigo ganin Barraq dauke da maganin ahannunshi yana wani irin kallonta yasa tafara neman rigarta dake kan gado. Barraq yamata kuri rabon dayaga jikinta harya manta. Sa hannu yayi ya tura kofar tarufu sanan yakara sa shigo wa dakin “wai mehaka?can’t u see dat am changing,kafita? ” Rufaida tafada a masifance, Barraq ya sakin mata murmushi tareda lankwasa kai alamun a’a kaman yanda takeyi. Daukar rigar tayi tasa agaban kirjinta tana nunashi da yatsa “wai kai baturen nan wani irin maye ne? ” saida takai bango sanan yasa hannu shi ta bayanta yahada ta da jikinshi, Rufaida ta rufe ido gam jikinta ko ina na rawa murmushi yasake yi aranshi yace”one character in common Rufaida den and now duk matsorata ne” duko da kanshi yayi yakai bakinshi saitin kunnenta yace”ni mayen Rufaida ne ” Rufaida ta sa hannu ta rufe kunnenta rigar tafadi akasa. Bude ido tayi suna hada ido tasake kulle idonta “let me go,wai mehaka,I hate dis stuff,plz let me go ” Barraq yasa hannu yakai wuyan ta yanama ta waiwayi zuwa kasa “only if u take ur drugs ” jin hannunshi nagab da kaiwa kirjinta ta rike hanun muryar ta na rawa sosai tace”to bani zansha “. Maman Abd Shakur
“”Plz Don’t kill him am begging yhu P.A, wlh inason Barraq sosai,plz! P.A. ya kalli Nana da jajayen idonshi “kowa na zaban Barraq kaina” ya girgiza kai “no I can’t take dis anymore, I can’t stand everyone choosing Barraq over me, nooo” yasa hannu ya daga Nana ya jefar da ita kan gado yasake daga karfen zai chakama Barraq Nana tai ihu daga kan gadon” shift to the left Barraq! Daidai lokacin da karfen ke sauka Barraq yadan matsa karfen ya yaga fatar gefen cikinshi sosai jini yafara bulbulowa, farar rigar dayasa ta batci da jini Nana tafashe da kuka tana ihu “u killed him PA ,ka kashemin Barraq dina, I hate yhu I hate yhu”. Sakin karfen P.A. yayi ya tsaya gaban Barraq ganin baya numfashi jini nabin bakinshi kanshi da cikinshi yasa yay murmushi. wandon shi dake kan gado ya dauka yasa yadau shirt dinshi yasa ya fizgo gashin Nana dake kuka sosai kan gado yakama less go,Nana ta fizge kanta “am not going anywhere, ka kasheni nima na bishi just kill me”. PA ya fashe da dariya yana cizan lebe hanunshi yasa ya matso kirjinta da karfi saida tai kara “ta yaya zan kasheki kinada abubuwan more rayuwa haka?bazan taba kashekiba kindawo sex machine dina,my prisoner”ya tura keyanta gaba tana kuka ya tusata cikin motar ta ya shiga yaja motar da gudu yabar anguwar gabaki daya. Ahankali Barraq ke lalube neman abunda zai daura akan ciwon saboda kar jininshi ya kare, kamo wani abu da baisan meba yadaiji taushi ya dunkule ya daura kan ciwon yana numfashi kadan-kadan Ahankali bakinshi ya furta Baby na…”. A firgice Rufaida ta farka daga baccin tana turo baki “ni ba Baby ka bane, mutum na baccin shi kana wani kiranshi ni “jin shiru yasa ta waiga bataga kowa adakin ba Amma ai taji muryan baturen nan yakirata. Gefen cikinta taji yana mata zafi sosai Bargon jikinta ta yaye ta kalli wurin taga jini,hannu tasa a wurin taga babu ciwo amma ga jini. Jin zuciyarta namata zafi da zugi kaman tai kuka gashi sai kawo mata bature yake yasa ta tashi tsaye. batabi takan batasa rigaba tadau hijabi tasa tafara bin dakuna tana budewa taga bashi fitowa daga part din gabaki daya tayi ta tafi part din dazu tana shiga taga Dad da Mummy da Amma, agogon dakin ta kalla taga biyar da rabi. Mum ta kalleta”Daughter na kin tashi?dazu na shigo kina bacci” Rufaida ta kallesu alamun damuwa karara a fuskarta tace”ina baturen nan?” Amma tace”dazu na ganshi dazai fita yacemin zaije ya kwaso miki kayane”. Rufaida tafashe da kuka”nidai ku kirashi ya dawo, inajin wani iri ajikina,duk inda yake he is not safe,nidai ku kira baturen”takara sa maganan tana kuka sosai. Dan tasamu kwanciyar hankali yasa Dad ya daga waya yakira Barraq sau uku ba a dagaba ajiye wayan yayi yace bai daukaba. Rufaida ta fashe da kuka Amma tace “halama yanzu meeting ya shiga ko wani uzuri”. Mum tai shiru tana kallon Rufaida itama tun dazu takejin wani iri kodai gaskiyan Rufaida ne he is not safe??something is wrong, definitely! Ta kalli Dad tace “Alh tura wani yabi bayanshi plz” Dad yace ok. Dukan sitairin mota Muzzammil yayi “damn dis holdup,haba dan Allah,Nigeria jaga -jaga komi suffer-suffer,am sick of dis country” cikin iko da yarda Allah yaga motoci sun fara tafiya yay maza yay gaba. Wuraren 6:00 yakara so gidan Nana dake water board. Ganin motar Barraq yasa yay murmushi “baiyi zuciya yatafi ba kenan, yana jirana”. paka motarshi yay da kyau yafito yacire necktie din wuyarshi ya wurga cikin motar ya rufe yay hanyar shiga gidan ahankali ya tura gate ya shiga cikin gidan. Ganin kofar sitting room abude yasa dan mamaki ya shigeshi gashi gidan shiru. Saka kafa yayi ya shiga falon ganin ba kowa a falon yasa yaji gabanshi yadan fadi ina Barraq??yaga motarshi awaje fa. Ganin kofar bedroom adan bude kadan yasa ya daga kafarshi dayaji yasoma sanyi yakai wurin, bai tura kofar ba ya tsaya abakin wurin ya bude murya yace”Guy are yhu in dere?” Yaji shiru he feels strange yarasa maisa, hannu yasa yakara sa tura kofar ahankali yakebin jini daya gani akasa kallo, hango Barraq dayayi warwas akasa yasa yakara sa ciki da gudu ya tsugunna agabanshi yasa hannaye biyu ya tallabo fuskar Barraq “who did dis to yhu Barraq ” where are ur eye glasses?”yafada yanamai waige waigen dakin hango gilashin afashe ya ruguje yasa ya kankame Barraq a jikinshi sosai yana kuka “who did dis to yhu Friend?” Barraq ya lashe lips dinshi dasuka bushe ahankali hawaye nabin gefen idonshi “take good care of Rufaida Muzzammil plz,katafi kabata maganin dare kaji,karka bari wani ya cutar min da Baby na, plz Muzzammil” yafadi maganan ahankali Muzzammil yarufe mai baki yana girgiza kai”stop talking as if u are going to die,yeah yeah yeah! I will take good care of Rufaida,amma kadena min magana kaman kana min wasiyya,zaka warke,but who did dis to yhu?” Barraq ya kara matse Hanun Muzzammil tareda rike inda ke jini acikin shi ahankali yay magana Muzzammil yakara kunenshi a bakinshi “DUDUWA! NANA!P.A! P.A! P.A!..” Muzzammil ya rufemai baki da sauri ganin cikinshi na bulbulo da jini,bakinshi ma Haka “keep quite Boo,u are bleeding, lemme call an ambulance” Barraq ya girgiza mai kai”I need water friend ” Muzzammil ya kwantar dashi ahankali yafita daga dakin neman ruwa fridge yaje ya dauko bottle water ya dawo dakin ya tsugunna ya taba jikin Barraq yaji sanyi baidamu ba ya dagoshi ya daurashi akan cinyanshi “B ga ruwan bude baki kasha ” yaji Barraq shiru yadan girgizashi “B” yasake jin shiru!.
