Matar nan da muka kawo muku rahoton halin da ta samu kanta a ciki, sakamakon watsa mata ruwan guba da aka yi a fuska, wato Malama Amina Musa Nasir, mai fafutukar kare hakkokin mata dake birnin Kano, har yanzu dai tana cikin wani mawuyacin hali a asibitin kwararru na Malam Aminu Kano.
Mijin wannan baiwar Allah Malam Muhammad Nasir ya shaidawa jaridar Blueprint cewa, matar tasa da ta gamu da wannan ibtila'i daga wasu azzulumai mamugunta tana cikin bukatar taimakon jama'a masu hali, sakamakon yadda jikinta ya yi mummunan lalacewa, saboda gubar da aka watsa mata a jiki, yayin da take kwance tare da maigidan ta cikin dare.
Ya ce, jama'a dai na taimakawa da gudunmawa daidai gwargwado, amma abin da ake samu bai kai wanda za a yi mata aikin da ake bukata ba, don haka ake bukatar taimako daga hukumomi da manyan masu hali su taimaka, wajen ceto rayuwar wannan baiwar Allah.
Amina Nasir mai shekaru 27 ta gamu da wannan mummunan jarabawa ce da ta canza mata siffar halittar ta da kuma nakasa mata fuska, inda aka ce yanzu haka idanunta ma a rufe suke ba ta ganin gari.
Da fatan gwamnatin jihar Kano da masu hali za su kai wa wannan baiwar Allah taimakon gaggawa.
Zuma times Hausa
Title :
Graphic Photos: Amina Musa Nasir Na Nima A Tallafawa Rayuwar Ta
Description : Matar nan da muka kawo muku rahoton halin da ta samu kanta a ciki, sakamakon watsa mata ruwan guba da aka yi a fuska, wato Malama Amina Mus...
Rating :
5