Ahankali ya zame hannunshi daga nata dayaga yana rawa yace “barshi zan zuba da kaina” da sauri ta mike tsaye zata fita daga dakin yace “amm nace ba” tadan juyo ta kalli center Capet din dake kasar dakin jikinta na rawa. yace”idan aka wanke miki gashin amiki kitso kinji” dagamai kai tayi, tafita daga dakin da sauri hartana tuntube. girgiza kai kawai yayi yanzu shine keson wanan yarinyar,lallai soyayya bakama Barraq adalci ba.
Tana komawa part dinsu tawuce dakinta ta kwanta akan gado tanamaida numfashin tsoro. kai mutumin nan yacika bata tsoro, to maisa lokacin dabaida glass banji tsoron shiba?take ma kanta tambaya a zuci.
Da yamma Mum tasa aka kaita wurin wanke gashi, wanke mata gashin sosai akayi aka mata kitso irin na turawa nan kaman kalaba tai kyau sosai banbancin ta da turawa fari kawai zasu nuna mata dan itabaka ce.
Zaune take a dakin Mum tagama yima Mum gyaran daki duk tai zufa Mum ta shigo tace”daughter kije kima son sallama,yau zai koma Nigeria ” da sauri Rufaida ta kalli Mum saikuma ta maida kanta kasa, Mum ta dauko wani magazine dake kan drower ta zauna kan gadon tana Karantawa. Ahankali ta mike tabar dakin. dakinta taje tasako karamin bakin hijab dinta akan riga da slet din kantin dake jikinta ja,tayi part dinshi, bude kofan tayi ta shiga jikinta na rawa ta tsugunna a kasa ta chusa kanta cikin cinya batare data kalli wani abu na falon ba.
“Zan koma Nigeria yau,kina bukatan wani abu?” Sassanyar muryarshi ya bugi kunnenta, Kanta akasa ta girgiza, yace”are u sure?”ta sake dagamai kai batare data kalleshi ba. Ahankali yace “Rufaida” tadago kanta taga sun hada ido da sauri ta kauda kai dudda yamata kyau sosai yau,yana sanye da suit mai ruwan toka,da neck tie mai gida gida,gashin kanshi yakara yawa gashi ya kwanta. maganarshi ta tsinkaya yana fadin”yau lesson teacher zai fara zuwa yana miki lesson just to keep u busy,and dan kituna abunda kika sani abaya, meanwhile innakai Nigeria zan nema miki certificate da testimonial na primary school, sai na JSSE,zan saki a school a garinnan, inaso kifara daga Ss1,dazaran nadawo zaki fara school kinjiko Rufaida” ta dagamai kai, yadan kalleta kafin ya dauko wayarshi daga kan table yana daddannawa yace”lastly banasonki da wasa,banason na ganki da any friends, be very very serious da karatun ki,dan banason Wanda bayason karatu,ki zama mai kokari da kwazo banda yawan wasa,and ki kasance mace mai kamun kai, da sitirce kanki,karkice dan kinga yanda yan garin ke shiga da aladarsu kice zaki dauka banaso,banason yawan surutu, take good care of ur self Rufaida, kafin na dawo naga kin iya duk abunda lesson teacher ki ya koyamiki,and I also want u to be social, kidinga zama tareda Mummy kina koyan abubuwan datake yi kinji da yanda take interacting da mutane?” Ta girgiza mai kai hawaye na zuba daga idonta, ya mike tsaye yana kallonta kafin yace “zan tafi”.
Ahankali itama ta mike tana share hawayen datake yi amma sun kasa daina zubowa, yadau yar karaman jakarshi yay hanyar fita, ya daura hanunshi kan door handle yaji kukanta yakara karuwa sama danada,juyowa yayi yana kallonta da sauri ta juyamai baya tana kuka, “kidena kuka Rufaida in sha Allah bazan dadeba,nasan Ni kadai kika sani, but karki damu Mummy zata kula dake more than yanda zan kula dake, karki manta abubuwan Dana fada miki,ga dakina nabar miki akwai wasu abu Dana ajiye miki a bedroom kije ki dauka,saina dawo Bye”. yajuya yafita daga dakin Rufaida takara fashewa da kuka, ahankali ta furta ” KAINE SIRRI NA Mai Gilashi, Allah ya kaika lpy”.