Barraq yay murmushi okay! Ya mika mata maganin ta karba cikin sarkewan murya tace”ai sainasha ruwa zan iya sha” Barraq yakara murmushi ganin dukta rude ya mika mata ruwan goran hanunshi, tasha kafin ta runtse ido ta watsa maganin a bakinta ta hadiye takara shan ruwa da sauri sanan ta rufe goran ruwan. Tai shiru yamata wani baken baken yaki bari tawuce. Dago idanunta tayi taga ita yake kallo,da sauri ta juyar da kanta tareda folding hannayenta akan kirjinta tana kunkune “ni ni ni fa nagaji da kallon nan, ni mutum ma yabani hanya na wuce,sai wani kallona ake, to tubarkalla masha Allah, ni kambun baka baya kamani iyayena sun tofeni da li’ilafi”. Hannu Barraq yasa ya juyo da fuskarta ta fuskan ce shi,batai tsammani ba taji yahada bakinshi da nata tai kokarin kwacen kanta takasa, saida yay wasa da ita sosai sanan ya saketa tafashe da kuka tana bugamai rigarta, dariya yayi sosai kafin yasa hannu ya rike rigar “oya tashi kije kiyi wakan mutafi gidanmu yanda zamufi yin amarcin da kyau ko?”ya karashe maganan tareda kashe mata ido daya. Bakin ciki kaman ya kasheta cike da masifa tace”babu inda zani anan zanta zama na,kuma wlh ni saika kaini gidanmu,kuma saina hadaka da baban mu ince tabani kakeyi” Barraq ya zaro ido yana murmushi “Haba Baby na kullum fa haka mukeyi da,harda ma wanda yafi wanan,shine yanzu zaki fada, amiki dariya ace kina tona asirin mijinki” tafashe da kuka tadau bra daga kan gado daya cire mata ta bugamai abaya”ni karka sake cewa haka,bana komi da kai,ni banama sonka banason bature, basu da karfi, kuma basu da karfin kashi,kashin su gabaki daya biscuit bone ne,abu kadan ku karye,gasu da yawan yin ciwo,ragwaye ne ku woyii”tamai gwalo. “mune ragwaye Baby na?” ya taso zai kamata tajuya zata gudu cikinta yawani murda hakan yasa tai baya zata fadi Barraq ya rike ta da sauri “Baby na are yhu okay?” Rikeshi tayi da karfi tana cije lebe”auch!cikina ciwo” tafada ahankali tana shirin kuka “Barraq yace”sorry zan fadanma Dr”,hannunshi ya daura kan cikin nata yana shafawa ahankali tai lamo tanajin saukar dumin hanunshi acikin cikin nata, hakan yasa taji ciwon na raguwa kadan kadan. “I can’t forget lokacin dakika ce i luv yhu Uncle B” gyara kwanciya tayi a jikinshi ta kuramai ido “nina ce haka?”ta murguda mai baki”i dont luv yhu”ta lumshe ido ahaka bacci mai nauyi yay gaba da ita. Kwantar da ita yayi akan gadon “I luv yhu soo much”yay ma goshinta kiss yaja bargo ya lullubeta. Bayi ya shiga yay wanka a gurguje ya shirya yadau car keys dinshi yafita. Kwaso mata kayanta yayi a babbar akwati yasaka a boot sanan ya koma ya kulle gidan, ya shiga mota mai gadi yabude mai gate sanan ya dawo ya tsaya wurin glass din driver ganin hakan yasa Barraq ya kashe motar ya juyo yace”any problem Samaila?PA bai biyaka albashin ka bane? ” mai gadi ya girgiza kai “Barr yabiyamu,akwai abunda nakeson fadama” Barraq yafito daga motar yarufe”muko ma inuwa mufita daga rana” bayan sun zauna akan bencin mai gadi sanan mai gadi yafara magana “ranan da matarka tarasa baby ta akwai wani abu daya faru mai gidana” Barraq yabashi duka hankalin shi “bayan Jonathan yabar kakar matarka ta shiga gida, ninace bari naje shago na siyo garin rogo,koda nafita naji ankira salla saina tsaya a massallaci nai salla bayan na idar ne natafi shago na siyo garin kwaki,ina fitowa naga kakar matarka natafiya tana waige waige saichan naga wata katuwar jeep ta faka agaban ta ta dauketa ” cikin sauri Barraq yace “kasan wanda ke motar?wanda ya dauketa?” Mai gadi yace”Oga Nana nagani,Nana wanda lokacin kana zuwa dani office dinka take zuwa nemanka, ita nagani ta dauki matar,inata mamaki ya akayi Nana tasan kakar matarka saisa nace duk inna ganka zan fada maka”. Barraq ya mike tsaye yana huci”Thank yhu Samaila,zan ganka gobe “samaila ya washe baki yasan ganin alheri Barraq zaimai,Nagode yallabai Allah karemana kai,Allah ja zamaninka” Barraq ya shiga motar shi da sauri yaja da karfin tsiya ” tukin hauka yake kanshi yay chaji yanzu ina zaiga Nana?ina zai ganta? Tunani kadan yayi ya dauko wayarshi yay dailing number Muzzammil ringing biyu ya dauka “Hello Boo I need yhu,ka samen a gidan gonar Nana dake water board” Muzzamil yace”B Nana again? Maikuma yafaru?” “Just muhadu a wurin ina