Kungiyar Boko Haram bangaren da Abubakar Shekau ke jagoranta, ta watsa sabon faifan bidiyo, wanda a ciki Shekau ya musanta kirarin da rundunar sojin Najeriya ta yi na cewa ta raunata shi a wani hari da ta kaiwa maboyarsa watan da ya gabata.
Cikin bidiyon da kungiyar ta watsa a shafin Youtube Shekau wanda yayi Magana cikin harsunan Hausa, Kanuri da kuma Larabci ya bayyana cewa yana nan garau babu abin da ya same shi.
A watan Augusta rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa Shekau ya samu mummunan rauni a farmakin sama da ta kai maboyarsa, wanda kwamandojin kungiyar ta Boko Haram da dama suka rasa rayukansu.
Har yanzu dai rundunar sojin najeriya bata maida martini ba kan sabon bidiyon.
Title :
Ina Nan Garau Da Raina - Abubakar Shekau
Description : Kungiyar Boko Haram bangaren da Abubakar Shekau ke jagoranta, ta watsa sabon faifan bidiyo, wanda a ciki Shekau ya musanta kirarin da rundun...
Rating :
5