Saida tagama cin kukan ta sanan ta shiga dakin tadake tsammani shine bedroom din,hadadden dakine an mai fenti Golden Brown, babu wani tarkace banda wardrobe na bango sai kuma katon table da computer kekai, gefeshi kuma wani farin karamin fishbowl ne da kifaye yan kanana aciki. Hango Babban akwati akan gado yasa takarasa wajen,ta bude akwatin. kayane na sawa kala kala, sai Novel na turenci guda uku, dawani littafi mai suna ” Educative Lady Behavior” ahankali ta mayar da komi ta kulle akwatin tana kallon dakin kafin taja akawatin tabar dakin, taje ta nunama Mum kayan.
Mum ta dinga murna tana shima Barraq Albarka.
Aranan karfe biyu lesson teacher yazo sai biyar yatafi. Hankalin Rufaida yatashi dan bata gane komiba Maths da Biology yamata ita turencin shima ne bata ganewa, tadau littafin ta dinga Karantawa, ganin taki ganewa yasa tai salla biyu na nafila taroki ubangiji yasa ta dinga ganewa. Cikin ikon Allah washegari dayazo yay mata English tadan gane ba laifi ahaka ahaka ajin yacigaba da tafiya harna tsawon wata biyu Wanda a yanzu Rufaida na gane komi daidai gwargwado, akwaita da kwazon ganin ta iya abu. Tana yawan zama da lidiya a kitchen tana koyan girkin da akeyi, gata da gyara jikinta koda yaushe tsaf tsaf take saisa Mum ke alfahari da ita. Tanajin dadin zama da Rufaida har cikin ranta, dan akwaita da girmama na gaba da ita gata da son aiki, kiri-kiri tahana masu gyarama Mum daki gyarawa,ita keyi da kanta, idan washing machine ya wanke kayan Mum ita kezuwa ta shanya idan sun bushe ta kwaso ta gogesu,Mum tai magana tadenayi akwai masuyi har tagaji ta kyale Rufaida dan taki denawa. aganin Rufaida tahakanne kadai zata saka musu abunda suka mata,sun haskaka rayuwarta sun mayar da ita mutum bayan rasuwar su Umma, sun tsamota daga wahalar Duduwa, sun kuma sota,sun nuna mata kauna tomeza tamusu daya wuce kyautatawa da musu biyayya??..
Rufaida kenan akwaita da tunanin manya wani zubin.
Zaune yake a office shida Muzammil. “Muzzamil wlh nakosa nagama abubuwan gabana natafi Russia, dan nasa Rufaida a school, gashi Dad kullum damuna yake da aure,saisa dukna kosa nabar Nigeria gaba day…a” Wayarshi yay ringing kallon wayan yayi yaga baisan number ba, ya share ganin ansake kira yasa Muzzamil ya kalleshi “pick d call mana,it might be important” yadau wayan ya kara a kunne tareda amsa sallaman dayaji an mishi a natse, Alhaji yace”dafatan ka ganeni Barrister ,Wanda yataba kawoma complain kan yarshi tabata,da sauri Barr ya rike kanshi kwata-kwata yamanta da alkawarin dayama mutanen nan zai nemo musu yarinyar su, baimasan inda paper dasuka rubutamai yanda yarsu take yakeba. Da kyar Barr yace” Alhaji am very sorry wlh aiyuka sunmin yawa,but gobe munada wani meeting na Barristoci a Lagos zanbi nyt flight cus meeting is around 8 nasafe,so idan mun gama by 1 zanzo wajenka mu tattauna da kyau kan yarka, ban address din wurinku ” nan Alhaji yabashi address dinshi sukai sallama.
Muzammil ya kalleshi yace “maisa zakaje gidanshi?” Barr yace “yakamata naje,dannai bincike,kuma kasan dole daga gidansu bincike zaifara,anan ne zan iya gathering all d necessary clues”. Muzammil yace” hakane fa” suka cigaba da fira.
