Majalisar koli na tattalin arziki wadda ta kunshi Mataimakin Shugaban kasa, gwamnoni da ministoci ta amince da shawarwarin sayar da wasu kadarorin gwamnati da nufin samun isassun kudaden farfado da tattalin arzikin Nijeriya.
Mai Magana da yawun Mataimakin Shugaban kasa, Laolu Akande ne ya tabbatar da haka inda ya ce majalisar ta amince da yin amfani da kudaden da aka karbo daga hannun barayin gwamnati wajen gudanar da manyan ayyukan raya kasa. Ministan Kasafin Kudi da Tsare tsare, Sanata Udo Udoma ne dai ya gabatar da shawarar sayar da wasu kadarorin gwamnatin.
Rariya
Title :
Gwamnoni Da Ministoci Sun Amince Da Sayar Da Kadarorin Gwamnati
Description : Majalisar koli na tattalin arziki wadda ta kunshi Mataimakin Shugaban kasa, gwamnoni da ministoci ta amince da shawarwarin sayar da wasu kad...
Rating :
5