Daga Rariya
Kungiyar Shi'a ta yi barazanar tayar da tashin hankali Idan har Shugaban Kungiyar Sheik Ibrahim El Zakzaky ya makance a inda ake ci gaba da tsare da shi.
Mai Magana da Yawun Kungiyar, Ibrahim Musa ne ya bayyana haka idan ya nemi gwamnati ta gaggauta sakin El Zakzaky don a samu damar duba lafiyarsa.
A shekaranjiya ne dai kotu ta yi fatali da bukatar Sakin Shugaban kungiyar wanda ake tsare da shi tun a shekarar da ta gabata bayan wani karamin rikici da ya barke tsakanin mabiyansa da rundunar soja a Kaduna.
Title :
Idan El Zakzaky Ya Makance Za A Ga Tashin Hankali - Kungiyar Shi'a
Description : Daga Rariya Kungiyar Shi'a ta yi barazanar tayar da tashin hankali Idan har Shugaban Kungiyar Sheik Ibrahim El Zakzaky ya makance a ind...
Rating :
5