Zaune take a garden ita kadai tasa jumpsuit ja,yay mata kyau gashinta dayasha gyara a sake sun zubo har bayanta,littatafan assignment na gabanta. da alumu tai zurfi cikin tunani dan hankalin ta baya kan book din. Jitayi an dafata, afirgice tajuyo ganin Mum ne yasa tai murmushi tace”Mummy”Mum ta zauna a gefenta tarike hanunta cike da damuwa tace” daughter dis days kina yawan tunani meke damunki tell me d truth ” Rufaida tai shiru kaman bazatayi magana ba, saida ta sauke ajiyan zuciya sanan kwalla yacika idonta tace”Mummy nima bansani ba,tun shekaran jiya nai mafarkin wata mata fara kakkyawa nada cikin 9 month,naga tana rashin lpy sosai,hawan jini yakamata,she is really suffering kuma tanata kiran sunana waini take nema,nine sanadin ciwon ta”, takarasa maganan tana kuka sosai. Mum ta rungume ta tana bubbuga bayanta tace “is ok, kidena tsoro is just mafarki,be prayerful kinji” ta dago kanta daga jikin Mum tana murmushi tana share hawayen.
Juyawa tayi tadau littafin gabanta ta bude ta mikama Mum tace” take a look at this Mummy ” Mum ta karba, ihun murna tasaki tareda mikewa tsaye tace “who Drew dis daughter?” Cike da Murna tace”is me,Nina zanaki Mum dazu” Mum ta kalli drawing din sosai,taga exactly fuskarta ne, ta kalli Rufaida tace”dama kin iya Zane haka? ” Rufaida tadanyi tsallen murna tace “Mum nima kawai naga hannuna nata zanaki,ni bansan yanayi ba”, Mum ta kalli drawing din taga dan karamin signature na zanen baby(jariri) tace” Rufaida wanan signature fa?”Maisa kikai signature na Zane?” Tayi dan dariya tace”Mummy wlh bansani ba,nadaiji da ina zanen kaman ina son baby,kawai sainaga na zana small baby as my signature ” Mum ta tafa mata very good daughter, zan siyo miki abubuwan drawing saiki dinga yi,kin fito da sabon samfarin signature. Rufaida tai ihu ta rungume Mum.
Karfe 2 na rana taima Barr Barraq a kofar gidan Alhaji Muhammad. Da kanshi Alhaji yamai iso zuwa Babban falonshi inda aka wadata gaban Barr da kayan ciye-ciye da shaye-shaye.
Bayan wani dan lokacin gaisuwa da labarta bayan rabuwa, Barr Barraq ya kalli Alh da matarshi dayagani da katon ciki haihuwa yau ko gobe yace” nazo nan gidanne cus inaso nahada all d necessary abubuwan daya kamata nasani kan yarku”. Yabude jakan laptop din jikinshi ya zaro wata zungureriyar takarda ya kalli Hj,yace”I will start with u Ma, cus kece uwa,u know ur daughter morthan anybody so inaso kibani labarin yarki takowani bangare”.
Hj ta sauke ajiyan zuciya kafin tafara magana””nidai sunana Maryam Muhammad yar fulanin yolace,mun dade dayin aure bayan kusan shekara 12 dayin auren mu Allah ya azurtamu da yarmu tafarko mai suna “Rufaida” sunar kakarta taci saisa Dani da babanta muke kiranta da “MEEMA”. Barr ya kalli yanayinta yadanyi rubutu kadan kafin ya dago kanshi yace ” cigaba ma” tace” Rufaida ko kuma ince Meema yarinya ce shiru shiru,ko kadan Meema batada fada,batada karfi kona digi,tun tana karama bata iya shiga cikin sa’ointa suyi wasa,cus dukanta ake, har wanda Meema ta girma ma saiya daki Meema kaga tana kuka batare data iya ramawa ba,wanan dibi’an Meema na rashin karfin fada na damuna gata da yawan kuka,abu kadan kesata kuka,gata da yawan tsoro. Haka nacigaba da kula da ita muna nuna mata so da kulawa,nida babanta mune kawayenta,dan bata iya shiga cikin yara, dazaran tadawo daga makaranta tana tareda mu adaki,ahaka Meema takai shekara 14 batareda Kawa ko dayaba, hartafara abun namu namata Wanda yazo mata da gardama tanada ciwon Mara sosai, dan akwai lokacin da muka kaita asibiti akace mumata aure, babanta bai dau maganar komiba dan aganinshi yarinya yar 14 zaima aure? Aibata isaba, haka muka dawo gida muna kulawa da ita. Har babanta yakara aure “Salameme” wacce itace mutum ta farko danasan batasan Meema kullum saita daki Meema,saidai inbata gantaba,ban taba mata magana akan tadena dukan Meema ba dannima banason hayaniya.