jiranka” Barraq ya daki sitarin motar dan gani yake baya sauri “bana forgiving abunda akama Rufaida,Nana ke kika turo aka kashemin Da, aka wahalar da matata” kara gudun motarshi yayi. Paka motarshi yayi a wajen gidan ganin motar Nana yasa ya tabbatar tana nan. Ya bude gate ya shiga. ahankali ya bude kofar dazai sadashi da falo ya shiga yana tafiya ahankali babu kowa a falo sai warin giya dake tashi dakuma bra da dan wando daya gani akan sofa, tsaki yayi yadaga kafa yacigaba da tafiya ganin wata kofa yasa ya daura hannu akan handle din zai bude jin numfashi da gurnani yasa ya tsaya yakasa kunne “Nana ki barni na shiga karna mutu,kin tayarmin da hankali ahhh plz”, muryan Nana yaji tace “saika fadan min cikin ya zube?dan Duduwa tace min ya zube Barraq ya tabbatar ma da hakan?” Barraq ya rike zuciyar shi da karfi dayaji P.A. yace”dazu da safe saida mukai waya dashi, yamace karnazo aiki,cikin ya zube zai kula da yarinyar kafin yay resuming, yanzu dai barni na shiga bayan haka komi kikeso zanyi koda zuwa dauko miki Duduwa ne daga gujungu”. Barraq baisan lokacin dayasa kafa ya daki kofar ta bude ba,wani tsalle yayi yahau gadon ya shako wuyar P.A. yafara duka yana jijjigashi “hw could yhu?”ya daki cikinshi,ya shakemai wuya gam P.A. yafara kakarin mutuwa. Nana data nemo zani ta daura tazo tarike Barraq “B let him go,ka sakeshi”jin muryar Nana hallittar dayafi tsana a duniya yasa hankalin shi yakara gushewa hankada P.A. yay akasa ya juyo ya kwashe Nana dawani gigitacchen mari. Ya rufeta da duka yana ball da ita tana ihu. Ahankali Barraq yaji saukar abunda baisan takamaiman me ba akanshi,yaji abu nabin kanshi wanda yakasa gane jini ne ko ruwa?. juyowa yayi dan damkar P.A. yaji an fizge gilashin idonshi an yar. Duhu ya bayyanah a ganinshi. PA ya daga dogon karfen mai tsinin baki yakara bugama Barraq akai, take Barraq yaji jiri na dibanshi amma yaki barin kanshi yakai kasa,ya rike guiwarshi yana tofar da jini daga bakinshi, P.A. ya daga kafa yay ball da kafar Barraq, Barraq yay kara ya zube akasa yafara tabe tabe yana neman gilashin idonshi. PA ya take hannun Barraq dayaga yana gab da tabo gilashin, yasa dayar kafanshi yay ball da gilashin glass din yafashe. PA yay dariya mai kara”I’ve always hate yhu Barraq,ban taba sonka for a single minute ba,am jealous of yhu,kullum ni kenan ka maidani mutum mara amfani,mai aiki a karkashin ka,mai kwasoma takardu yasama amota,mai biyan workers dinka”. Ya ciji lebe” I hate u Barraq,u killed my future,saisa duk wani abu dazai cutar dakai nakeyi amma tunda yanzu kaga noni I will just take ur life”. ya daga karfen ya saita tsinin akan cikin Barraq, hanunshi ya daga zai chakama Barraq aciki. Ahankali Barraq ya saki kara,Nana ta saki ihu noooooo! Why PA?I love him,I always do,why???” hannunshi ya daura akan kirjin shi yaji zuciyar shi bata bugawa ta tsaya chak “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un ” Muzzammil yafara Marin fuskarshi yana kuka “am dreaming, mafarki nake katashi daga mafarkin” daura kanshi yayi akan kirjin Barraq ya girgizashi “Noooooo!karka tafi ka barni plz, kadawo Barraq kadawo” daga jikinshi yayi daga na Barraq ya cire rigar jikinshi ya rufe fuskar Barraq dashi. Ya zauna a wurin ya tankwashe kafa yana kuka sosai banawasa ba. Karan wayarshi data dameshi ya dauka ganin Daddy Barraq yasa yay picking kafin yay magana Dad yayi”son kana tareda abokin naka ne, Rufaida nata kuka wai taji ajikinta he is not safe,kuna tare ne kabani shi muyi magana??” Muzzammil ya share hawayen idonshi muryar shi na rawa yace “Dad kabar inda suke zan fadama wani abune ” Dad ya kalli Rufaida dake kallonshi da Mum yamusu M urmushin yaki kafin yafito daga dakin da sauri yace”menene Muzzammil tell me?is Barraq okay?” Muzzammil yakasa rike kukan dake neman kwacemai yafashe da Kuka sosai “Dad yace “Muzzammil is everything okay?where is Barraq? ” Muzzammil yace”Daddy u have to come to No 37 water Board area, gidan Nana” Arude Dad yace”meke faruwa Muzzammil? ni namiji ne I can take and handle it,tell me” Muzzammil yace”Daddy just come,they’ve killed him, they’ve killed Barraq, Dad sun kashemin abokina Barraq is Dead Daddy…” ahankali wayar dake hanun Daddy ta sulale tafadi akasa tartsatsatsas!”
