Dakarun 33 Brigade na rundunar sojojin Nijeriya a wata farauta da suka fita a kauyen Mai Hari dake karamar hukumar, Alkaleri a jihar Bauchi a jiya Alhamis sun yi artabu da barayin shanu da garkuwa da mutane.
Bayan musayar wuta da suka yi, sojojin sun yi nasarar kashe biyu daga cikin 'yan bindigan tare da ceto mata hudu da yaro karami guda daya da aka yi garkuwa da su.
Yanzu haka an mika wadanda aka ceto din ga iyalansu da misalin karfe biyu na ranar jiya.
A bangare daya kuma, Dakarun Kunamar Daji sun ci gaba da farauar su inda suka fatattaki barayin shanun daga mafakarsu dake jihohin Gombe da Bauchi.
Rariya
Title :
Graphic Photos: Sojoji Sun Ceto Wasu Mata Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Jihar Bauchi
Description : Dakarun 33 Brigade na rundunar sojojin Nijeriya a wata farauta da suka fita a kauyen Mai Hari dake karamar hukumar, Alkaleri a jihar Bauchi...
Rating :
5