Bana mantawa da watarana Meema na 15 ta shigo dakina tana kuka nace mata menene tacemin Anty(salameme) tace mata wai watarana saitasa ta manta da mamarta da babanta ya zamto batasan kowaba,ta manta mu a duniya, maganar ta dami Rufaida tanata cemin yanzu Amma wai zan iya mantaki a duniya keda Abba?. Nace mata karki damu bazaki taba mantamuba Salameme wasa take miki,da kyar na lallabata tai shiru nabar dakinta nakoma dakina ina tunanin maisa zata fadama Meema irin maganar nan, ina zaune a wurin naga Meema ta shigo dakina da murnar ta tana rike dawasu cardboard paper farare guda biyu ta shinfidasu agabana naga sak zanena Dana Baban ta ne, na tambayeta me dalilinta na zanamu tace toba Anty tace zan mantaku ba,kinga tunda nazanaku ai bazan taba mantaku ba,kallon zanen nayi ina dariya sainaga tayi signature da zanen baby Dana tambayeta dalili saitace min… Kuka yaci karfinta, Alh ya shafa bayanta yana fadin ya isa kuka baida kyau agareki yanzu. Da kyar tai shiru tace”Dana tambayeta dalili saitace min”Amma inaso ki haifamin kanwa ko kani,halan idan ina amfani da signature na baby ki haifamin baby ” dariya kawai nayi ina mamakin yarintar Meema, tundaga lokacin babanta ya bude mata wani Babban daki a gidanan inda take Zane zanen ta. Barr Barraq yace “zan iya ganin dakin?” Suka kaishi har dakin Zane kala kala duk Wanda tayi saitadan zana karamin baby akasa,bayan yagama rubuce Rubuce suka dawo falo. Barr ya kalli Alh yace”sir banda ciwon Mara batada wani ciwo? Maybe Aljanu haka or something else kaga sai muyi tunanin ko sune suka dauketa??” Alh ya girgiza kai,gaskiya Rufaida batada wani ciwo sai na Mara,Wanda nasan duk inda take yanzu tana wahala da ciwon. Barr yasake wurgo wani tambayar “dayar matar kafa” Alh yace “tunda naga tadami uwar gidan na chanza mata gida,naraba su”.
Barr Barraq yay rubuce-rubuce ya maida paper cikin jaka kafin ya dago kai ya kallesu yace”Alh, Umma banason nabaku much hope,even though bansan adininmu sosai ba,but d little I know daga abokina Muzammil shine duk Wanda ya dogara ga Allah,to Allah ya isar masa,watakila wanan itace jaraba warku,Ni ban isa na nemo muku Rufaida ba,saida yardar Allah,haka wayau na ko wayanku bazaisa a gantaba” ya kalli Amma yace”Umma have faith, trust in Allah,ki yarda shikadai zai iya bayyana miki yarinyar ki, ki kwantar da hankalin ki ki sauka lpy,in sha Allah za’aga yarku. I will try my best na nemota,da gobe zanyi tafiya but nadaga tafiyan sai next month”.
Ya mike tsaye tareda daukar jakanshi yace”nabarku lpy” Alh da Umma sukamai godiya da shatara na arziki duk bai karbaba haka yatafi suna mai yabon kyawawan dabi’un Barr Barraq.