Ahankali yadaga kafa ya juya ganin Mum tsaye abayanshi hawaye na kwarara a fuskarta yasa ya kakalo murmushi ya sakar mata yazo zaibi ta gabanta ya wuce tarike hanunshi”dont hide anything, maiya sami Son?I know something is wrong I can feel it here”ta nuna mishi zuciyarta tana kuka sosai. Dad ya rungume ta yana shafa bayanta ahankali yace”Adama kisan Allah shike hallito bawa yakuma dauke abinshi idan yaso ko? “Ta girgiza kai tare da rike kirjinta “karkiji tsoro,ki dake kikuma yarda da kaddara,Barraq ya rasu! “Amma da karaso warta kenan wajen tace”what! Mum ta rike rigan Dad gam tai kasa zata fadi Dad ya riketa da sauri yana lallashin ta, Amma tafashe da kuka tazo ta kama hannun Mum tana kuka. Mum ta kalli Amma “wasa yake dena kuka Maman Auta dena kinji”. Dad da idanunshi yay ja yace”Amma take her inside ki dau Rufaida ki kaita part din Barraq banason tasan komi,batada lapiya kar ciwonta ya dawo sabo,bari naje mutaho dashi”. Dad yay hanyar gate yay magana damai gadi maigadi ya dafe kanshi kafin ya bude gate din da sauri Dad ya shiga katuwar jeep yaja yafita mai gadi yarufe gate da sauri yafita ya shiga mota suka tafi tare da Dad. Dad yana tuki yana kiran mutane da yan uwanshi saida ya biya yadau imam din anguwar su da wayansu mutane dasukayi mota guda dan ansan Barrister Barraq ko ina. Ahankali Imam ya tura kofar bedroom din gidan Nana dan tunda suka shiga gidan Dad jikinshi yay sanyi idanunshi sukai jajir sukai zuru zuru. hango Muzzamil zaune gaban Barraq da fuskarshi ke alullube duk jini yasa Dad ya rike zuciyar shi Muzzammil ya dago jajayen idanunshi ya kalli su Dad ciki harda Dadinshi da sauri yatashi ya rungume Dadinshi yasaki Kuka. Kafin yasaki dadin shi ya rungume Dadin Barraq yana kuka sosai. Dad ya shafa bayanshi Muzzammil ya sakeshi ya koma gefe. Dad ya karaso ya tsugunna yasa guiwowin shi akasa yakai hanun damanshi ya yaye rigar Muzzammil dake kan fuskarshi, ganin Fuskar Barraq dinshi ya bayyana yasa ya daga hannu ya kulle bakinshi yana kokarin hana kukan dake neman zuwan mishi ganin gawan danshi agaban shi. Ahankali ya dukar da kanshi ya sumbaci goshin Barraq yamai addu’a ya lumshe idonshi yana tunanin randa Barraq yacemai I luv yhu Daddy a restaurant din wajen asibiti. Wani mugun kuka ya kufcemai. Daddy ya girgiza kai “Barraq noo, u can’t die! Barraq kai kadaine dana namiji ku biyu gareni,narasa grandson dina,banason rasaka yanzu dan Allah kadawo”Baban Muzzammil ya kama kafadarshi ya murza alamun ya yakuri Dad ya juyo ya kalli Muzzammil cikin dishahshiyar muryarshi yace “waya mishi haka?waya kashemin da?” Imam ya girgiza kai “wanan za yishi anjima, yanada kyau akai gawa makwancinta da wuri mutafi” ya daga Dad ahankali. Yayinda mai gadi ya kawo pakaceciyan tabarma Imam Daddy da Dadin muzzammil suka daga Barraq suka sashi aciki aka nannade shi suka daukoshi aka fito dashi aka sashi a dogon bus din da Dadin muzzammil yazo dashi. Duk aka shishiga mota aka kama hanyar zuwa gida dan yimishi sutura. Alokacin gari yasoma duhu dan mangariba ta wuce amma isha bai riga yayiba. Rufaida dake zaune akan gado Amma a gefenta idanunta yay jajir tadai daure takiyin kuka dan kar Rufaida ta gane wani abu. Zumbur Rufaida ta mike ta rike zuciyar ta gam tana hawaye Amma ta tambaya “menene “Rufaida ta fashe da kuka sosai “bakin ciki nakeji sosai azuciyata, jinake kaman zan mutu,wlh bature kawai nakeson gani. Inajin alamun shi araina,kaman yana cikin gidanan yanzu,naji kamshin turaren shi”. Ahankali Amma ta zaunar da ita “zauna Rufaida, nanda anjima zai dawo meeting ya tsareshi”ta share hawayen ta”are yhu sure?” Amma ta gyada mata kai. Zaunawa Rufaida tayi shiru Amma ta tashi cikin dabara tadan bude labulen window hango maza an cika gidansu ga su dad sun dauko abu a tabarma ya tabbatar mata Barraq ne kasa rike hawayen ta tayi da sauri ta gogesu ta saki labulen ta kalli Rufaida datai tagume gwanin ban tausayi tace”bari naje nakawo miki abinci,ki jirani karki fito” tafita daga dakin da sauri batare data jira amsan Rufaida ba. Minti 30 da fitar Amma Rufaida ta tashi ta bude kofa ganin maza an cika ko ina a gidan wasu na kuka yasa jikinta yafara rawa taji wani irin motsi acikinta kaman na yaro, ganin wani dan tsoho na kuka agefe yasa Rufaida taje wajenshi “Baba meke faruwa? ” “yarinya mutumin daya taimake ni arayuwa yabani jari,yarana mata uku sun tashi aure Banda komi ya dauken mun nauyinsu,yamusu komi na daki yabiya kudi akama matata aikin cancer a nono datake dashi,shine yarasu,wasu mugaye suka kasheshi”. Rufaida ta rike cikinta gam ta tsugunna a wurin “Baba ya sunanshi menene kamanininshi?” Tsohon ya sharce majina “Barraq!Rufaida ta zaro ido dan taji dazu abbanta yakira baturen nan da Barraq. Ahankali Muryarta na rawa tace”Baba bature ne? ” Baba ya girgiza kai “eh jini biyu ne dai”Mamar shi yar rasha(Russia)babanshi dan Nigeria”. Rufaida ta tsala wani irin uban ihu tafashe da kuka tai hanyar part din Daddy yanda maza suka cika wajen yasa tajuyo takoma dakinsu tana kuka wardrobe ta bude taga suit baki daukowa tayi tasa ta daure wandon da dankwali saboda yamata yawa tasa necktie, rasa yanda zatayi da uban gashin ta yasa ta dauko wani facing cap data gani tasa ta dunkule gashin aciki tana kuka sosai”wlh saina ganka, saina kutsa cikin mazanan na ganka,dan Allah karka mutu” kara rike cikinta tayi dataga yakara motsi ta tashi da kyar tafito. Koda takaraso wurin taga an lullube abu da fararen kaya ansa amakara jiri tafara gani batasan lokacin data shiga cikin dandazon mazan nan ta dinga kutsawa har saida ta taba makarar ta rike gam tana kuka. Muzzammil dake hawaye ya juyo dan yaga me bugeshi garin kokarin kama makara. Ana saka makarar a mota Rufaida tariga kowa fadawa ciki ta chusa kanta a cinya tana kuka. Tadaiji mota natafiya wanda hakan yasa ta dago kanta ta kalli kowa Daddy kadai ta gane acikin mutanen Motar. Kuka tasake fashewa dashi sabo kafin ta zabura saboda motsin dataji cikinta nayi ta rike cikin gam tana kuka cikeda ihu tace”kadena min ciwo,wlh saina raka bature gidan gaskiya,inason shi,Allah ya jikan mijina ” kowa na motar ya zabura yana kallon mutumin da akaji da muryar mace, Dad yakai hannu ya cire hular gashin ta ya zuba akafada atare Dad da Muzzammil sukace “Rufaida! Kuka tasake fashewa dashi tana wani irin haki kaman zata mutu, ganin kowa na motar take biyu biyu ta hade hannayeta da kyar ta iya magana “Dad dan Allah karka koran zan bishi ne, idan kace a’a zan mut…”bata karasa maganan ba idanunta suka fara juyawa wani irin mugun jiri ya kwasheta ta sulale kwance a wurin hannunta daya ya sauka akan farin kyallen da Barraq ke ciki”. Dad yay salati Muzzammil yaza. ..” Muzzammil yace”Daddy look” ganin farin kyalle na motsi sosai yasa sauran mutanen cikin motar suka fara neman wurin guduwa. “Daddy budeshi, doguwar suma ce,he is alive! Maman Abd Shakur
Muzzammil yataya Dad suka ciroshi Dad ya warware kyallen jikinshi. Ahankali Baban muzzammil ya paka mota agefen titi sauran motoci da machina dake binsu abaya duk suka paka suna mamakin maiya tsayar da motar daya dauko gawa.
