Rahotanni sun tabbatar da cewa a yau ne, tsohon gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Shema, ya kai kansa ofishin hukumar EFCC mai yaki da Mass yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati.
Wadansu majiyoyi a hukumar ta EFCC sun tabbatar aw BBC cewa yanzu haka tsohon gwamnan yana ofishin, inda yake rubuta jawabi ana kuma yi masa tambayoyi.
A jiya ne dai tsohon gwamnan ya musanta sanarwar da EFCC ta fitar ranar Laraba cewa ba ta san inda yake ba, don haka tana neman shi ruwa-a-jallo. Hukumar dai na neman Shema ne game da zargin yin sama da fadi da wasu makudan kudin Jihar ta Katsina.
Title :
Ibrahim Shema Ya Mika Kansa Wa EFFC
Description : Rahotanni sun tabbatar da cewa a yau ne, tsohon gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Shema, ya kai kansa ofishin hukumar EFCC mai yaki da Mass y...
Rating :
5