Zaune yake adakinshi yadan kishingida da gado yana zukar tabarshi, kayan bacci ne a jikinshi dan bai dade da shigowa ba yay wanka yay salla. Jin knocking din da’ake yi a sitting room yasa ya mike tsaye ya bude kofar dazata sadashi da sitting room, Wurgar da karan taban hanunshi yay akan tiles yasa kafa yatake kafin yakara sa wurin kofar ya bude Daddy ya shigo dakin sanye da farar jallabiya ya zauna akan kujerar zaman mutum daya yahade rai, ahankali Barr ya maida kofan yarufe yakaraso tsakiyar dakin ya zauna akan kujera kanshi akasa yace “Good evening Daddy “,Dad bai amsashi ba cikeda bacin rai ya kalli Barr da kanshi akasa yace” Mummy ka tafada ma sakona” Barr ya girgiza kai tareda furta”eh Daddy tafada min,but Dad banda wacce zan aura” Dad ya dakamai tsawa just shout up!, I said shout up Barraq, duk matayen dake duniyar nan ace ka kasa picking one ka aura,kullum tsufa kake karayi 35years is not a joke. Barr ya dafe kanshi dan mugun darawa yake bayason yaga yanada Dad fushi but amma me zaiyi baida wacce zai Aura maganar Dad yadawo dashi daga tunanin dayake “ina shekara 75 ku biyu kacal Allah yabani a duniya dakai da Auta,don’t you feel ashame of ur self Barraq, All ur friends sunyi aure banda kai” zama yayi yana sauke ajiyan zuciya kafin yace” Barraq ina bukatan jikoki dazanyi wasa dasu,yace just take a look at dis big house kullum empty babu yara masu wasa,I want my house to be full with children, Barraq banason nai forcing dinka ka aure Nana saboda banason nama yarona abunda bayaso but listen” ya daddaki hannun kujera tareda nuna Barraq da yatsa “wlh,billahil azim Barraq nabaka two weeks ka kawomin matar dazaka aura inba hakaba u will see my… Da sauri Barraq ya sakko daga kan kujera yarike kafan Dad hawaye ya cika idonshi ya kifa kanshi akan kafar hawayen shi na zuba akan kafar Dad hakan ya mugun karyama Dad zuciya yadau hanunshi ya chusa a cikin gashin kanshi murya Chan kasa yace” Son ko bakada lpy ne? Tell me d truth “Barr ya girgiza kai,Dad yasa hannu ya dago kanshi ya rike kuncinshi kafin yasa hannu ya share hawayen daya zubo daga idonshi ahankali yace to meke damunka Barraq maiya hanaka aure?”
Ahankali Barraq muryan shi na rawa yace “Dad inada wanda nakeso,but yarinya ce karama,iyayenta sun rasu,tanada grandma data tsaneta sosai,and the law has given me her custody…” Nan yaba Dad labarin Rufaida gabaki daya batare daya boyema Dad ko abu dayaba,daidai da yanda ta taimake shi a kauye saida yafadan ma Dad.
Saida yagama fadanma Dad komi sanan Dad yace”maisa zaka boyemin all dis things Barraq,kama ubanka adalci kuwa harka tsinci yarinya gwamnati tabaka kudinta,shari’a tabaka yarinyar ta dawo karkashin ka saika boyemin duka ka kyauta?” Barraq ya girgiza kai yay kneeling agaban Dad yana girgiza kai araunane I was wrong Daddy dan Allah kayafemin,wlh Dad nai hakane saboda tsoron na tunkareka da zance,I thought bazaka saurare nibane” Dad ya girgiza kai “bazan taba ganin zakai taimako nahana kaba Barraq” ya girgiza kai ahankali yace zauna, Barraq ya zauna Dad ya daura hanunshi akanshi yana murmushi yace “am proud of you son,ina alfahari dakai,ina godiya da Allah daya bani kai a matsayin da,duk wanda Allah ya azurtashi da d’a mai jinkan wasu,mai tausayi da taimakon marasa karfi to hakika Allah yamai Babban kyauta,Allah maka albarka”ahankali Barraq yace” Ameen Daddy” Dad yace ” dudda law ne yabaka Rufaida dagayau duk wani abu nata na dauka yadawo kaina, daga yanzu nine mahaifin Rufaida, zan zame mata mahaifin data rasa,haka zan hadata aure da Dana danasan dan arziki ne,dan bazan bama yata abunda zai cutar da itaba. Barraq baisan lokacin da murmushi ya subuce maiba.
Dad yakara kallonshi yace”gobe zan kira Mum dinka ta tahomin da Rufaida, sudawo Nigeria zan aurar da Rufaida gareka, kaje ka fara shirye shiryen Aure in 2weeks, ina certificates din daka samo mata?” Barraq yatashi ya shiga bedroom dinshi ya kawoma Dad ya karba ya dudduba sanan ya sauke ajiyan zuciya yace “zan nema mata makaranta,amma tana dakinka zata fara karatu,Allah sanya maka albarka, Dad ya fita daga dakin dauke da certificates din a hanunshi. Wani irin ihun murna Barraq yay yafara neman wayanshi yana Muzammil must here dis good news, wani tsalle yayi yafada gado zan zama ango in 2weeks.