Daddin Muzzammil ya bude mota ya fito,Imam ma yafito suka zagayo baya,Muzzammil ya bude musu da sauri hawaye na kwarara a idonshi ahankali yace “Daddy da ranshi doguwar suma yayi,mutafi asibiti kawai” Dadin muzzammil yakai dubanshi ga Dadin Barraq dayasa Barraq a kirji yana hawaye sosai ahankali Barraq ya furta “Boo water,I need water” Dad ya dago kanshi da sauri yace”Muzzammil bamu ruwa ” kafin kace kwabo mutanen da suka zageye motar kowa yafara gudun nemo ruwa a shagunan dake kan hanya. Wani bawan Allah yasamu aka dinga pasin pasin goran ruwan faro saboda yanda jamaa suka taru har ya iso cikin motan muzzammil ya karba ya bude yabama Dad,Dad ya saka abakin Barraq da sauri yafara sha rabi na zuba akasa, Dadin Muzzammil ya gyara mai bakinshi ajikin ruwan yadan sha dadan yawa sanan Dad ya cire goran a bakinshi. ahankali Dad yace “mutafi asibitin”. Da kyar jama’a suka matsa ma Dadin Muzzammil da Imam suka fito suka shiga mota akaja, yayinda Muzzammil ya rufe kofa. Jama’a anata al’ajabin al amarin wato daguwar suma yayi. Aka koma mota wasu suka bisu wasu kuma suka juya gida tareda fatan Allah bashi lafiya. Karfe 10:30 P.M. suka isa Baban asibitin garin Abuja mai suna “Handsome Shakur Specialist Hospital” kwararun likita suka karbi Barraq da Rufaida da gaggawa. Anata yima Dad gaisuwar Allah bashi lpy mutane na tafiya. Muzzammil yasamu yadan kebe ya ciro wayarshi ganin kusan 35miss calls din Hafsat yasa yakirata da sauri yay mata bayanin abunda yafaru. labarin ya girgizata Muzzammil yace duk dare zai dawo tanuna mai bakomi,ya kula da abokinshi zuwa gobe yazo ya dauketa yakaita ta dubasu sukai sallama suka katse wayan. Yana gama wayan kiran Mum ya shigo wayarshi da sauri ya dauka Mum da muryarta ya dishe sosai tace”Muzzammil neman Daugther muke bamu ganta ba,kuyi sauri ku dawo” Muzzammil yay murmushi dimple dinshi suka bayyana “Mum kira Daddy danshi yakamata ya baki goodnews dinan” ya katse wayan yayi dailing number wani abokinshi ishak babban police ne,daya rike matsayin DpO yamai bayanin komi,DPO yace”gobe da safe zasuzo idan lokacin Barraq zai iya magana dole suyi magana dashi dan yamusu bayanin maiya kaishi gidan Nana,da sauran vital informations. Muzzammil yay godiya ya katse wayan tareda komawa cikin asibitin. Maman Abd Shakur
Suna fitowa suka tarar da Amma da Muzzammil da Auta dake zaune kusa dashi yana lallashinta. Dad ya zauna Amma ta tambayeshi ya jikin murmushi ya sakar mata “cikin nanan bai zube ba,nakusa zama grandpa”.
