Hatsaniya ta barke tsakanin wasu matasa da jami'an Hisbah, da yammacin jiya Asabar a garin Hadejia dake jihar Jigawa.
A ranar Juma'ar da ta gabata ne hukumar Hisbah a karamar hukumar Hadejia ta ce ta fitar da sanarwa soke dukkan wani kide-kide ko biki da zai hada 'yan mata da samari wuri guda.
Bayan wannan sanarwar ne, a jiya Asabar hukumar Hisbar ta kai sumame cikin garin Hadejia, inda a cikin sumamen da jami'an Hisban suka fita, suka yi arba da gungun matasa da 'yan mata suna gudanar da bikin aure, a unguwar Gawuna dake cikin garin Hadejia, inda jami'an hisbar suka iske ana cashewa tsakanin 'yan mata da samari, lamarin da ya sa jam'iyan hisbar suka harzuka, suka yi yunkurin kwace kayan kidan, inda su kuma matasa suka ce ba za su yadda da hakan ba.
Hakan ne ya janyo fafatawa tsakanin matasa da jami'an hisba, inda yanzu haka matasa da dama suna asibiti domin karbar magani sakamakon raunika da suka samu a lokacin fafatawar.
Sai dai a zantawata da Malam Aji Kima Hadejia yace matasan sun musanta cewa jami'an Hisbah sun bayar da sanarwar hana kide-kide.
Title :
Graphic Photos:Anyi Rikici Tsakanin Matasa Da Yan Hisbah A Jigawa
Description : Hatsaniya ta barke tsakanin wasu matasa da jami'an Hisbah, da yammacin jiya Asabar a garin Hadejia dake jihar Jigawa. A ranar Juma...
Rating :
5