Zaune suke a cikin jirgi,Rufaida ta kankame Mum jikinta na rawa Mum nata mata dariya tana kai daughter na kincika tsoro,a shagwaban ce ta dago fuskarta daya cika da hawaye ta sharbe hawayen tace”Mummy ai jirgin yanasa naji hanjin cikina kaman zasu fitone” Mum takara tunsurewa da dariya tace”Relax daughter, ai ganinan tareda ke,bazan taba bari wani abu ya sameki ba” lumshe ido Rufaida tayi ta daura kanta akan kafadar Mum tace “thank yhu Mummy, u mean everything to me Mother” Mum tasa hannu ta shafa kumatun ta “don’t thank me kinfi haka a wurina,I will give yhu everything idan inadashi” hawaye ya zubo daga idonta “I soo much luv yhu Mummy, keda Ummana nafiso a duk duniya” Mum ta lumshe ido tana murmushi “keda Barraq kune komina na duniya,banason wani abu dazai tabamin ku,inason ku sama da komi a duniyar nan” Rufaida ta kankame Mum tana dariya ahankali.
Kama hanunta Mum tayi tana kallon yatsun hakan yasa Rufaida ta natsu tana kallon Mum, Mum ta sauke ajiyan zuciya tareda maida hanun Rufaida kan cinyarta tace “Tun ranan farko da Son ya kawoki wurina nagane akwai soyayyar ki atattare dashi da sauri Rufaida ta dago kanta daga jikin Mum ta kalleta,murmushi Mum ta sakar mata tareda jawo kanta ta maida jikinta tana shafawa” kubiyu nafiso a duniya,saisa naso Ku biyu Ku auri juna saboda nasamu jikoki daga abu biyu danafi so aduniya wanda hakan zaisa nai farin cikin daban tabayi ba aduniya” tadan dukar da kanta dan taga yanayin Rufaida sai taga idonta a lumshe tai lamo da kanta a jikinta, murmushi Mum tayi”Daughter zaki iya cikamin wanan burin nawa?zaki iya taimakamin ki auri Dana mai sonki?” Rufaida tai shiru jikinta yafara rawa, jin shiru nakusan yan mintuna yasa Mum tace”idan kincemin a’a daughter I will understand and consider, bazan tabajin haushin kiba,and bazan taba tursasa kiba,niba Mum dinki…” Da sauri Rufaida ta dago da kanta takara hanunta abakin Mum tana girgiza mata kai”u are,and u will always be my Mummy, kinmin komi,kinban kaya, happiness,abinci,ilimi yaza’yi nakasa cikina uwata burinta Kwara daya,ur only wish Mummy? Dabanzama yatagari ba,na yarda zan aureshi,zan kula dash…” Mum tasa hannu ta share mata hawayen idon “banason ki tursasa kanki,banason kiga natakura miki,kaman ina saki dole” Rufaida ta girgiza kai “Mum kin isa ki tursasa min,kin isa kitakura min,kin isa kisani dole saboda ke uwata ce,karki Kara tunanin kin tursasa ni Mommy wlh bakiyi ba,kuma baki tababa” Da sauri Mum ta rungume ta ta sumbaci goshinta daidai lokacin da jirginsu yay landing a Abuja Airport.
Sakkowa sukayi hanunta na cikin na Mum,sai kalle kalle take,ahaka harsuka fito daga arrival inda suka tarar da Amma a tsaye sai duba agogon hanunta take,Mum ta karaso wurin kafin Amma taji an rungumeta bazata ba tsammani dariya sukayi kafin Mum ta saketa Amma ta karbi handbag din hanun Mum tace “Mum Barraq ya hanya” da harshen turenci,Mum tai murmushi tace “lpy ina auta na maisa baku taho tareba?” Amma tai murmushi “kema kin Santa tanachan tana kwainane wai itama zatama amaryan Uncle B girki,Mum tai dariya dasauri Amma tace” ina maganan Amaryan ina take na ganta? Da sauri Mum ta juyo tana daughter ahankali Rufaida tafito daga bayan Mum kanta akasa tana wasa da yatsar ta muryanta na rawa tace ina wuni, Amma takamo hannayen ta biyu tadan tsunguli kumatun ta ahankali tace”bazan amsa gaisuwar kiba,shine kika boye abayan Mummy saboda bakiso na ganki ko?” Rufaida ta girgiza kai yakuri, da sauri Amma ta kama baki dena bani hakuri amaryan Dana muje gida kici abinci ki huta gwara baniso ki wahala dan daki wahala gwara tsohuwar nan ta wahala ta nuna Mum tana dariya,Mum ma tai dariya kafin su shiga mota driver yajasu zuwa gida.