Farin ciki ya lullube fuskarta. Mum ta zauna gefen Amma tace”any news akan son ?”Amma ta girgiza kai “har yanzu Dr bai fito yamana bayanin komi ba”. Mum ta rike kuncinta tana sauke ajiyan zuciya damuwa ya bayyana akan fuskarta. Amma ta dafa kafadarta “Hey!don’t worry,Barraq is a fighter zai warware,komi zai koma normal kaman da I promise” Mum ta daura hanunta akan na Amma ta lumshe ido”thank yhu Amma,tashi muje mu duba daugther” suka mike atare Mum ta bude dakin da Rufaida ke ciki suka shiga har alokacin tana bacci ana kara mata ruwa. Suka zazzauna. Dad ya dauko waya ya kira iyayen Rufaida ya sanar dasu komi daya faru bayan tafiyar su salati Alh yayi ya sanar da ubangiji yace”Allah yabashi lpy, in sha Allah zamuzo gobe mu dubasu”. Dad yace”no need kaida kakeda maras lafiya” Alh ya sauke ajiyar zuciyar yace”Akwai abunda ban fadama ba jiya bayan mun dawo,cikin haukar ta ta sanar mana ita tama Rufaida asiri ta manta damu ta shiga duniya, she’s paying for wot she did,baruwana da haukan ta ramin muguntar data hakane tafada ciki nida Umman Rufaida zamuzo gobe, Allah kara musu lafiya yasa kaffara ne ” Dad yace”Ameen”. Dad ya kalli Muzzammil yace”son kaje gida mana Daugther na nemanka ” Muzzammil ya girgiza kai “sai B yatashi zan tafi, Dad ina sapayan gilashin shi? ” Dad yadanyi shiru “baida wani sapayan gilass ,normally a eye clinic dinshi na India idan gilashin sukai expire yaje biyu suke bashi,so lokacin dayay hatsarin nan a kauyen Duduwa da bikin ka har gilas dinshi ya kone na tahomai da sapayan yasa,yanzu dole mu fitar dashi a duba idon achan kafin sumai gilashin dayay suiting idon a yanzu, but dat will be bayan ya warke ” Muzzammil ya sauke ajiyan zuciya “Allah sa muji alkhairi” Dad ya amsa da “Ameen “. Suna zaune a wurin DPO da wasu polisawa guda uku suka shigo Muzzammil na hangoshi ya tashi ya shigo dasu inda suke ya kalli Dad yace”Dad nakira sune saboda na fadin musu abunda Barraq yafada min da iya abinda nasani,dan duk wanda yayma Barraq abunan saina kulleshi” DPO ya mikama Dad hannu suka gaisa kafin su zazzauna. Ahankali Muzzammil yamusu bayanin komi tun lokacin dayake office Barraq ya kirashi, harya iso yaga Barraq cikin jini da abunda yafadan mishi. Dad yay mamaki yace”Nana?Nana dai dana sani? ” Muzzammil yace”Eh ita Dad” Dad yay shairu. DPO yay rubuce Rubuce kafin ya kalli Muzzammil da Dad yace”kiran sunayen mutanen nan uku da Barraq yayi acikin jini makes dem our suspects, PA,Duduwa da Nana. Cus muna bama irin maganan nan amfani sosai,but still zamu so ji daga bakin Barraq idan ya tashi. And zamu nemo Nana,Duduwa PA dan interrogating dinsu,zamu tafi yanzu zamu iya dawowa any time dan yimuku tambayoyi idan mun shiga duhu akan binciken”. Ya tashi yamika ma Dad da Muzzammil hannu suka gaisa. Muzzammil ya taka musu zuwa wajen asibiti suka shiga mitarsu,kafin ya dawo ciki ya zauna kusa da Dad. Wuraren 12 na rana likita yafito daga dakin da aka shigar da Barraq, saida ya wanke hannu da fuska sanan ya zo wirinsu yace”congratulations sir,Barraq is safe and sound,mutum daya kadai zai iya zuwa ganinshi for now,saidai patient din nata kiran sunan Rufaida Rufaida sometimes yace”Baby na I suggest akai mai me sunan ya ganta gaskiya” Dad ya washe baki yacema Dr “thank yhu sosai”, Dr yay murmushi yace “Sir akaima patient dina abunda yaketa kira plz”,Muzzammil yace”Sure,yanzu ma kuwa”. Maman Abd Shakur
Karfe 6 na safe taima Mum da Amma harda Auta da fuskarta tai suntum ya kumbura saboda kuka a asibiti. Duk suna zaune Dad ya dauki Auta dake kuka yana lallashin ta wata likita tafito daga wani hadadden Daki. Tana sanye da farin coat data daura akan riga da wandon dake jikinta,hannayeta sanye da hand gloves,tasanya iD dinta a wuyanta da aka rubutu sunanta ajiki “Dr Rukayya Sadau”. Takaraso ta tsaya agaban su Dad tace”Ina iyayen Patient Rufaida? ” Dad ya mike da sauri tace”ku biyoni office ” Dad da Mum sukabi bayanta. Ta zauna su Dad suka zauna bude file din Rufaida tayi tana yan dube dube da karance karance. Kafin ta kalli Dad tace”Sir jiya kace bata dade dayin bari ba da ina tambayarka akanta?” Dad ya gyada kai “yes tai bari 2 days ago” “an mata wankin ciki ne bayan tai barin?” Dad ya girgiza kai”no,Doctor yace cikin yariga yafita basai anyiba, kawai mu dinga bata abinci mai kara jini ajiki da magungunan daya bamu” Dr Rookey Sadau tadanyi rubutu acikin file din kafin ta dago kanta ta kalli su Dad murmushi Kwance akan fuskarta tace”Cikin bai fita ba,sun tsayar da jinin da wuri,maybe saboda yanda tai bleeding din yasa basu gane da wuri cikin nanan ba,but cikin yarku nanan for now inhar zakubi kaidodin dazan baku ” Dad yama kasa magana saboda farin ciki Mum ce tai magana “menene kaidodin?” Dr Rookey tace”ku hanata daga any object ko abu mai nauyi,sanan any exercise irinsu tsalle-tsalle,guje-guje da dirke-dirke tadena yi saboda suna kawo zuban jini hakanan ko zubar ciki ma. zaku kiyaye abubuwan cinta tana yawan cin abinci mai kara jini sanan ta guji abinci mai siga sai shawarwarin dazan baku shine Mai ciki ta dinga yawan cin wake saboda yana karama yaron cikinta kaifin kwakwalwa sanan yana bama maiciki ruwan Nono sosai. Shan kankana yana gyara fatar yaro acikin ciki,kuma yana karama yaro kaifin kwakwalwa. Cin ganyen irinsu ugu da alayyahu yana kara jini ajikinsu,Sanan alokacin da mace keda ciki wanda ke yawan sata amai tadinga cin kwakwa (coconuts)da rake(sugar cane) yana rage yawan amai. And suna hana yaro ya dinga kurjaren zafi, wutar dare and d rest bayan an haifeshi,kuma suna rage ciwon nakuda. Cin dabino(Dates) strengthen the muscles of the uterus akarshen watan haihuwa. Kuma Yawan cin dabino yanasa mace ta bude ta cikin sauki batare da an karata ba a lokacin haihuwa. Cin dabino ga mai ciki dama wacce ta haihu yana karama ruwan Mama elements din da ake bukata na karama yaro lafiya da kariya daga kowace irin cuta. Sanan sai shawarwarin kula da yanayi (mood)din datake ciki. Yanada kyau mai ciki ta kasance cikin farin ciki kowani lokaci,ta kalli abu mai kyau,taji abu mai kyau,ta sha abu mai kyau,ta shaki kamshin abu mai kyau. Dan ko wani hali mai ciki ke ciki haka dan cikin ta ke ciki. Yanada kyau mai ciki ta nisanci bakin ciki ko bacin rai,sanan kartaji haucin kowa kota tsani wani abu,ko ta dinga bakin ciki dawani. Dan duk hali /yanayin damai ciki ke ciki yana affecting yaron cikin ta. Ta kalli Mum tace” Ma ko film din ban tsoro baaso mai ciki na kallo inhar suna bata tsoro irinsu vampires films,Horror films and d rest duk bai kamata ba. (It is important to have good feelings,good thoughts, and not to carry grudges,have fear of something or be unduly worried about something. A pregnant woman should remain calm,happy and should not be allowed to be over concerned and allow herself to be overtaken by grief. The thoughts you generate within urself will affect the kind of disposition the child will have. If u are sad and miserable the child will be equally affected. REMEMBER! it is the mother’s womb that is carrying the baby and that the baby is affected by whatever she is thinking, feeling, reading and listening to. It is better and advisable for a pregnant woman to keep a good company, to read good books. Example The Holy Qur’an.) likita tace “zaku iya tafiya sai jibi zamu sallameta dan 16prime ce,we need to monitor her” Dad da Mum sukai godiya suka fita. NOTE:Duk abunda nafada akan mai ciki yakama ta tayi hakane,gaskiya ne,Allah sa wasu su amfanu da my little ilimi, Ameen. Maman Abd Shakur
Dr Rookie Dad yay ma bayanin komi babu bata lokaci tasa nurses suka gungura Rufaida zuwa dakin da Barraq yake batare da anbar su Dad sun shiga dakin ba.
