DALILI NA FARKO: ALI NUHU dai musulmi ne kuma nima musulmi ne. Dan haka wajibi ne dama musulmi ya so dan uwansa musulmi.
DALILI NA BIYU: ALI NUHU yana mai da hankali wajen yin ibada ga karatun Al-qur'ani.
DALILI NA UKU: ALI NUHU yana da lokaci na musamman wanda ya ware dan ganawa da iyalansa da kuma kyautata musu dai dai gwargwadon sa.
DALILI NA HUDU: ALI NUHU yana iya kokarinsa wajen tallafawa jarumai har Allah ya daukaka su.
DALILI NA BIYAR: ALI NUHU mutum ne wanda bayida hassada, yana iya kokarinsa wajen taimakawa mutane.
DALILI NA SHIDA: ALI NUHU mutum ne wanda bayi wasa da aikinsa, ya bata muhimmanci sosai, hakan ne yasa haryanxu tauraronsa yake haskakawa.
DALILI NA BAKWAI: ALI NUHU mutum ne wanda ya ke son masoyansa, dalilin hakane ya sa akullum masoyansa karuwa sukeyi.
DALILI NA TAKWAS: ALI NUHU mutum ne wanda bai yarda kaci mutuncin abokin aikinsa ba, don kawai kana sonshi.
DALILI NA TARA: ALI NUHU mutum ne mai ilimi, iliminsa ne ya sa basirar sa kullum karuwa yakeyi.
DALILI NA GOMA: ALI NUHU yana son Allah da Manzonsa,, zai yi wuya kaji yayi magana daya, biyu zuwa uku ba tare da ya ambaci sunansu ba.
Wadannan sune dalilai goma da suka sa nake son Alinuhu.
Ya Allah ka kara daukaka wannan bawa naka, ka sa yafi matsayin da yake ayanxu.
Ya Allah ka kareshi daga sharrin shaidan, mahassada, aljanu da ma wa'yanda basu son ganin cigabanshi. Ameen Fkd Alinuhu Onelove Dalilaigoma
Daga Ali Nuhu fans
Title :
[Daga Jama'a] Dalilai Goma (10) Da Yasa Nake Son Ali Nuhu
Description : DALILI NA FARKO: ALI NUHU dai musulmi ne kuma nima musulmi ne. Dan haka wajibi ne dama musulmi ya so dan uwansa musulmi. DALILI NA BIY...
Rating :
5