Da kyar Barraq ya furta “My Rufaida kece?”Jin motsin dayayi a dakin Dr Rookie tai murmushi takama hanun Rufaida ta saka a cikin hanunshi tace”ga Ruffy dinka anan,bacci take,karkai magana da yawa cus of ur condition,take care” tajuya ta mayar musu da kofa tafita. ahankali Barraq ya murza hanunta tareda lumshe ido “get well soon Baby na,naso zan iya ganinki yanzu”yakai hanunta kan bakinshi ya sumbaci hanun ahaka bacci yay gaba da shi.
Washe gari akabar Su Dad suka shiga ganinsu har alokacin bata tashiba sai Barraq da idonshi biyu Mum ta rungume shi gam tana kuka Auta ma haka da kyar sukai shiru. Dr yabama Dad takardar transfer zuwa India saboda yimai gilash.
Karfe 12:Am na Rana Rufaida ta farka ahankali ta tashi zaune daga gadon da kyar tana yatmutse fuska. Kallon dakin tafara bataga kowaba,daga hanunta dazatayi da zumar sosa fuska taji kaman an riketa, da sauri ta juyo ganin Baturen da tasan ance yamutu yasa taji kanta yafara juyawa yayinda zuciyarta ke tashi tanajin wani irin amai na taso mata, bata ankara ba tafara kwara amai da bakomi ciki sai ruwa yellow Mum dake zaune wajen dakin tana karanta jarida ta ajiye a gefe ta shigo dakin da sauri ganin Rufaida na amai yasa takoma waje da gudu takira Dr. Dr da Nurses suka biyo bayan Mum aka shigo dakin daura Rufaida sukayi akan gado suka fita da ita zuwa dakinta. Barraq yace Mum maiya sami Rufaida? ?ta rike hanunshi Son karka damu amai ne kawai.
**********
Bayan sati biyu.
Zaune Rufaida take a falon Amma ta tasa dan wake agabanta tana kallo takasa ci ko kadan. Ta rame sosai tayi wani irin haske. Kirjin da baya ne kawai acike dam. Amma ta zauna kusa da ita tace”Rufaida kefa kika daman na miki dan wake kuma kin kici,ko kinfiso sai Auta ta dawo daga makaranta ta tasaki agaba tana kuka kafin kici?kin manta fadan da Umman ki da Abbanki suka miki jiyako?” Rufaida ta girgiza kai tana share hawaye “Amma ni bature nakeson gani,kunce yana raye amma ni ban ganshi ba,tun randa na ganshi a mafarki harna dinga Amai ban kara ganinshi ba” Amma tai murmushi “oya ci koda kadanne nabaki albishir mai dadi kiji” tadan kalli Amma,Amma ta gyada mata “trust me,I promise zakiji dadin news din,amma kifara ci dan rabonki da abinci tun jiya da daddare da Auta ta tasaki agaba kikaci yam balls,so kike bebin cikin ki ya rame? ” Rufaida ta girgiza kai tareda sa hannu aciki plate din tafara ci ahankali har taci rabin plate sanan ta kalli Amma nakoshi. Amma ta shafa kanta kafin ta mika mata maganin rana tasha da kyar sanan tace “Amma fadamin?” Amma tai murmushi “dazu kina bacci Dadin Auta yakira yace min yau zasu dawo dashi da Muzzammil da Barraq dinki ita kuma Mum zata wuce Russia dan tanada case a chan ana nemanta” cikin murna Rufaida ta rike hanun Amma tace”Amma wanan baturen shine Barraq ko,shine zai dawo? ” Amma ta gyada mata kai tana murmushi, murmushi Rufaida tasake yi tareda chusa kanta tana murmushi Amma tai dariya oya tashi ki dauko hijabin ki na kaikai Zee Hamza saloon wata yar katsina amiki gyaran jiki dana gashi da kunshi.
Karfe 5:00 na yamma suka dawo Rufaida sai sheki take fuskar nan tai kyau. Amma ta kaita part din Barraq tahada mata ruwan turare tai wanka dashi. Amma tace bari naje na duba abincin da Fauzeeya(yar aiki)ta hada. Ta wuce tafita. Rufaida tai wanka tafito ta zauna a gaban madubi tana kallon lallin da akamata dake burgeta. Ahankali tasake mikewa ta dauko wata katuwar handbag ta juye akan gado tana murmushi “Umma na nagode da kayan kwalliyan da kika kawomin” kwalliya tayi sosai tai kyau sanan tasake dauko katuwar jakar da Umma ta kawo mata taciro wani bakin 3quarter wando wanda da kadan ya wuce guiwa da Jan shimi armless anmai kwalliya da fulawowi bakake,saka kayan tayi ta chusa shimi cikin wandon (zanzaro)tadau wani kacha da yazo tare da wandon a matsayin belt ta zura ta kulle tareda sakinshi yabi gefen hip dinta ya kwanta. Zama tayi agaban madubi ta zira jan dan kunne karami yana walkina kaman Diamond tadau wani hair clip jajaye masu suffan kananun fulawowi ta jerasu agaban gashinta abin yay mata kyau sosai takara dawowa yarinya sak. murmushi tadan saki ta kalli madubin tai mai fari”toni kai madubi mena kallona?,ai dai ban cema inason bature ba “ta murguda baki”am just soo excited yau bature zai dawo” tasa tafukan hanunta ta rufe fuskarta “to uhm, uhm ai jiya da Umma tazo tace nadinga gayu,nai gayu sosai randa bature zai dawo” da sauri ta mike tsaye”laaa turare na da Umma tace nasa duk randa zai dawo” da sauri tasake bude jakar ta dauko wani dan karamin kwallba ta bude ta tsiyaya turare a hanunta ta murza ta shafe jikinta dashi tareda lumshe ido jin wani sassanyar kamshi na shiga jikinta. Jin ana kiran sallan mangari ba yasa ta shimfida dadduma tai salla takara gaggyara dakin ta wuce falo ta kwanta akan kujera tana kallon “Love is timeless” ko minti sha biyar batayi da fara kallon ba Bacci yay gaba da ita.
Suna fitowa daga bangaren ya kalleta ya shafo kanta”Auta na ki koma daki kije kiyi karatu, ba kince min gobe kunada exam ba?”Auta tadan zumburo baki “but Uncle B i missed yhu saisa nakeson na bika na kwana a part dinku” da kyar Barraq ya hadiye yawun daya taru a bakinshi yadan zaro ido”Okay Okay Auta naji amma yanzu kifara komawa part dinku revise ur book very well anjima saina zo mutafi ki kwana tareda mu “murmushi ya bayyana akan fuskar Auta tasaki Uncle B tajuya tace”to zanyi karatun sosai yanda bazan manta bako?” Barraq ya gyada kai good gurl tajuya takoma part dinsu. Yayinda Barraq yay murmushi yaja trolley hanunshi zuwa part dinshi. Ahankali ya bude kofar dakin wani sanyayyen ni’imantaccen kamshi ya ziyarci hancinta. Ya lumshe ido ya bude.
Maman Abd Shakur
Kafin ya daga kafa ya shiga falon ya maida kofa ya rufe. ware ido yayi hango abu mafi soyuwa agareshi kwance tana bacci cikin kwanciyan hankali. Karasa wa gaban kujeran yayi ya tsugunna yana kallon ta shimin ya zazzago yanda ta kwanta hakan yabashi daman ganin abunda yafiso gani, lumshe ido yayi da sauri jin wani irin shock nabin jinin shi. Ahankali yasa hannu ya shafa lallan dayaga an mata a hannu dan ya mugun burgeshi ga fatar ta yakara taushi ya daura hannu akan cikinta ya lumshe ido” My Baby Allah rayamin kai,baka taba gaisawa da Baban ka bako?”Yadan bude ido kadan “don’t worry yau dole na gaisa dakai” Ahankali ya dukar da bakinshi yakai saitin kunnen ta “My Rufaida ur Husby is back” turo baki tayi cikin barci takara muskuta wa cikin bacci. Barraq yakai ganinshi wurin abun dake kara tadamai hankali. Hanunta yadan daddaka ahankali”Baby na Baby na ” bude ido tayi kadan ta kalleshi ganin bature tsugunne agabanta yakara haske gashin kanshi ya kara kwanciya ga sabon farin gilashin da akamai yafi nada kyau da karbanshi yasa takarasa bude ido gabaki daya ta kalleshi murmushi ya sakar mata “tashi nine nadawo” tashi tayi zaune idanunta suka ciko da kwalla tana kallonshi “kaine ko yauma mafarki nakeyi?” Barraq yay murmushi “nine mintsile ni kiji” ya mike tsaye itama ta tashi takai hannu ta taba fuskarshi taji ta taba fuska kuka ya kufce mata Barraq ya bude hannu tafada kirjinshi tana kuka sosai,ya kwantar da kanshi a kan gashinta yana shakan kamshin dake neman sa hankalin shi ya gushe dago kanta tayi daga jikinshi ta zame jikinta daga nashi ta juya taji Barraq ya rike mata hannu”ina zaki? ” idanunta alumshe cikin karamar murya tace”fitsari nakeji sosai” saki ta yayi tajuya tana tafiyan ta mai daukan hankali daya kara birkita Barraq harta shiga bayin ya sauke ajiyan xuciya yafada kan kujera yana rage kayan jikinshi.
Koda tafito daga bayin ta tsaya tai salla issha ta cire hijabin jikinta ta linke ta ajiye ta dawo falon daga shi saidan farin boxer ta ganshi ya rike glass cup zuma aciki cike yana sha yayinda dayan hanunshi ke dauke da remote yana kallon News. Baisan da shigowar taba yadaiji alamun ana kallonshi hakan yasa ya juyo da kanshi karaf idanunsu suka hadu da sauri ta juya tana yarfe hannu bakinta na rawa tace”na..uhm. .na. .kawoma ab…abinci?ya..ya jikin ka..?” Murmushi ya danyi ya ajiye kofin zumar akan kujera ya tashi batai tsammani ba taji an rungumeta ta baya jikinta yafara bari “am okay banajin yunwa “ke kinci abincin?”ta gyada mai kai tana kokarin tureshi kara matseta yayi kafin ya juyo da ita yahada bakinshi da nata yana tsotsa da zafi zafi.
Kuka Rufaida tasaki sosai ta tureshi “ka sakeni,me kakemin,banaso” Barraq ya girgiza mata kai,muryarshi adishe yace”No” Fuuu tajuya ta shiga cikin daki ta bugo kofa Barraq yakoma kan kujera ya zauna yakara sa shanye zuman shi ya kashe kallon ya kashe wutar daki yatafi bedroom a kwance ya ganta tana dandanna waya ko kallo bai ishetaba wutar dakin ya kashe kafin ya kwanta akan gadon yay shiru chan kuma ya tashi yafita daga dakin da sauri ya koma falo ya kwanta akasa flat ganin hakan yaki taimakonshi yasa yafara sit up.
Kunna wuta dataji anyi yasa ya tsayar da sit up din dayakeyi ya juyo yaga Rufaida ce sanye da farin kayan bacci shara shara iya guiwa. yacigaba da abunda yakeyi. Ahankali tazo kusa dashi ta zauna bai kalleta ba hakan yasa ta murguda baki “kai Baturen nan maina barina ni kadaai adaki kasan bana iya bacci ni kadai ko?” Yadan kalli yanda take turo baki aranshi yace”tasha kuka da rashin lpy dabana nan, amma yanzu jibeta ta ganni tafaramin tsiwan dis new Rufaida en… kwanciya tayi akan kafanshi “wlh bazaka sakeyin wanan abun ba,inama ma magana kayi banza dani ko?” Barraq ya murguda mata baki,da sauri ta tashi ta zauna ta ware ido tana kallonshi “laaa ka iya murguda baki dama? kai baturen nan kai tamace ne? ” bai kulataba sai rungumeta tsam dayayi a jikinshi yafara aikamata da sakonni masu zafi, data nemi kwace kanta takasa. Ahankali ya rada mata a kunne”Amarci da new Rufaida zan fara yau”.